Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Rope - A turance tana nufin igiya. Misali; Na gama wankin zan shanya a kan igiya yanzu. HAU; Igiya (Tana nufin abin da ake amfani da shi don yin shanyar kaya ko ɗaure abubuwa)
Rubber Research Institute of Nigeria (RRIN) - Cibiyar Binciken Noman Roba Ta Najeriya
Rule / Agreement - A turance tana nufin ƙayyade. Misali: Sun ƙayyade dokokin da za a bi wajen gudanar da taron. HAU: Ƙayyade (Tana nufin sanya doka, sharaɗi, ko iyaka, ko cimma yarjejeniya)
Rule/Law - A turance tana nufin doka. Misali; Duk wanda ya karya doka sai an masa hukunci. HAU: Doka (Tana nufin ƙa'idoji ko tsare-tsare)
Rumour - A turance tana nufin jita-jita. Misali; Ya shahara wajen yaɗa jita-jita, sai dai mu yi masa fatan shiriya. HAU; Jita-jita (Tana nufin zancen da ba shi da tabbas)
Rumours / Gossip - A turance tana nufin ƙishin-ƙishin. Misali: Na ji ƙishin-ƙishin ɗin cewa za a yi juyin mulki a ƙasar nan. HAU: Ƙishin-ƙishin (Tana nufin yaɗa maganganu ko labarai marasa tabbas)
Run - A turance tana nufin gudu. Misali; Idan ka yi gudu zuciyarka na harbawa da sauri. HAU;Gudu (Tana nufin tafiya da ƙololuwar sauri)
Running short of something - A turance tana nufin cankacakare. Misali; Kayan marmarin sun zama cankacakare. HAU; Cankakare (Tana nufin ƙarewar abu ƙarƙaf)
Rural Area - A turance tana nufin karkara. Misali; Mutanen karkara suna da karamci matuƙa. HAU; Karkara (Tana nufin ƙauye)
Rural Electrification Agency (REA) - Hukumar Raya Karkara da Wutar Lantarki
1 278 279 280 281 282 332