Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Camera - A turance tana nufin kyamara. Misali: Umar ya sayi sabuwar kyamara domin ɗaukar hoto. HAU: Kyamara (Tana nufin na’urar da ake amfani da ita wajen ɗaukar hoto ko bidiyo).
Camfi - Tana nufin yadda da maganganu marasa tushe. Misali; Mutanen da sun yadda da camfi sosai. ENG; Superstition (A turance tana nufin camfi)
Can - Tana nufin nesa da inda ake. Misali; Na ajiye butar a can. ENG; Over there (A turance tana nufin can)
Canary - A turance tana nufin kanari. Misali; Tun asuba nake jin kukan kanari a kan bishiyar gidan nan. HAU; Kanari (Tana nufin wani nau'in tsuntsu ma'abocin rera waƙa)
Cancak - Tana nufin ɗungurungum, wato a ɗauke abu gaba ɗayansa. Misali; Ta ɗauke jakar cancak daga kan teburin. ENG; Completely Gone (A turance tana nufin cancak)
Cancanta - Tana nufin dacewa. Misali; Malamin ya cancanta a ba shi lambar yabo, saboda ƙokarinsa. ENG; Deserve (A turance tana nufin cancanta)
Candle - A turance tana nufin kyandir. Misali: Mun kunna kyandir saboda wutar lantarki ta ɗauke. HAU: Kyandir (Tana nufin abin da ake kunna wa domin samar da haske, musamman idan babu wuta).
Canine Tooth - A turance tana nufin fiƙa. Misali; Yaron ya fara fiƙa. HAU; Fiƙa (Tana nufin haƙoran gaba)
Canja - Tana nufin sake wani abu da wani. Misali; An canja lokacin jarrabawar daga ƙarfe ɗaya zuwa ƙarfe biyu na rana. ENG; Change (A turance tana nufin canja)
Cankacakare - Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf. Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare. ENG; Running short of something (A turance tana nufin cankacakare)
1 44 45 46 47 48 337