Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Saturday - A turance tana nufin rana ta shida a mako.  Misali; Ranar Asabar ne bikin. HAU; Asabar (Rana ce ta shida a ranakun mako)
Sayings of prophet Muhammad SAW - A turance tana nufin Hadisi. Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta. HAU: Hadisi (Tana nufin maganganun manzon Allah SAW)
Scabies - A turance tana nufin ƙurajen fata masu ƙaiƙayi Misali: Ƙarzuwa na iya yaɗuwa cikin sauri idan ba a kula da tsafta ba. HAU: Ƙarzuwa (Tana nufin cutar fata da ƙazanta ke haifarwa, inda ƙananan ƙuraje ke fitowa a sassan jiki.)
Scalp Disease - A turance tana nufin kora. Misali; Yana da kora, idan ka sa hularsa za ka iya ɗauka kuma lalura ce mai wuyar sha'ani. HAU; Kora (Tana nufin nau'in cutar fata da yake fitowa a kai)
Scheme - Shiri, Tsari
Science Teachers Association of Nigeria (STAN) - Ƙungiyar Malaman Kimiyya Ta Najeriya
Scorpion - A turance tana nufin kunama. Misali; Kunama ce ta harbi Lado a ƙafa. HAU; Kunama (Tana nufin ƙwaro mai cizo kuma mai dafi)
Scraps of food stuck to the pot - A turance tana nufin ƙanzo. Misali; Idan an gama tuwo, za mu kwashi ƙanzo don mu shanya. HAU; Ƙanzo (Tana nufin ragowar abincin da ke maƙalewa a cikin tukunya idan an gama girki)
Scratch - A turance tana nufin kuje. Misali; Amir ya faɗi ya kuje a gwuiwa. HAU; Kuje (Tana nufin jin ciwo a saman fata)
Seal - A turance tana nufin hatimi. Misali; Wasiƙar tana ɗauke da hatimin sarki. HAU; Hatimi (Tana nufin wata shaida ko alama)
1 280 281 282 283 284 332