Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
National Water Resources Institute (NWRI) - Cibiyar Nazarin Albarkatun Ruwa Ta Ƙasa
National Youth Council of Nigeria (NYCN) - Majalisar Matasan Najeriya
National Youth Service Corps (NYSC) - Hukumar 'Ƴanhidimar Ƙasa/Hukumar Masu Hidimar Ƙasa
Native Doctor - A turance tana nufin boka.
Misali; Zuwa gurin boka kan sa mutum ya rasa imanin sa.
Kishiyarsa; Malam
HAU; Boka (Tana nufin jakadan shaiɗanun aljanu, wanda yake bauta musu da yin abinda suka umarce shi)
Navel - A turance tana nufin cibiya.
Misali; Jaririn yana da cibiya babba, sai an gasa masa sosai.
HAU; Cibiya (Tana nufin sashen jiki da ke tsakanin ciki da mara)
Naƙalta - Iyawa,Gogewa, samun kwarewa a kan wani abu ko aiki ko sana'ar da mutum ya koya ko yake aiwatarwa yau da gobe.
Near - A turance tana nufin kusa.
Misali; Ana siyar da wainar gero a kusa da gidanmu.
HAU; Kusa (Tana nufin dab da)
Need - A turance tana nufin buƙata.
Misali; Ina buƙatar kwanaki masu yawa kafin na kammala wannan aikin.
HAU; Buƙata (Tana nufin abinda ake muradi ko ake so)
Neighing - A turance tana nufin haniniya.
Misali; Dokunan suna ta haniniya tun safe.
HAU; Haniniya (Tana nufin kukan doki)
Net Bag - A turance tana nufin cali.
Misali; A zuba tumaturan a cikin cali saboda kar ya lalace.
HAU;Cali (Tana nufin jaka mai raga-raga)