Tag: yadda ake

  • Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki 02

    Yadda Za Ki Ja Hankalin Mijinki 02

    A bayani na farko mun bayar da wasu bayanai a kan yadda ake jan hankalin miji; Ga sauran bayanan nan.

    4. Iya Taku

    Takunki a lokacin da kike gabansa da tsayuwarki da zamanki, dole ne ya zamo na musamman.Ya kasance daban kuma cikin salo na ɗaukar hankali. kar ki kasance mara kuzari ko kina nuƙu-nuƙu a yayin da kike tare da shi.

    5. Ku yi Siyayya Tare

    Yana da kyau kuna yin siyayya tare musamman ƙananun kaya masu ɗaukar hankali, wanda za ki yi masa kwalliya da shi, shi kaɗai. Kuma ki nemi zaɓinsa a kan irin wanda yake so, hakan zai saka shi ya kasance cikin zumuɗi.

    6. Ado Da Kwalliya

    Ba dole ba ne, sai kin caɓa kwalliya mai yawa sosai ba, a wasu lokutan canza yanayin gyaran gashinki ko gyaran fata yana jan hankalin mai gida. Ko Kuma canza launin jambaki ko ƙara wani sabon launi a kan fuskarki wanda bai saɓa gani ba.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Zaki Inganta Halayyarki Da Ɗabi’u Masu Kyau danna nan

  • Yadda Ake Yin Kabbarar Harama

    Yadda Ake Yin Kabbarar Harama

    Bayan gama iƙama a sallar jam’i ko sallar mutum shi kaɗai; mace ce ko namiji, sai ya yi kabbarar harama wacce ita ce mabuɗin sallah.

    Yadda ake yin ta shi ne, furta kalmar (Allahu Akbar) tare da ɗaga hannuwa biyu daidai kafaɗu biyu; ko kuma daidai kunnuwa biyu; ko kuma saman ‘yan yatsun, su kawo daidai kunnuwa.

    Shi kuma mahaɗar tafin hannu da tsintsiyar hannu ya zo daidai kafaɗu; wannan kabbarar haramar ita ce da zarar mai sallah ya furta ta, ta haramta masa duk wani aiki da ba shi da alaƙa da sallar; kamar yin magana, ko waiwaiye, ko cin wani abu, ko tauna, ko dariya, ko sauraren wani abu can daban, da bai shafi karatun liman ba.

    Sai ɗan abin da yin sa babu laifi, kamar yin kuka saboda jin abin da Ƙur’ani yake faɗa; na rahama, ko azaba, ko daɗin karatun ko sosa jiki, ko yin ɗan motsi kaɗan, ko gyaran murya. Yin wannan kabbara ta harama, wajibi ne a sallah ga bin jam’i ko yin sallah; shi kaɗai mace ce ko namiji ne, mamu ne ko limami ne, wanda duk bai yi ta ba, ba shi da sallah, saboda da ita ce ake fara buɗe sallar, kamar yadda bayani ya gabata.

    Ana so mai sallar ya yi (du’aa’ul istiftah) wato addu’ar buɗe karatun sallah wacce yin ta (mustahabi) ne; ma’ana abin da aikata shi lada ne, rashin aikata shi kuma ba laifi ba ne; a taƙaice dai an ba ka zaɓi na idan kana so ka yi; idan ba ka so kuma ka bari.

    Ga yadda ake furta wannan addu’ar:

    (Allahumma baa’id baini wa baina kaɗayaya kama ba adta bainal mashriqi wal magribi, Allahummag silni bil ma’i wal salji wal bardi wa nakkini minaz zunubi wal kaɗayaya kama yunaƙƙal saubul abyad minal danas).

    Fasarar wannan addu’a shi ne; Allah ka nisanta tsakanina da zunubaina kamar yadda ka nisanta tsakanin mahudar rana da mafaɗar ta; Allah ka wanke ni da ruwa da kankara da ruwan sanyi, ka wanke ni daga zunubaina da kurakuraina; kamar yadda ake wanke fararen tufafi daga cikin datti.

    Bayanin da Ibnu taimayyah ya yi a kan wannan addu’ar a lokacin da ɗalibinsa; Ibnul Ƙayyim ya tambaye shi ma’anar wannan addu’a ga mai yin sallah, shi ne ya ce; “Idan mutum yana aikata saɓo zuciyarshi bushewa take yi, har ta kai matakin da za ta yi tauri, yadda hasken imani ba zai iya shiga ba, sai ya wayi gari imaninsa ba ya ƙaruwa.

    Idan ya aikata wani babban saɓon, sai zuciyarsa ta kama da wuta tana cinye ragowar imanin da ke zuciyar. Ga shi kuma babu abin da ke kashe wuta sai ruwa, shi Kuma ruwan sanyi shi ne zai ƙarasa murkushe ragowar ɓurɓushin wutar, bayan an kashe asalin wutar da ruwa, ita kuma ƙanƙara ita ce za ta mayar da zuciyar ta koma mai laushi, kamar yadda take kafin ta aikata manyan saɓo. Wannan shi ne dalilin da yasa ake so mumini ya dinga yin wannan addu’ar.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani da Bismillah A Cikin Sallah Danna nan

  • Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah

    Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah

    Mai yin sallah zai buɗe karatun Alƙur’ani da Bismillah a ɓoye, ba tare da mamu sun ji karatun Bismillah ba, shi ne limami kuma sallah ce da ake bayyana karatu.

    A mazhabin Malikiyya kuma zai bayyana karatun Bismillah ne a fili, zai karanta Fatiha sannan ya sake yin wata Bismillah kafin ya karanta surar gaba.

    Zai tsaya ne ya ɗora hannunsa na dama a kan hannunsa na hagu; a kan ƙirjinsa ko ƙasan ƙirjinsa saman cibiyarsa; ya ɗora idanunsa biyu a daidai inda yake sujuda, kuma ya bar idanunsa a buɗe, ba tare da lumshe su ko rufe su ba; domin rage yawan tunani da zancen zuci a cikin sallah.

    Sannan zai karanta surah ko wani yanki na surah ko wasu ayoyi; gwargwadon abin da Allah ya sanar da shi na Alƙur’ani yana tsaye; yana iya fasa karanta surah ko ya canza surah idan ya ji ya kakare; ko kuma ta ɗauke a cikin ƙwaƙwalwarsa ko ya rasa mai tuna masa ko bai rasa ba, 

    Yana iya karanta aya ɗaya koda ba mai tsayi ba ce, wajan karatu ya kula da haƙƙin mamu; kar ya tsawwala musu wajen karanta surori masu tsayi ko yawa idan yana limanci; idan shi kaɗai ne ya tsawaita yadda ya so.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Alwala danna nan

  • Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    Yadda Za Ki Kula Da Fatarki

    A yadda mayuka da kayayyakin gyaran jiki suka yi yawa a kasuwa; zaɓar abubuwan da za su taimaka wa fatar jikinki yana iya zama abu mai matuƙar wahala. Amma idan kin san yanayin fatarki, sai ki zaɓi abubuwan da za ki yi wajen kula da fatarki a kullum.

    Ga misalan yadda za ki kula da fatarki:

    1. Goge Kwalliya Kafin Bacci

    Idan ya kasance an miki kwalliya mai yawa ta zamani, to yana da kyau ki samu abin da za ki goge ta tas, kafin ki kwanta barci. Koda wacce ta yi miki kwalliyar ta taya ki gogewa, amma idanuwa da laɓɓa suna buƙatar kula ta musamman, saboda haka; sai ki samu abin goge kwalliya (wiper) jiƙaƙƙiya, ki sake gogewa a hankali.

    2. Wanke Fuska

    Yana da kyau mace ta dinga wanke fuskarta sau biyu a rana. Da safe kafin ki yi kwalliya, sai kuma da dare kafin ki kwanta. Ana wanke fuska da ruwan ɗumi, ba mai zafi ba; sannan kuma a sake shafa sabulu a murza a hankali lungu da kwarmin fuska, sannan a sake ɗaurayewa.

    3. Amfani Da Toner

    Bayan an wanke fuska, ana so a shafa toner. A samu wani ɗan soso mai laushi a matsata kaɗan, sai ana shafawa a hankali ban da gurin ido sannan ba a wankewa.

    4. Amfani Da Moisturizer

    Bayan toner ta bushe a kan fuskarki, yana da kyau a yi amfani da moisturizer a kan fuska, hadda tafin hannu ma idan kin so. Idan kuma kina fama da baƙin zagaye ko kumburi ko tattarewar ido, sai ki samu wani mai na musamman.

    5. Yin Murza (Scrubbing)

    Ana iyayin murza ta, musamman sau ɗaya ko sau biyu a sati, za ki samu sinadarin AHA ko BHA ko Kuma wani sabulun ruwa, sai kina dangwala da hannunki, kina murzawa a hankali a kan fuskarki.Bayan wasu mintoci sai a wanke da ruwan ɗumi.

    6. Yin Amfani Da (Sunscreen)

    Yawan shiga rana kan iya jawo tattarewar fuska, ko kuma nuna alamun girma. Yana da kyau duk lokacin da za ku fita rana, ku shafa sinadarin da yake hana hasken rana illa a kan fatarku. Ana shafa wannan sinadarin ne bayan amfani da toner da moisturizer.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Gyaran Gashi Na Musamman danna nan

    Domin karanta bayani akan Yadda Ake Gyaran Jiki Yai Laushi Kuma Yai Kyau danna nan

  • Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah

    Wajibcin Karatun Fatiha A Cikin Sallah

    Karatun fatiha ga kowanne mai yin sallah wajibi ne; babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba, sai dai banda mutum 1, wato sabon musulunta da bai iya karanta komai cikin Alqur’ani ba; zai yi sallah a haka, koda bai iya Fatiha ba.

    Amma sai a ba shi sunan Allah da zai yi masa kirari da shi, da kalmomin neman gafara da rahama da shiriya; wanda zai nemi Allah ya yi masa amadadin karatun Fatiha kafin ya koyi yadda ake karanta ta.

    Haka kuma, karanta Fatiha ɗin a tsaye wajibi ne, sai dai idan mutum yana da larura, misali; mara lafiya da ba zai iya sallah a tsaye ba, sai a zaune; ko mai buƙata ta musamman da ba shi da ƙafafun da zai tsaya.

    Yana da kyau ga mai yin sallah shi kaɗai ko limanci idan ya zo aya ta ƙarshen Fatiha ya ce; “Aamiin”. Wato Allah ka amsa mana.

    Haka kuma, mamu dake bin limami sallah, su ma su ce, “Aamiin”, idan mutum ya dace wajen faɗar kalmar Aamiin, tare da mala’iku, Allah zai masa gafara.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zaɓi Ga Maamu Wajan Karatun Fatiha A Cikin Sallah danna nan.

  • Yadda Ake Meat Pie

    Yadda Ake Meat Pie

    Meat pie wani abinci ne da ake yin shi da fulawa.

    Abubuwan Da Ake Buƙata wajen haɗa Meat Pie

    Flour (350g)

    Margarine (150g)

    Maggi guda 4

    Ruwa yadda zai isa

    Hodar (cin–cin ) cokali 2

    Nama nuƙaƙƙin nama (170g)

    Kwai 3 / Albasa biyu, Attaruhu biyu (a daka su)

    Kayan ƙanshi kaɗan.

    Kayan Aiki

    Murhu/Risho/Gas/Oven

    Kasko

    Mazubi (mai tsafta)

    Injin murji/katako na murji/kwalba

    Fefe

    Kofi (mai gida-gida)

    Cokali mai yatsu

    Yadda Ake Haɗawa

    A samu fulawa a tankaɗe ta. A zuba a mazubi mai tsafta, a juye margarine a gurgutsira shi a cikin fulawa, sai a cakuɗa ta, a barbaɗa hoda da maggi a cikin fulawa ko ina ya ji.

    A fasa ƙwai a zuba, a cakuɗa gabaki ɗaya ta haɗu, sannan a kawo ruwa a dinga zubawa da kaɗan da kaɗan; har ta haɗe jikinta, sai a rufeta tayi minti 30. Sai a ɗauko niƙaƙƙen naman a zuba mai a kasko kamar rabin lita.

    Mu zuba a kasko ya ɗan yi zafi kaɗan, kafin a sa nama, sai a kawo albasa da attaruhu da aka daka, a kawo maggi da kayan ƙanshi kaɗan a juya naman, har sai ya soyu.

    Sai a sauke, a ajiye a gefe, sai a ɗauko fulawar a bubbuga ta, ta ɗan tashi, sai a samu katako na murji da abin murzawa; a guggutsura fulawar sai mummurza ta kamar fefe, mutara a gefe sai a ɗauko fefe ɗaya, mu samu ƙaramin kofi, mu yi gida-gida da ita.

    Sannan a ɗebi naman a dunga zubawa cokali, biyu ana zubawa a tsakiyar kowace fulawar, har sai ya ƙare; daga nan sai mu kama bakin kowane ɗaya murufe, bayan mun shafa ruwa a gefansa;

    Mu samu cokali mai yatsu, mu daddanne, mu sa cokali mai yatsu mu haɗa samansa kaɗan, za a iya soyawa ko gasawa, in ana son gasawa sai a samu farantin gashin, mu shafe shi, mu jera meat-pie ɗin a kai.

    A kunna oven a rage wutar, a saka shi a ciki, a gasa har sai ya yi ruwan ƙasa ko kuma a soya a mai me zafi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Fish Cake danna nan

  • Yadda Ake CupCake

    Yadda Ake CupCake

    Cupcake wani abinci ne wanda ake haɗa shi da fulawa

    Abubuwan Da Ake Buƙata idan za a haɗa cupcake

    • Fulawa gwangwani 4
    • Butter gwangwani 2
    • Ƙwai 4 – 6 sugar gwangwani 2
    • Baking hoda ƙaramin cokali 2

    Kayan Aiki

    • Oven
    • Mazubi
    • Gwangwanayen cake
    • Takardar gashin cake
    • Cokali

    Yadda Ake Haɗawa

    Za a sami mazubi mai tsafta, sai a juye sukarin da butter a buga, har ya haɗa jikinsa, sai a fasa ƙwan duka, sai a sake bugawa a zuba baking hoda.

    Da ɗan Flavour kaɗan a ƙara bugawa naɗan, lokaci sai a samu gwangwanayen cake a sa takardar gashin cake a cikinsu, sai a zuba babban cokali 2 nakwaɓin a kowanne gwangwani, sai mu gasa a oven har sai ya yi ruwan ƙasa mai haske.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Beef Burger danna nan

  • Yadda Ake Beef Burger

    Yadda Ake Beef Burger

    Beef burger wani abinci ne na Turawa wanda ake haɗa shi tare da biredi.

    Abubuwan Da Ake Buƙata

    • Nama (niƙaƙƙe) (250g)
    • Albasa manya 5
    • Attaruhun 2
    • Ƙwai 1
    • Kayan ƙamshi (ƙarami cokali)
    • Tafarnuwa ƙwallo 2
    • Tumatur manya 2
    • Ganyen lettuce/ abin ɗanɗano
    • Cocumber/ cheese slices (yankakke)
    • Roll bread yadda ake buƙatar sa.

    Kayan Aiki

    • Mazubi (mai tsafta)
    • Kasko
    • Murhu/Risho/Gas

    Yadda Ake Haɗa Beef Burger

    A zuba nama a mazubi mai tsafta, a zuba da kayan ƙamshi da attaruhu da albasa niƙaƙƙiya da ƙwai da abin ɗanɗano, sai a haɗa a cakuɗa sai a du

    nƙula da ɗan girma.

    Sai a danna shi ya koma ƙasa, ya ɗan yi faɗi, sai a sa mai a kasko mara kamu, a ɗan shafa mai kaɗan, sai a ɗan sa naman a cikin kaskon, in wannan ɓarin ya soyu sai a maida ɗaya ɓarin, har shi ma ya gasu.

    Sai a sauke a ajiye a gefe, sai a ɗauko tumatur 2, albasa 2, cocumber babba guda ɗaya, sai a wanke da gishiri a tsane a gefe, a yanka su falefale, sai a ɗauko salak a ciccire shi a wanke da gishiri ya tsane.

    Daga nan, sai a ɗauki biredi biyu a kifa shi a kaskon da aka gasa naman, mu gasa shi sama-sama; sai a ɗauko biredi a shafa masa man salak, sai a ɗaura salak tumatur ɗaya, a sa nama a tsakiya, sai a ɗauko cocumba a sa da albasa; da (cheese slice) guda ɗaya a ɗora a kan naman a rufe da biredin, haka za a yiwa sauran har a gama da kayan haɗin da sauran biredin har a gama .

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Mahshi danna nan

  • Mene Ne Shafin Blog

    Mene Ne Shafin Blog

    Blog wani shafi ne da ake buɗewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tunasarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma yana a matsayin wata kafa ta yaɗa labarai da tallace-tallace.

    Abubuwan Da Za a Tattauna:-

    A. Menene Blog.
    B. Matakan da ake bi wajen samar da shafin na Blog
    C. Muhimmancin shafin Blog.
    D. Yadda ake amfani da shafin Blog.

    A. Ma’anar Blog:

    Blog wani shafi ne da ake buɗewa domin ilmantar da al’umma wani ilmi na daga mai shi wannan shafin; ko kuma tuna sarwa a kan abubuwan da suke faruwa a tsakanin al’umma, hakan nan kuma Blog na matsayin wata kafa ta yaɗa labarai da tallace-tallace.

    B. Matakan Da Ake Bi Wajen Buɗe Shafin Blog

    Matakin Farko: Zuwa Shafin Domin Yin Rijistar (create your Blog now)

    Ka shiga adireshin samar da shafin na http://www.Blogger.com sai ka je inda aka ce create your Blog now; ma’ana ka bude shafinka na Blog yanzu. Sai ka cike sunan da kake son Blog naka ya zama, amma ya zama babu mai irin shi. Haka kuma wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da kake so.

    Mataki Na Biyu: Zaɓar Kalmar Sirri (select a password)

    Sai ka zaɓi lambar sirrinka wato password wanda kake buƙatar ya zama, wanda wannan lambar sirrin ”password” yana kamawa daga alamomi guda shida zuwa sama da haka; amma akwai buƙatar wajen sanya lambar sirrin ”password” ya zama haɗakar baƙaƙe: lambobi, da kuma wani abin da ba kowane zai iya ganowa ba.

    Haka kuma ya zama ka sanya lambar sirrin da za ta yi wahalar ganowa ga wasu, amma mafi sauki a gare ka wajen tunawa.

    Mataki Na Uku: (Select a Display Name)

    Sai sunan da zai zama na Blog naka, ma’ana DISPLAY NAME; wanda da wannan sunan ne za ka iya amfani da shi wajen shiga ka yi rubutunka domin ƙaruwar waɗanda kake so su amfana.

    Abin Lura:

    Wajen zaɓar sunan, yana da kyau ka zaɓi sunan da zai kare mutuncin kanka, kuma ya zama babu mai irin sa; domin yin rijista a shafin internet idan da wanda ya riga ka buɗewa da irin wannan sunan; kai sai dai ka nemi wani sunan ko kuma bayan kasanya sunan sai ka sanya wata alama da za ta nuna kai ne ba wancen na farkon ba.

    Haka kuma, wannan suna shi ne sunan da zai ba ka damar shiga shafin naka duk san da ka so. Sannan yana da kyau ka sanya sunan da ba zai yi wahalar nema ba.

    Mataki Na Huɗu : (enter an email address)

    Sai ka sanya email address naka, wanda yana da matuƙar muhimmancin sa shi, kasancewar ma idan babu shi rijista ba ta yiwuwa, wanda daga baya ma za ka iya canja wannan email din; domin idan ya zama ya lalace ko ya sami matsala. Haka kuma wannan email, ba zai nuna ba a shafinka na Blog, sai in ka so; domin boyewar zai taimaka maka ka sami tsaro daga masu kutse/mafasa. Bayan ka kamala wannan sai ka karanta dukkanin tsare-tsaren da suke bada damar buɗe shafin Blog; ”read terms of services” kafin ka danna zuwa gida na gaba, wato “continue”.

    Mataki Na Biyar: Bawa Blog Naka Tittle (Give your blog a tittle)

    Wannan shi ne wani suna ko alama da zai ba ka damar ya fito a saman dukkanin wani rubutu da za ka yi; a kan kowanne shafi, sai dai ya danganta da rubutun da za ka yi, kuma ya zama ka canja.

    Mataki Na Shida Zaɓar Adireshinka Na Blog: (choose a web address to your blog)

    A wannan guri zai ba ka damar zaɓar adireshin da zai yi sauƙi wajen samun ka a shafin Blog; wanda kuma zai bayyana ga ma’abota shiga shafin.

    Misali http://yourblogspacename.blogspot.com, da ga wannan sai zaɓar tsarin da blog naka zai zama domin kayatarwa wato “template” kada a zaɓi dukkan abun da aka gani wajen zaɓe a nutsu wajen zaɓin; domin samar da kalar da masu bibiyar shafin za ta ƙayatar da su. Domin zai iya ba ka damar canjawa daga baya a cikin jerin saiti na shafin. Da zarar ka kamala wannan to shafin ka na blog ya buɗu.

    C. Muhimmancin Shafin Blog

    Dangane da bayannan da ya gabata, a kan mene ne Blog kuma ya ake buɗe shi, ku san dai yana da matuƙar muhimmanci musammam ga, masu san su yaɗa wasu bayanai da jama’a za su amfana, haka kuma yana da matuƙar muhimmanci ga ‘yan Kasuwa da kuma ɗaliban ilmi dama sauran al’umma masu san ci gaba ta hanyar amfani da yanar gizo wato “internet” a Turance.

    D. Yadda Ake Amfani Da Shafin Blog

    Da zarar ka samar da wannan shafi na blog domin watsa rubututtukanka. Shi kenan sai farawa, yadda ko za ka fara shi ne :
    Bayan ka buɗe shafin naka, sai ka shiga “start posting” inda a nan ne za ka sami damar tsara rubutunka da kuma watsa shi. Shirya tsari mai ƙayatarwa domin jan hankali wato “tittle”; sai ka rubuta rubutun ka haɗi da cika ka’idojin rubutu domin mai karatu ya fahimta.

    Sannan bayan ka kamala sai ka dannan kan “publish post” da hakan shi zai ba ka damar rubutunka ya tafi duniya kuma ya zama duk wanda ya bi cikin internet a kan abu makamancin naka; to zai ba shi damar ganin rubutun tare da saƙon da kake son isarwa.

    Haka kuma, idan kana buƙatar wani ya je ya karanta sai ka gaya masa “tittle” na saƙonka; ko rubutunka wanda da zarar ya bincika zai samu.

    Duk lokacin da ka sanya sabon rubutu a kan Blog naka, yana da kyau ka watsa shi domin amfanuwar mutanen da kake so su amfana, saboda haka wasu ma idan suka nemi makamancin abin da ka sanya za su gani su ƙaru .

    Domin neman Karin bayani za ku iya samu na a 08087633060.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Abubuwan Da Ya Kamata Ka Sani Dangane Da Twitter danna nan

  • Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp

    Yadda Ake Amfani Da Kafar Sadarwa Ta Whatsapp

    Sau da yawa mutane na mu’amala da kafar social media ta whatsapp; amma akwai tarin abubuwa da ba su san yadda ake amfani da su ba yadda ya dace; ko kuma ba su san yadda za su aiwatar da wasu abubuwa ba.

    Waɗannan wasu kadan ne daga cikin irin abubuwan da ake iya aiwatarwa da ba kowa ya sani ba:

    TURA SAƙO GUDA ƊAYA GA MUTANE DA YAWA (BROADCASTING)

    Wannan wata hanya ce da ake tura saƙo guda ɗaya zuwa ga mutane da yawa; da zarar ana son a yi wannan; sai a tafi kan MENU inda ke da wasu alamomi guda uku.

    Sai mutum ya zaɓi Broadcast wanda a nan ne zai ba ka damar tura saƙon zuwa ga mutane da yawa

    SAUYA NAU’IN RUBUTU

    Wanna ma wata alama ce da za ka iya sauya nau’in rubutu, misali ya tafi a kwance ko kuma ya yi kauri ko ya zama a cikin alamar sokewa.


     Domin tafiyar da rubutu a kwance sai a rubuta _rubutu_ sai a tura.
     Idan kana so ka sanya rubutu ya yi kauri, sai a yi amfani da *rubutu* sai a tura.
     Haka ma idan kana son alamar sokewa sai a yi amfani da ~rubutu~ sai a tura.

    Domin Karanta Cikakken bayani a kan Yadda Ake Amfani Da MyMTN App Domin Gano Wasu Muhimman Bayanai Akan Layin Ka Na MTN danna nan