Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cheek - A turance tana nufin kunci. Misali; Ya sha mari a gefen kuncinsa na hagu. HAU; Kunci (Tana nufin gefen fuska na hagu ko na dama)
Cheeks - A turance tana nufin kumatu. Misali; Fauziya ta shafa hoda a kumatu. HAU; Kumatu (Tana nufin jam'in kunci wato gefen fuska na hagu ko na dama)  
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chemical Society of Nigeria (CSN) - Ƙungiyar masana sinadarai ta Najeriya
Chewing Stick - A turance yana nufin asawaki. Misali; Na tarar yana asawaki da na je gidan. HAU; Asawaki (Itace ne da ake goge haƙora da shi)
Chicken/Hen - A turance tana nufin kaji. Misali; An soya kaji za a yi mana miya da su. HAU; Kaji (Tana nufin jam'in kaza)
China Radio International (CRI) - Gidan Rediyon caina /sin
Christian - A turance tana nufin banasare. Misali; Wani banasare ya tare a yankin nan. HAU; Banasare (Tana nufin mai bin addinin kiristanci)
Christian - A turance tana nufin kirista. Misali; Makociyata kirista ce, kuma muna zaman lafiya sosai. HAU; Kirista (Tana nufin mabiya addinin kiristanci wato ahalil kitabi)
Christian Association of Nigeria (CAN) - Ƙungiyar kiristoci ta Najeriya
1 48 49 50 51 52 298