Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Over there - A turance tana nufin can. Misali; Na ajiye butar a can. HAU; Can (Tana nufin nesa da inda ake)
Overturn/ Upside down - A turance tana nufin birkice. Misali; Ya birkice ɗakin yana neman maɓallin rigarsa. HAU; Birkice (Tana nufin a juya abu daga sama zuwa ƙasa)
Pagan - A turance tana nufin arne.  Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne. HAU; Arne (Tana nufin wanda ba shi da addini)
Palm wine - A turance tana nufin bammi. Misali; Bammi yake sha shi yasa kullum ba ya cikin hayyacinsa. HAU; Bammi (Abin sha ne mai gusar da hankali)
Panting, Gasping - A turance tana nufin haki. Misali; Gudun da na yi ya sa ni haki. HAU; Haki (Tana nufin yin numfashi sama-sama da sauri)
Pardon/Forgiveness - A turance tana nufin gafara. Misali; Allah mai gafara ne ga bayinsa. HAU;Gafara (Tana nufin yafiya musamman ta Allah SWT)
Parent Teachers Association (PTA) - Ƙungiyar Iyaye da Malaman Makaranta
Parents - A turance tana nufin iyaye. Misali; Wajibi ne biyayya ga iyaye idan mutum yana son gamawa lafiya. HAU; Iyaye (Tana nufin mahaifi da mahaifiya)
Parliamentary Staff Association of Nigeria (PASAN) - Ƙungiyar Ma'aikatan Majalisar Dokoki Ta Najeriya
Pastor - A turance tana nufin fasto. Misali; Maƙococinsa babban fasto ne. HAU; Fasto (Tana nufin limamin coci)
1 245 246 247 248 249 300