Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cereal like acca - A turance tana nufin iburo.
Misali; Na auno iburo a kasuwa.
HAU; Iburo (Tana nufin hatsi mai kama da acca)
Certified Institute of Cost Management of Nigeria (CICMA) - cibiyar naƙaltar kididdigar uwar kuɗi ta najeriya
Certified Pension institu of Warehousing Materials Management (CPIWMM) - cibiyar naƙaltar dabarun ajiyar kayayyaki
Certified Pension Institute of Nigeria (CPIN) - cibiyar naƙaltar Harkokin fansho ta najeriya
Chain - A turance tana nufin kaca.
Misali; An canjawa keken kaca, yanzu yana tafiya lafiya lau.
HAU; Kaca (Tana nufin sarƙa musamman irin wadda ke juya kafar keke)
Chair - A turance tana nufin kujera.
Misali; Inna ta siyo sabuwar kujera.
HAU; Kujera (Tana nufin abin da ake zama a kai)
Chameleon - A turance tana nufin hawainiya.
Misali; Hawainiya na tafiya ne a hankali kamar dodon koɗi.
HAU: Hawainiya (Tana nufin wata dabba mai kama da ƙadangare, tana canja launi ta saje da inda take don ba wa kanta kariya daga abokan gaba.)
Chana Radio International (CRI) - Gidan Rediyon Caina/Sin
Change - A turance tana nufin canja.
Misali; An canja lokacin jarrabawar daga ƙarfe ɗaya zuwa ƙarfe biyu na rana.
HAU; Canja (Tana nufin sake wani abu da wani)
Change of position - A turance tana nufin juyi.
Misali; Indo ta zata naƙuda ta fara amma juyi ne.
HAU; Juyi (Tana nufin canjawa daga wani yanayi zuwa wani)