Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Thickness - A turance tana nufin kauri.
Misali; Kunun da ta dama ya yi kauri sosai, sai an ƙara ruwa.
HAU; Kauri (Tana nufin abin da ba siriri ba ko kuma wanda ba ruwa-ruwa ba)
Thief - A turance tana nufin ɓarawo.
Misali;An kama ɓarawo a gidan Alhaji Iro jiya da daddare.
HAU; Ɓarawo (Tana nufin mutumin da yake sata)
Thin and Flimsy - A turance tana nufin fale-fale.
Misali; Yadin da aka ba mu fale-fale ne ba shi da kauri.
HAU; Fale-fale (Tana nufin abu mara nauyi ko kauri)
Things done or said intentionally - A turance tana nufin gayya.
Misali; Da gayya ta yi mata magana don su yi faɗa.
HAU: Gayya (Tana nufin da gangan ko ana sane)
This year - A turance tana nufin bana.
Misali; Bana damina ta yi harshe, ma'ana an yi ruwa sosai.
HAU; Bana (Tana nufin shekarar da ake ciki)
Thresh Grain - A turance tana nufin casa.
Misali; Sai an casa shinkafar sannan za a dafa.
HAU; Casa (Tana nufin cire tsaba daga cikin kwansonta, kamar shinkafa da gero da sauransu)
Throne - A turance tana nufin karaga.
Misali; Sarki yana zaune a kan karaga tun safe.
HAU; Karaga (Tana nufin kujerar mulki ko sarauta)
Throw powdered or ground thing into the mouth - A turance tana nufin hambuɗa.
Misali; Madara ta hambuɗa a baki ta gudu.
HAU; Hambuɗa (Tana nufin ɗiban abu a watsa a baki)
Thunder - A turance tana nufin tsawa yayin da ake ruwan sama.
Misali; Mun ji saukar aradu da tsakar dare ana mamakon ruwa.
HAU; Aradu (Tsawa da ake yi yayin da ake ruwan sama)
Thunder Rumbling - A turance tana nufin cida.
Misali; Ruwa ake da cida tun da safe har ga shi yamma ta yi.
HAU; Cida (Tana nufin rugugin tsawa yayin da ake ruwan sama)