Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Chartered Institute of Taxation OF Nigeria (CITN) - Cibiyar naƙaltar Haraji Ta Najeriya
Chartered Insurance Institute of Nigeria (CIIN) - Cibiyar naƙaltar inshora ta Najeriya
Charttered Insurance Institute of Nigeria (CIIN) - Cibiyar naƙaltar inshora ta Najeriya
Chattered Institute of Finance Control of Nigeria (CIFCN) - Cibiyar naƙalter hada-hada da ƙayyade kuɗaɗe ta Najeriya
Chattered Institute of Treasury Management (CITM) - Cibiyar naƙaltar gudanarwar ma'ajiya
Chattered Institute of Treasury Management (CITM) - Cibiyar naƙaitar gudanarwar ma'ajiya
Cheap - A turance tana nufin arha.
Misali; Kayan da Malam yake siyarwa suna da arha.
HAU; Arha (Tana nufin abu mai sauƙin samu, ko kuma wanda ake siyan sa da kuɗi kaɗan)
Cheaply - A turance tana nufin bulus.
Misali; Ya siyi gidan a bulus saboda mai gidan kuɗi yake buƙata.
HAU; Bulus (Tana nufin samun abu a arha ba tare da an sha wahala)
Cheaply - A turance tana nufin ɓagas.
Misali; A ɓagas y samu kayan da ya siyo.
HAU; Ɓagas (Tana nufin samun abu cikin sauƙi ba tare da an sha wahala ba)
Cheat/Trick - A turance tana nufin damfara.
Misali; Samari na koyon damfara ta hanyar yanar gizo sosai.
HAU; Damfara (Tana nufin a cutar da mutum ta hanyar yin dabaru a ƙwace masa kuɗi ko wani abu)