Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Very Short - A turance tana nufin ɗigil. Misali; Na ga wani ɗan ɗigil a kasuwa yau. HAU; Ɗigil (Tana nufin ɗan gajere ko ƙanƙani)
Very Sweet - A turance tana nufin carkwai. Misali; Raken yana da zaƙi carkwai. HAU; Carkwai (Tana nufin zaƙi sosai)
Very Wet - A turance tana nufin jagab. Misali; Ruwa ya jiƙa su jagab saboda ba su daɗe da fita ba ya sakko. HAU; Jagab (Tana nufin tsananin jiƙewa)
Veterinary Conucil of Nigeria (VCN) - Majalisar Likitocin Dabbobi Ta Najeriya
Vigilante Group of Nigeria (VGN) - Hukumar Jami'an Banga Ta Najeriya
Village Head - A turance tana nufin dagaci. Misali; An naɗa shi dagaci a ƙauyensu. HAU; Dagaci (Tana nufin shugaban ƙauye)
Voice Of America (VOA) - Muryar Amurka
Voice of Nigeria (VON) - Muryar Najeriya
Wages - A turance tana nufin jinga. Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin. HAU; Jinga (Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi)
Waistcoat - A turance tana nufin falmaran. Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske. HAU; Falmaran (Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu)
1 287 288 289 290 291 300