Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

World Boxing Council (WBC) - Hukumar Wasan Dambe Ta Duniya
World Boxing Organization (WBO) - Kadaurar 'Ƴandambe Ta Duniya
World Health Organization (WHO) - Hukumar Lafiya Ta Duniya
World Medical Association (WMA) - Ƙungiyar Likitoci Ta Duniya
World Trade Organization (WTO) - Hukumar Kasuwanci Ta Duniya
World Youth Organization (WYO) - Kadaurar Matasa Ta Duniya
Worship - A turance tana nufin bauta. Misali; Musulmai sun yarda da Allah shi ne kaɗai abin bauta. HAU; Bauta (Tana nufin sadaukarwa da biyayya ga abinda mutum ya yarda da shi)
Worth, Value - A turance tana nufin daraja. Misali; Zinare na da daraja a halin yanzu. HAU; Daraja (Tana nufin muhimmanci ko tsada)
Yam - A turance tana nufin doya. Misali; Doya za mu dafa yau da rana. HAU; Doya (Tana nufin ɗaya daga cikin nau'in abinci wanda ke sa ƙarfin jiki)
Yandagaji - Waɗanda ba kwararrun 'yanwasa ba a harkar wasanni.
1 244 245 246 247 248 251