Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
West African Women Association (WAMA) - Ƙungiyar Matan Afirka Ta Yamma
Where - A turance tana nufin inda.
Misali; Mukullin yana inda nake ajiye kayana.
HAU; Inda (Tana nufin gurin da abu yake)
Whip - A turance tana nufin bulala.
Misali; Malam ya zane ɗaliban da suka makara da bulala.
HAU; Bulala (Tana nufin busasshiya kuma nannaɗaɗɗiyar fata da ake amfani da ita wajen duka)
Whip, Flog - A turance tana nufin fyaɗa.
Misali; Ai alamajirin nan ya sha fyaɗa a gurin malaminsu.
HAU; Fyaɗa (Tana nufin duka musamman da tsumagiya)
Whirlwind - A turance tana nufin guguwa.
Misali; Bishiyar ta faɗo ne yayin da ake guguwa.
HAU; Guguwa (Tana nufin iska mai ƙarfi)
Whistling - A turance tana nufin fito.
Misali; Waye yake fito a waje?
HAU; Fito (Tana nufin fitar da iska da baki har ya ba da wata siririyar ƙara)
Whole - A turance tana nufin ilahiri.
Misali; Ya shafe ilahirin jikinsa da maganin.
HAU; Ilahiri (Tana nufin duka ko gaba ɗaya ko bai ɗaya)
wikiHausa - wikiHausa kundin ilimi (insakulofidiya) ce da ke ilimantar da jama'a yara da manya da maza da mata wajen samun ilimi a saukake, cikin harshen Hausa.
Wisdom - A turance tana nufin hikima.
Misali; Ya yi amfani da hikima wajen daidaita abokan da suka samu saɓani.
HAU; Hikima (Tana nufin dabara ko baiwa)
Wish - A turance tana nufin buri.
Misali; Zuwa ƙasa mai tsarki shi ne babban buri na.
HAU; Buri (Tana nufin abinda mutum yake so ya cimma)