Tag: addu;a

  • Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Yadda Nau’ikan Sihiri Suke Da Kuma Matakan Magance Su

    Nau’ikan Sihiri

    a. Akwai kurciya

    b. Dan baka

    c. Sihirul firaƙ

    d. Sihirul muhabba

    e. Sihirul jini

    f. Sihirul tasrif

    g. Sihirul sariƙ

    Wannan su ne nau’i kaɗan daga cikin nau’ikan sihiri. Kowanne kuma da yadda ake yin sa. Ana yin sihiri mace ta saukar wa da ‘yar uwarta jini, ta rinƙa yin jini a duk lokacin da mijinta ke ɗakinta. Ana yin sihiri uba ya ji ya tsani ‘ya’yan wata sai na ɗaya. A na ma mutum sihiri ya ga duk abinda ya samu ya ruguje, ka ga kana samu amma kuma abun yana rushewa. Kuma ana iya yin sihiri a hana budurwa aure. Sannan ana iya yin sihiri mace ta rinƙa warin jaɓa, saurayi ya zo wajenta ya ji tana wari.

    Ana yi wa yaro sihiri dan a lalata rayuwarsa, ya zama ɓarawo, ɗan iska ko kuma ɗan shaye-shaye. Koma dai wane irin sihiri ne. Allah bai taɓa yin ciwo ba sai da maganinsa.

    Akwai matakai da ake bi domin a karya sihiri. Wani sihirin za a iya yi da an karya shi sai ya dawo, wani kuma da an karya shi yake tafiya. Sakamakon rashin kariya ne da tun farko ba a yi ba shi yasa da an karya zai iya dawowa.

    Da yawan waɗanda sihiri ke jikinsu ba su cika yadda da cewa sihirin ne ba. Gane sihiri aka yi maka, harka nemi maganin karya shi da na kariya shi ma arziki ne. Ga matakan da ya kamata ka ɗauka wajen maganin kariya yadda duk wani sihiri ba zai kamaka ba da kai da iyalanka, haka tsafin mai tsafi ba zai kamaka ba. Ko da mutum yana magana yana fitar da wuta a bakinsa saboda sihiri, to da yardar Allah ka fi ƙarfinsa. Sai dai a ganka ana faman duka amma ka kasa faɗuwa, ka zama shagwan mada. A kan yi amfani da ayoyi guda 33 a cikin Al-Ƙur’ani domin neman kariya daga sihiri.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Za ka karanta su ne bayan fatiha Suratul baƙarah aya ta 1-5 Ayatul kursiyyu aya ta 255 Amanar rasul zuwa ƙarshen surar Suratul A’araf aya ta 54-56

    Sannan ka karanta;

    “ƙulid’ullaha awid’ur rahman, ayyam ma tad’u falahul asma’ul husna, wala tajhar bi salatika wala tukhafit biha wabtagi baina zalika sabila”

    Har zuwa ƙarshen suratul Isra’i

    Da kuma suratus safat aya ta 1-11 Da suratur rahman aya ta 33-35

    Sannan ka karanta;

    “lau anzalna hazal ƙur’ani ala jabalin lara’aitahu khashi’an mutasaddi’an min khashyatillah, wa tilka amthalu nadribuha linnasi la’allahum yata fakkarun”

    Zuwa ƙarshen suratul hashri

    Da surar jinn aya ta 3-9 Sannan suratul buruj aya ta 20-22

    Waɗannan ayoyin akan samu ruwan rijiya ko na zam-zam ko ruwan sama a karanta su kowacce ƙafa bakwai a tofa a cikin ruwan, a sa za’afaran ko na mai, ko na gari, ko kuma na ciyawa. Sai a rinƙa ɗiba kaɗan ana sha da safe da kuma in za a kwanta. Za kuma a iya karanta su a tofa a cikin man zaitun da man habba da man kwa-kwa ko na riɗi, a rinƙa shafawa a jiki. Mutum zai iya shafawa da iyalansa gaba ɗaya. Muddin kai da iyalanka za ku rinƙa shafa wannan addu’ar, ba wani tsafin mai tsafi ko sihirin mai sihiri da zai yi tasiri a jikinka insha Allah. Sannan wannan addu’ar ka karanta ta a gidanka kullum da safe, Ubangiji zai ba iyalanka da gidanka kariya daga dukkan sharrin mutum da aljan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kariya Daga Hassada, Maita, Da Sharrin Aljanu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Maganin Damuwa danna nan

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa

    Wannan addu’ar mutum yakan yi ta idan ya shiga cikin damuwa ko ya shiga cikin wani hali, ko tashin hankali; ya rasa yadda zai yi sai ya lazimci karanta wanan addu’ar. Allah zai fidda shi daga cikin wannan tashin hankalin da damuwa.

    An ruwaito daga Imam Ali Hassan Shazah, yana koyawa almajirinsa wannan addu’ar. Ga ta kamar haka;

    “Ya wasi’u ya Aleem, ya zal fadlul azeem, wa in tamsasni bi durrin fala kashifa lahu illa anta, wa’in turidni bi khairin fala raadda bi fadlik, tusibu man tasha’u min ibadak wa antal gafurur rahim”

    Akan so duk lokacin da ka yi salla ko ka yi wani aikin alkhairi ka karanta wannan addu’ar, Ubangiji Allah zai yaye maka damuwarka In Sha Allah. Ansamo wannan addu’ar daga littafin MAFATIHUL FARAJ shafi na 110. Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Kyautata Tsakanin Ka Da Ubangiji Da Neman Gafara dannna koren rubutu. Don karanta Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Addu’o’in Tashi Daga Barci

    Addu’o’in Tashi Daga Barci

    “Alhamdu lillaahil- lazii ahyaana ba’ada maa amaatanaa wa’ilaihin nushuuru”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya rayar da mu bayan ya ɗauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi yake}.

    Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce; wanda ya farka da daddare yace:

    “Laa’ilaha illallahu wahdahu la shariikalahu lahul mulku walahul hamdu wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun. Subhanallahi wal hamdu lillaahi walaa ilaaha illallahu Allahu akbaru walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil laahil aliiyil aziimi, Rabbigfirlii”.

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma shi Mai iko ne a bisa komai, Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu ƙarfi sai ga Allah, Maɗaukaki, mai girma Ya Ubangijina! Ka gafarta mini}.

    Wanda ya faɗi wannan za a gafarta masa, idan kuma ya yi addu’a za a amsa masa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za a karɓi sallarsa.

    “Alhamdu lillaahil lazii afaani fii jasadii waradda alayya ruuhi wa’azina lii bi zikrihi”

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo min da raina, kuma ya ba ni izinin ambatonsa}.

    “Inna fii khalƙis- saamaawati wal ardhi wakhtilaafil laili wannahari la ayaatil li ulil albaab allaziina yazkurunallaaha ƙiyaaman waƙu’udan wa alaa junuubihim wayata fakkaruuna fii khalƙis- samaawati wal ardhi rabbanaa maa khalaƙta hazaa baaɗilan subhaanaka faƙinaa azaban naari rabbanaa innaka man tudkhilun nara faƙad akhzaitahu wamaa liz zaalimiina min ansaari rabbanaa innanaa sami’ina munaadiyan yunadii lil imani an aminuu bi rabbikum fa’amanna rabbanaa fagfirlanaa zunuubanaa wa kaffir annaa sayyi’ atinaa watawaffanaa ma’al abraar rabbanaa wa atinaa maa wa’adtanaa alaa rusulika walaa tukhzina yaumal ƙiyaamati innaka laa tukliful mii’ada fastajaaba lahum rabbuhum annii laa udhi’u amala amilin minkum min zakarin au ansaa ba’adhukum min ba’adhin fallaziina haajaruu wa ukhrijuu min diyaarihim wa uzuu fii sabiili waƙaataluu wa ƙutiluu la’ukaffiranna anhum sayyi’ atihim wala udkhilannahum jannatin tajrii min tahtihal anhaaru laziina kafaruu fil bilaadi mataa’un ƙaliilun summa ma’awaahum jahannamu wa bi’isal mihaadu laakinil laziina taƙau rabbahum lahum jannatun tajrii min tahtihal anhaaru khaalidiina fiihaa nuzulan min indil laahi khairun lil abraar wa’inna min ahlil kitaabi laman yu’uminu bil laahi wamaa unzila ilaikum wamaa unzila ilaihim khaashi’ina lillaahi laa yashtaruuna bi ayaatil laahi samanan ƙaliilan ulaa’ika lahum ajruhum inda rabbihim innal laaha sari’ul hisaabi yaa ayyuhal laziina aamanuus biruu wa saabiruu wa raabuɗuu Wattaƙullaaha la’allakum tuflihuuna”.

    (Ali imrana, aya ta 190 zuwa ƙarshen surar)

    {Haƙiƙa a cikin halittar sammai da ƙassai, da saɓawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma’abota hankula. (su ne) waɗanda suke ambaton Allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingiɗe, suke kuma tunani a kan halittar sammai da ƙassai (suna cewa):

    “Ya Ubangijinmu! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa kai, duk wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu mataimaka. Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa; ku yi imani da Ubangijinku. Sai muka yi imani.

    To ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun ayyukanmu, ka kuma karɓi rayukanmu tare da mutane nagari. Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alƙawari da shi a kan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alƙiyama. Haƙiƙa, kai ba ka saɓa alƙawari.

    Sai Ubangijinsu ya amsa musu (cewa); Haƙiƙa, Ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace sashinku daga sashi yake.

    To, waɗanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yaƙi, kuma aka kashe su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu; (wannan) sakamako ne daga Allah.

    Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai- koman waɗanda suka kafirta a cikin garuruwa ta ruɗe ka. Jin daɗi ne ɗan ƙanƙani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta.

    Amma, waɗanda suka ji tsoron Ubangijinsu, suna da aljannatai waɗanda ƙoramu suke gudana ta ƙarƙashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga Allah; abin da kuwa ya zo daga wajen Allah shi ya fi ga managarta, kuma haƙiƙa akwai daga ma’abota Littafi wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar.

    Zuwa gare su, suna masu ƙanƙan da kai ga Allah, ba sa musanya ayoyin Allah da ɗan tamanni ƙanƙani. Waɗancan suna da ladansu a wurin Ubangijinsu. Haƙiƙa Allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi haƙuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin haƙuri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron Allah ko kwa rabauta}.

    (Ali Imran, 190 zuwa ƙarshen surar).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Lokuta Da Yanayi Da Kuma Wuraren Da Ake Karɓar Addu’a

    Yana cikin kamala da girman karamci da rahamar Allah ya sanya a kowanne lokaci dare da rana bawa ya fuskanci Allah yayi addu’a za’a amsa masa.

    Tare da akwai wasu lokuta da gurare waɗanda Allah jalla wa’alaa ya albarkacesu da daraja ta musamman, wanda addu’a acikinsu keda tasiri na musamman. Ga wasu daga ciki:

    1. Addu’a ranar Arafah.

    2. Addu’a a Lailatul ƙadr.

    3. Addu’a akashi daya cikin ukun karshen dare.

    4. Addu’a bayan tahiyar karshe.

    5. Addu’a a cikin sujjadah.

    6. Addu’a tsakanin kiran Sallah da Iƙama.

    7. Addu’a yayin saukar ruwan sama.

    8. Addu’a ranar juma’a.

    9. Addu’a yayin shan ruwan zam-zam.

    10. Addu’a yayin da ake kiran sallah

    11. Addu’a yayin tashi daga bacci.

    12. Addu’a a kwanaki goman farko na Dhul-hijjah.

    13 .Addu’a a cikin ka’abah.

    14. Addu’a yayin gama karatu ko karantarwa.

    15. Addu’a yayin da mayaƙa sukayi sahu.

    16. Addu’a a majalissan da ake ambaton Allah.

    17. Addu’a yayin da imani ya ƙaru a zuciya.

    18. Addu’a bayan zare ran mamaci.

    19. Addu’a yayin jifan jamraat.

    20. Addu’a akan dutsen safa.

    21. Addu’a akan dutsen marwa

    22. Addu’a a mash’aril haram.

    23. Addu’a yayin ziyarar marar lafiya.

    24. Addu’a gabannin sallar azzahar.

    25. Addu’a a watan Ramadhan.

    26. Addu’a yayin sahur ga mai azumi.

    27. Addu’a yayin buɗa-baki ga mai azumi.

    28. Addu’a yayin shiga tsanani, matsi da ƙunci.

    29. Addu’a da addu’ar zun-nun Alaihis salaam.

    30. Addu’a da Istirja’i.

    31. Addu’a a multazam.

    32. Addu’a a Makam Ibrahim.

    33. Addu’a yayin karatun suratul fatiha.

    34. Addu’a yayin ƙarfafuwar Mahabbah da Ikhlasi a zuciya.

    35. Addu’a yayin carar zakara.

    Duba:

    1. Du’aa na Dr. Yassir Qadhi

    2. Addu’a wa Manzilatahu Minal Aqidatil Islamiyyah na Dr. Jilan Alarusiy wanda rubuntunsa ne, na Masters Degree kulliyatud da’awah, Qismul Aqidah a Jami’atul Islamiyyah Madinatul Munawwarah a shekarar 1410A.H.

    3. Ahmiyyatud Du’a wa Kaifiyyatahu fis Sunnatin Nabawiyyah na Dr.Ibrahim al-Hamd.

    Domin karanta cikakken bayani akan Alkunyar Da Ake Wa Manzon Allah (S.A.W) danna koren rubutun nan.

  • Addu’a A Lokacin Da Mutum Zai Hau Abin Hawa

    Addu’a A Lokacin Da Mutum Zai Hau Abin Hawa

    Bismil laahi wal hamdu lil laahi subhaanal lazii sakkhara lanaa hazaa wamaa kunnaa lahu muƙriniina wa innaa ilaa rabbinaa lamunƙalibuuna, alhamdu lil laahi, alhamdu lil laahi, alhamdu lil laahi, Allaahu akbar, Allaahu akbar, Allaahu akbar, subhaanakal laahumma innii zalamtu nafsii fagfirlii fa’innahu laa yagfiruz zunaaba illaa anta”.

    {Da sunan Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Tsarki ya tabbata ga (Ubangiji) wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Haƙiƙa mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Allah ne mafi girma. Tsarki ya tabbata gare ka, ya Allah! Haƙiƙa ni na zalunci kaina, ka gafarta min, domin babu wanda yake gafarta zunubai sai kai}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Idan Mutum Zai yi Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa danna nan.

    Edita; RMK

  • Yadda Ake Amsa Wa Kafiri Idan Yayi Sallama

    Yadda Ake Amsa Wa Kafiri Idan Yayi Sallama

    Amsa Sallama – Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Idan ma’abota littafi (yahudu da nasara) suka yi muku sallama, to ku ce musu; “wa’alaikum”. {Ku ma haka}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare danna nan.

    Don karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya danna nan

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan

  • Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi

    Yadda Ake Addu’ar Sanya Tufafi

    “Alhamdu lil laahil lazii kasaani haaza (sauba) wa razaƙaniihi min gairi haulin minnii walaa ƙuwwatin”.

    {Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, wanda ya tufatar da ni wannan (tufa); kuma ya azurta ni da ita; ba tare da wata dabara daga gare ni ba ko wani ƙarfi}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Ake Ma Wanda Ya Sanya Sabuwar Tufa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Shekara Nawa Shugaban Halitta Ya Yi Azumin Ramadan A Rayuwarsa?

    Shekara Nawa Shugaban Halitta Ya Yi Azumin Ramadan A Rayuwarsa?

    Amsa: Ya yi azumin Ramadan ne na tsahon shekara tara.

    Domin karanta cikakken bayani a kan A Cikin Azumin Ramadan Na Shekaru Tara Da Ya yi, Sau Nawa Ya yi Azumi Talatin, Sau Nawa Ya yi Azumi Ashirin Da Tara? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Manzon Allah Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi Wasallam) danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Shin Mace Ma Zata Iya Shiga Ittikaafi?

    Shin Mace Ma Zata Iya Shiga Ittikaafi?

    Amsa: Za ta iya shiga ittikaafiidan bata da miji, idan kuma tana da miji, sai idan yayi mata izini.

    Hujja: “Matan Shugaban halitta sunyi ittikaafi bayansa”.

    Marawaici Ummuna A’isha. Littafi: Sahihul Bukhari Sahihu Muslim, Fathul Baari.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Akwai Wata Ibada Ce Da Akafi Son Mai Ittikaafi Ya Dinga Yi? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Idan Mutum Baya Azumi Saboda Uzuri Na Shari’ah, Shin Zai Iya Duk Ibadar Da Mai Azumi Yake Yi Kamar Sadaka, Ƙiyamul Laili, Karatun Alqur’ani, Salati, Istigifari, Da Sauran Ayyukan Lada?

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.

  • Wane Lokaci Ne Ake Shiga, Sannan Wane Lokaci Ake Fita?

    Wane Lokaci Ne Ake Shiga, Sannan Wane Lokaci Ake Fita?

    Amsa: Ana shiga ne bayan sallar asuba, wasu malaman kuma sunce, kafin rana ta faɗi Shugaban halitta yake shiga, wajen zamansa ne, sai bayan sallar asuba yake zuwa, yana fita ne bayan magriba, a daren idi, kafin shigowar yinin idi.

    Hujja: Marawaici Abu Huraira, littafi: Sahihul Bukhari, Sahihu Muslim, Abu Hanifa, Maalik, Sha’fi’i, Ahamad.

    Domin karanta cikakken bayani akan Akwai Bambanci Ne Tsakanin Yinin Idi Da Daren Idi? danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Sallar Idi danna nan.

    Danna link ɗinnan; https://chat.whatsapp.com/JtD82AjZZmo3AtSTaKP05r domin shiga WhatsApp group namu na Ramadan.