Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Patch - A turance tana nufin faci. Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro. HAU; Faci (Tana nufin sacewar taya)  
Paternal Uncle - A turance yana nufin Baffa. Misali; Alhaji Barau baffana ne. HAU; BAffa (Yana nufin ɗanuwan mahaifi)
Patience - A turance tana nufin haƙuri. Misali; Ya samu  mace mai haƙuri shi yasa zamansu ya yi tsayi. HAU; Haƙuri (Tana nufin dangana da rashin ɗaukar mataki idan an maka laifi) Kishiyarta; Rashin haƙuri
Paw - A turance tana nufin dagi. Misali; Na ga shatin dagi a ƙofar gida, amma ya fi kama da na kare. HAU; Dagi (Tana nufin tafin ƙafar dabbobi masu ƙafa huɗu kamar kare da mage da sauransu)
Pay - A turance tana nufin biya. Misali; An biya ma'aikata albashin su na wannan watan. HAU; Biya (Tana nufin bayar da kuɗi sakamakon wani aiki, ko bayar da wani abu a dalilin yin wani aiki)
Pay Attention - A turance tana nufin kula. Misali; Idan za ki tsallaka titi ki kula saboda motoci na wucewa da gudu. HAU; Kula (Tana nufin mayar da hankali a kan abu)
Peace Corps of Nigeria (PCN) - Rundunar Zaman Lafiya Ta Najeriya
Pediatric Association of Nigeria (PAN) - Kungiyar Likitocin Yara Ta Najeriya
Penalty to atone for breaking certain islamic law - A turance tana nufin kaffara. Misali; Azumi uku ake yi a kaffarar rantsuwa. HAU; Kaffara (Tana nufin abin da mutum zai yi don karya rantsuwa ko sakamakon kisa da sauransu. Akan yi kaffara da azumi ko ciyarwa da sauransu)
Pencil - A turance tana nufin fensir. Misali; 'Yan aji ɗaya da fensir suke rubutu. HAU; Fensir (Tana nufin abin rubutu)
1 246 247 248 249 250 300