Tag: addu;a

  • Awaɗanne Ranaku Ne Ake Yin Ittikaafi?

    Awaɗanne Ranaku Ne Ake Yin Ittikaafi?

    Amsa: Ana yin ittikaafi ne a goman ƙarshen Ramadan.

    Hujja: “Shugaban halitta yana zaman ibada a masallaci a goman ƙarshen Ramadan, har Allah ya karɓi rayuwarsa”.

    Marawaici Ummuna A’isha, littafi: Sahihu Muslim, Sahihul Bukhari.

    Domin karanta cikakken bayani akan Wane Lokaci Ne Ake Shiga, Sannan Wane Lokaci Ake Fita? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Da Wane Lokaci Ne Mutum Zaiyi Buɗa Baki A Shari’ah? danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Shin Akwai Addu’a Da Akeyi Kafin Mutum Yayi Buɗa Baki?

    Shin Akwai Addu’a Da Akeyi Kafin Mutum Yayi Buɗa Baki?

    Amsa: Akwai addu’a da mai yin buɗa baki zaiyi, amma sai bayan yayi buɗa bakin ake yin addu’ar.

    Hujja: “Zahabaz zama’u, wabtallatul uruqu, wasabbatal ajaru inshaAllah”.

    Marawaici Ibn Umar, littafi: Sunan Abu Dawud, Sunan Nassa’i, Haakim, Baihaqi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Lokacin Buɗa Baki, Lokaci Ne Na Amsa Addu’ar Mai Azumi Akan Wata Buƙatarsa? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Mutum Zai Yi Idan Ya Yi Buɗa Baki A Gidan Mutane danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba

    Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba

    An karɓo daga Mu’awiyya Ibn Haidah (Radiyallahu anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Haƙiƙa yin saƙaka a asirce tana gussar da fushin Ubangiji, Kuma haƙiƙa ayyukan alhairi suna kawar da mummanar faɗuwa”(Musibu da Asarori) Ɗabarani 951; Sahihul Jami’il Sagir (3759).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Mu Yi Alhairi, Mu Guji Rowa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasallam) Yake Shan Ruwa. danna nan

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    Falalar Sassauci Ga Wanda Ake Bi Bashi

    An karɓo daga Abul Yasar (Radiyallahu anhu) ya ce: Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce:

    “Wanda ya yi jinkiri ga wanda yake cikin ƙunci ko ya yafe masa abin da yake bin sa, Allah zai sanya shi a cikin inuwarsa”

    (Muslim: 3014).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sadaƙa Tana Kawar Da Musiba danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za A Ci Jarabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauki danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Yin Sadaka A Asirce

    Falalar Yin Sadaka A Asirce

    An karɓo daga Abu Harairata (Radiyallahu anhu) yace: Annabi (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce: “Mutane bakwai Allah zai sanya su a cikin inuwarsa a yinin da babu wata inuwa sai inuwarsa:

    1) Shugaba mai adalci.

    2) Matashi da ya taso kan bautar Allah.

    3) Mutumin da zuciyarsa take a rataye a masallaci.

    4) Da mutanen da suke ƙaunar juna saboda Allah, suka haɗu a haka, suka rabu a haka.

    5) Da mutumin da kyakkyawar mace mai matsayi ta neme shi, sai ya ce: Ni ina tsoron Allah.

    6) Da mutumin da ya yi sadaka a ɓoye ta yadda hagunsa ba ta san abinda damansa ta bayar ba.

    7) Da mutumin da ya tuna Allah yana shi kaɗai, har ya yi ƙwalla. (Bukhari 1423, Muslim 1031).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Ba wa Ɗan Uwa Sadaƙa danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Zikiri

    Falalar Zikiri

    Allah Maɗaukakin Sarki ya ce:-

    “Fazkuruunii azkurkum washkuruu lii walaa takfuruunii

    { ku ambace ni, zan ambace ku, ku gode mini kada ku butulce min} (Baƙara, aya ta 152).

    Yaa ayyuhal – lazina amanuzkurul laaha zikran kasiiran wasabbihuuhu bukratan wa’asiilaa“.

    { Ya ku waɗanda suka yi Imani, ku ambaci Allah ambato mai yawa } (Ahzab, aya ta 41).

    Wazzakiriinal – laaha kasiiran wazzaakiraati a’addallahu lahum magfiratan wa’ajran aziimaa

    { Da masu ambaton Allah da yawa maza, da masu ambaton sa mata, Allah ya tanadar musu gafara da lada mai girma }

    (Ahzab, aya ta 35).

    Wazkur Rabbaka fi nafsika tadharru’an wa khifatan wa duunal jahri minal ƙauli bil guduwwi wal’asaali walaa takun minal Gafiliina”.

    { Kuma ka ambaci Ubangijinka a cikin zuciyarka, kana mai ƙasƙantar da kai da tsoro, ba da ɗaukaka murya ba (tsaka-tsaki tsakanin asirtawa da bayyanawa), da safe da maraice, kuma kada ka zamo daga cikin gafalallu } (A’araf, aya ta 205).
    Kuma Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: “Misalin wanda yake ambaton Ubangijinsa da wanda ba ya ambaton Ubangijinsa, kamar misalin rayayye da matacce ne”.

    Kuma yace: { Shin ba na ba ku labarin mafi alherin ayyukanku ba, kuma mafi tsarkinsu a wajen Sarkin da yake mallakar ku, kuma mafi ɗaukakarsu ga darajojinku, kuma mafi alheri gare ku da ku haɗu da abokan gabarku ku riƙa dukan wuyayinsu, suna dukan wuyayinku? Suka ce ka ba mu labari. Ya ce: Ambaton Allah Maɗaukaki}.

    Kuma ya ce: { Allah Maɗaukaki yana cewa: Ni ina tare da zaton bawana da ni, kuma ina tare da shi idan ya ambace ni. Idan ya ambace ni a cikin jama’a zan ambace shi a cikin jama’ar da ta fi su alheri, in ya kusance ni taki ɗaya zan kusance shi kamu guda, in ya kusance ni kamu guda zan kusance shi tsawon gaɓa guda, in ya zo min ya na tafiya zan zo masa ina gaggawa }.
    Daga Abdullahi ibn Busr, Allah ya yarda da shi, ya ce: Ya Ma’aikin Allah! Shari’o’in Musulunci sun yi yawa a gare ni; saboda haka ka nuna mini wani abu da zan yi riƙo da shi. Ya ce; { kar harshenka ya gushe face yana ɗanye daga ambaton Allah }.

    Kuma Mai tsira da amincin Allah ya ce; { wanda ya karanta harafi ɗaya daga Littafin Allah yana da (ladan) kyakkyawan aiki ɗaya saboda shi; kuma dukkan kyakkyawan aiki ɗaya yana da (ladan) misalinsa goma. Ba ina cewa Alif Lam Mim harafi ba ne a’a, Alif harafi ne, Lam harafi ne, Mim harafi ne}.

    Kuma daga Uƙbata ibn Amir, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya fito alhali muna cikin rumfa, sai ya ce; A { wane ne daga cikinku zai so ya fita kullum da safe zuwa ƙoramar Buɗhan ko Aƙiƙ; ya dawo da taguwa biyu masu manyan tozuna, ba tare da yin wani laifi ba, ko yanke zumunta? } muka ce; “Muna son haka” .

    Ya ce: { Ɗayanku ya je masallaci ya nemi sani, ko ya karanta ayoyi biyu daga cikin Littafin Allah; Mabuwayi mai ɗaukaka, ya fi masa taguwa biyu, ayoyi uku sun fi masa taguwa uku; ayoyi huɗu sun fi masa taguwa huɗu, da kwatankwacin adadinsu na raƙuma }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; {wanda ya zauna a wani waje bai ambaci Allah a wajen ba; wannan zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah. Wanda ya kwanta a makwanci bai ambaci Allah a wajen ba; shi ma zai zamanto masa abin bibiya a wajen Allah}.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da suka zauna a wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba; kuma ba su yi salati ga Annabinsu ba, face ya zamo musu abin bibiya; in Allah ya so ya yi musu azaba, in ya so ya gafarta musu }.

    Kuma mai tsira da amincin Allah ya ce; { Babu wasu mutane da za su tashi daga wani majalisi da ba su ambaci Allah a cikinsa ba, face sun zama kamar sun tashi daga kan mushen jaki ne; kuma zai zamanto musu abin da- na- sani }.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’o’in Tashi Daga Barci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Addu’a Bayan An Gama Cin Abinci

    Alhamdu lil laahil lazii aɗ’amanii hazaa wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ciyar da ni wannan (abincin); ya azurta ni da shi, ba tare da wata dabara ko ƙarfi daga gare ni ba}.

    Allamdu lil laahi hamdan kasiiran ɗayyiban mubaarakan fiihi gaira makfiyyi walaa muwadda’in walaa mustagnan anhu Rabbunaa“.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, yabo mai yawa, kyakkyawa, kuma abin sanya albarka a cikin sa; (Allah) wanda ba a ɗauke masa azurta bayinsa, kuma ba a rabuwa da shi (a bar nema daga wurinsa), kuma ba a wadatuwa ga barinsa; shi ne Ubangijinmu}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Baƙo Ga Wanda Ya Gayyace Shi Cin Abinci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Cin Abincin Manzon Allah (Sallallahu alaihi wassallam) danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Shiekh Sa’id Ibn Ali Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Shugaban Istigfari

    Shugaban Istigfari

    An karɓo daga Shaddad Ɗan Aus (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: shugaban Istigfari shi ne ka ce :

    Allahumma anta Rabbi, laa ilaha illa anta, khalaƙatani, wa ana abduka; wa ana ala ahdika, wawa’adika mastaɗ’atu, abu’u laka, bini’imatika alayya; wa abu’u laka, bi zanbi fagfir lii, fa innahu laa yagfiruz zunuba illa anta”

    Ya ce: wanda ya faɗi wannan da safe yana mai cikakken imani sai ya mutu a wannan yinin kafin yamma; to shi ɗan Aljanna ne, idan da daddare ne yana mai cikakken imani, sai ya mutum kafin safiya; to shi ɗan Aljanna ne” (Bukhari 6306).

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Haƙiƙa ni kaina ina yin istigfari ina tuba fiye da sau saba’in a yini ɗaya”. (Bukhari 6307, 3259).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Salati Ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Salati Ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) Bayan Tahiyya danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Sujjadar Tilawar Alƙur’ani

    Addu’ar Sujjadar Tilawar Alƙur’ani

    “Sujada wajhii lillazii khalaƙahu wa shaƙƙa sam’ahu wa basarahu bi haulihi wa ƙuwwatihi (Fatabaarakal-laahu ahsanul khaaliƙiina)”.

    {Fuskata ta yi sujada ga wanda ya halicce ta, kuma ya tsaga ji da gani a gare ta; da iyawarsa da kuma ƙarfinsa. (Allah mafi gwanintar masu halitta, ya girma, kuma alherinsa ya yawaita}.

    “Allaahummaktub lii bihaa indaka ajran, wa dha’a annii bihaa wizran waj’ilha lii indaka zukhran, wa taƙabbalhaa minni kamaa taƙabbaltahaa min abdika Dawuda”.

    {Ya Allah! Ka rubuta mini lada saboda ita (sujadar), ka kankare min zunubi saboda ita; ka sanya ta ta zamo taskar arziki gare ni a wajen ka, kuma ka karɓe ta daga gare ni kamar yadda ka karɓe ta daga bawanka Dawuda}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tahiyya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Wanda Ya Yi Sabon Aure, Ko Ya Sayi Abin Hawa

    Addu’ar Wanda Ya Yi Sabon Aure, Ko Ya Sayi Abin Hawa

    Idan ɗayanku ya auri mace, ko ya sayi bawa mai hidima, to ya ce:-

    Allaahumma innii as’aluka khairahaa wa khaira maa jabaltahaa alaihi, wa a’uzu bika min sharrihaa wa sharri maa jabaltahaa alaihi“.

    {Ya Allah! Ina roƙon ka alherinta da alherin da ka ɗabi’antar da ita a kansa; kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da ka ɗabi’antar da ita a kansa}.

    Idan kuma ya sayi raƙumi, to ya kama tozon raƙumin ya faɗi kwatankwacin wannan (addu’ar).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Idan Mutum Ya Yi Fushi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Sakamakon Zalunci Yake danna nan.