Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
New opportunities/ Progress - A turance tana nufin buɗi.
Misali; Allah ya ƙara buɗi ga duk masu sauƙaƙawa talakawa.
HAU; Buɗi (Tana nufin samun damammaki ko cigaba a kasuwanci ko karatu ko wasu al'amura)
New Partnership for Africa’s Development (NEPAD) - Gidauniyar Haɗin Guiwar Bunƙasa Sabuwar Afirka
News Agency of Nigeria (NAN) - Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya
Newspaper - A turance tana nufin jarida.
Misali; Dattijai na son karanta jarida don jin halin da duniya take ciki.
HAU; Jarida (Tana nufi takarda mai ƙunshe da rubutun labarai)
Newspaper Proprietors Association of Nigeria (NPAN) - Ƙungiyar Mamallaka Kamfanin Jarida Ta Najeriya
Next year - A turance tana nufin baɗi.
Misali; Auren sai baɗi za a yi shi.
HAU; Baɗi (Tana nufin shekara mai zuwa)
Nigarian Instutite of International Affairs (NIIA) - Cibiyar Nazarin Hulɗar Jakadanci Ta Najeriya
Niger Basin Authority (NBA) - Hukumar Kogin Kwara
Niger Delta Development Commission (NDDC) - Hukumar Raya Yankin Neja Delta
Nigerian (Football) Referees Association (NRA) - Ƙungiyar Alƙalan Ƙwallon Ƙafa Ta Najeriya