Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Search - A turance tana nufin caje. Misali; Na caje yaran duka ban ga wanda ya ɗauki littafin ba. HAU; Caje (Tana nufin duba ko ina)
Search - A turance yana nufin biɗa. Misali; Ya samu abinda ya je biɗa a balaguron da ya yi. HAU; Biɗa (Tana nufin nema ko lalube)
Second (of time) - A turance tana nufin daƙiƙa. Misali; Na samu faɗuwar gaba na tsawon daƙiƙa ashirin saboda firgicin da na shiga. HAU; Daƙiƙa (Tana nufin motsawar da ƙaramin hannun agogo yake yi)
Second-hand goods - A turance tana nufin kwanceTana nufin kayan da aka taɓa amfani da su a baya sannan aka bayar ko aka siyar. Misali:Ya sayi kayan kwance a kasuwar Sabon Gari Market saboda sun fi araha. HAU: Kwance (Tana nufin kayan da aka taɓa amfani da su a baya sannan aka bayar ko aka siyar).
Secret - A turance tana nufin asiri.  Misali; An tonawa mutumin asiri, dama ya daɗe yana  satar kayan mutane. HAU; Asiri (Tana nufin abinda yake a ɓoye)
Securities & Exchange Commission (SEC) - Hukumar Kadarori da Hada-hadar Hannun Jari
See something from afar - A turance tana nufin hanga. Misali; Kamar Talatu na hanga tana shiga gidan maigari. HAU; Hanga (Tana nufin gano abu daga nesa)
Seed - A turance tana nufin iri. Misali;Iri ya yi tsada yanzu shi yasa manoma ke kokawa. HAU; Iri (Tana nufi abin da ake shukawa)
Seeking contribution from various people - A turance tana nufin karo-karo. Misali; Za mu yi masa karo-karo ya siyi babur ya kama sana'a. HAU: Karo-karo (Tana nufin haɗaka ma'ana a haɗo wancan da wannan guri ɗaya)
Seeking Devine Counsel - A turance tana nufin istihara. Misali; Ya kamata ki yi istihara a tsakanin masu neman auren ki. HAU; Istihara (Tana nufin neman zaɓin Allah)
1 281 282 283 284 285 332