Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Understand - A turance tana nufin gane.
Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi?
HAU; Gane (Tana nufin fahimta)
Kishiyarta; Rashin Ganewa
Understand - A turance tana nufin fahimta.
Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske.
HAU; Fahimta (Tana nufin ganewa)
Kishiyarta; Rashin Fahimta
Ungrateful - A turance tana nufin butulu
Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa.
HAU; Butulu (Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa)
Union - Tarayya, Gamayya, Ƙungiya
United Labour Congress (ULC) - Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago
United Nations (UN) - Majilisar Ɗinkin Duniya
United Nations Development Program (UNDP) - Shirin Bunƙasa Ƙasashe Na Majilisan Ɗinkin Duniya
United Nations Economic Commission for Africa (UNECA) - Kwamitin Tattalin Arzikin Afrika Na Majalisanr Ɗinkin Duniya
United Nations Educational, Scientific & Cultural Organization (UNESCO) - Hukumar Raya llimi da Al'adu da Kimiyya Ta Majisalir Ɗinkin Duniya
United Nations Environmental Program (UNEP) - Shirin Kyautata Mahalli Na Majilisanr Ɗinkin Duniya