Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Shoulder of Meat - A turance tana nufin karfata. Misali; Karfata na samu a rabon naman da aka yi. HAU; Karfata (Tana nufin kafaɗar naman rago ko sa ko raƙumi da sauransu)
Shouting - A turance tana nufin kuwwa. Misali; Yara na waje suna kuwwa saboda saukar ruwan sama na farko. HAU; Kuwwa (Tana nufin ƙara)
Shouting - A turance tana nufin kururuwa. Misali; Sadiƙ yana da rowa idan aka ɗauki abinsa kururuwa yake. HAU; Kururuwa (Tana nufin ihu da ƙarfi)
Showing eagerness - A turance tana nufin hanƙoro. Misali; Tun safe yake hanƙoro, saboda za su buga ƙwallon ƙafa da abokansa. HAU; Hanƙoro (Tana nufin nuna zaƙuwa)
Showing Energy - A turance tana nufin kuzari. Misali; Jaririn yana da cikakken kuzari masha Allah. HAU; Kuzari (Tana nufin ƙarfi da lafiya)
Showing off one’s stylishness of dress - A turance tana nufin ƙaye. Misali: Matashin ya yi shiga mai ban ƙaye a wajen bikin da sabbin kaya masu kyau. HAU: Ƙaye (Tana nufin iya kwalliya ko tsara sutura domin jan hankali ko burgewa)
Shrilling done by women to express joy - A turance tana nufin guɗa. Misali; Matan sun kaure da guɗa a lokacin da aka shigo da amaryar. HAU; Guɗa (Tana nufin wani salo na sarrafa ihu da mata ke yi musamman a lokutan farin ciki)
Side - A turance tana nufin gefe. Misali; Na ajiye kayan a gefen rijiya. HAU; Gefe (Tana nufin wani sashe)
Side of the body between thorax and hips - A turance tana nufin kwiɓi. Misali: Ya riƙe kwiɓinsa saboda ciwon da ya ji bayan ya faɗi. HAU; Kwiɓi (Tana nufin ɓangaren jikin mutum da ke tsakanin ƙirji da kwankwaso, wato gefen ciki)
Sign/Indication - A turance tana nufin ishara. Misali; Duk wanda ya yi mugunta sai ya ga ishara kafin ya mutu. HAU; Ishara (Tana nufin nuni ko alama)
1 285 286 287 288 289 332