Tag: addu;a

  • Yadda Ake Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    Yadda Ake Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    “Allaahumma Rabbas samaawaatis sab’i wamaa izlalna, wa Rabbal shayaaɗiini wamaa aƙlal na, Rabbas shayaaɗiini wamaa adhlalna, wa Rabbar riyaahi wamaa zaraina, as’aluka khaira hazihil ƙaryati wa khaira ahlihaa wa khaira maa fiihaa, wa a’uza bika min sharrihaa wa sharri ahlihaa wa sharri maa fiihaa”.

    {Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da abin da suka rufe; kuma Ubangijin ƙassai bakwai da abin da suke ɗauke da shi; kuma Ubangijin shaiɗanu da waɗanda suka ɓatar; sannan Ubangijin iska da abin da ta yayyaɗa! Ina roƙon ka alherin wannan alƙarya; da alherin mutane da ke cikinta, da alherin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsari da kai daga sharrinta; da sharrin mutanenta; da sharrin abin da ke cikinta}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Shiga Kasuwa danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W) danna nan.

    Edita; RMK

  • Addu’ar Komowa Daga Tafiya

    Addu’ar Komowa Daga Tafiya

    Abdullahi ibn Umar, Allah ya yarda da shi, ya ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya kasance idan ya kama hanyar dawowa daga tafiya wani yaƙi; ko aikin hajji ko umara, idan ya hau tudu sai ya yi kabbara sau uku; sannan ya ce:

    “Laa ilaaha illallaahu wahdahu laa shariika lahu, lahul mulku walahul hamdu, wahuwa alaa kulli shai’in ƙadiirun, aayibuuna taa’ibbuna, aabiduuna li rabbinaa haamiduuna, sadaƙal laahu wa’adahu, wa nasara abdahu wa hazamal ahzaaba wahdahu”.

    {Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaɗai; babu abokin tarayya a gare shi. Mulki nasa ne (shi kaɗai); kuma shi mai iko ne a kan komai. Mu masu komawa ne, masu tuba, kuma masu godiya ne ga Ubangijinmu. Allah Ya gaskata alƙawarinsa, Ya taimaki bawansa, Ya ruguza rundunonin kafirai shi kaɗai}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yin Kabbara Da Tasbihi Yayin Da Ake Tafiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Edita; RMK

  • Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Addu’a Idan Aka Ji Haushin Karnuka Da Daddare

    Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce; ‘Idan kuka ji haushin karnuka, da kukan jaki da daddare, to ku nemi tsarin Allah daga gare su; don kuwa su suna ganin abin da ba kwa gani’.

    Domin karanta cikakken bayani akan Falalar Yaɗa Sallama A Cikin Al’umma danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Munafuntar Al’umma Da Rashin Fayyace Alƙibla danna nan.

    Don karanta Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza danna nan

  • Yadda Ake Addu’ar Shiga Da Fita Daga Banɗaki

    Yadda Ake Addu’ar Shiga Da Fita Daga Banɗaki

    “(Bismillahi) Allahumma inni a uzu bika minal khubusi wal khabaa’isi”.

    {(Da sunan Allah) Ya Allah ina neman tsarinka daga shaiɗanu maza da shaiɗanu mata}.

    Addu’ar Fita

    “Gufraanaka”

    {Ya Allah gafararka (nake nema)).

    Domin karanta cikakken bayani akan Zikiri Kafin (Gabanin) Da Bayan An Gama Alwala danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sallar Alwala Da Falalarta danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Haramcin Zalunci Da Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta

    Haramcin Zalunci Da Tasirin Addu’ar Wanda Aka Zalunta

    An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “An ba da umarni a yi wa wani bawan Allah bulala ɗari a cikin kabarinsa, sai ya yi ta roƙo yana addu’a a yi masa afuwa har sai da ta dawo bulala ɗaya.

    Da aka shaula masa sai kabarin ya cika da wuta ya suma. Da ya farfaɗo sai ya ce: “Shin akan me kuka zane ni?” Sai ya ce: “Saboda ka taɓa yin sallah ba ka da tsarki, kuma ka taɓa wuce wani ana zaluntarsa ka ƙi ka taimaka masa”.

    Abus Shaikh Ibn Hayyan ne ya rawaito shi a cikin Littafin Attaubikh.

    Ƙarin Bayani

    Lallai ne a taimakawa waɗanda ake zalunta a ƙwato musu haƙƙinsu, wannan nauyi ne akan hukumomi da ɗaiɗaikun mutane, kada a bar zalunci ya yi ta tafiya har ya zama jiki, sai fushin Allah da azabarsa su shafi kowa.
    Shi ma azzalumi a taimaka masa ta hanyar hana shi aikata zalunci da hukunta shi da kuma toshe dukkannin ƙofofi da hanyoyin da duk dama da yake yin zaluncin.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Shugabanci A Musulunci (Hadisai Tamanin Da Biyu Akan Shugabanci) wanda Shehu Mansur Dala ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Edita; Rumasa’u M. kallamu

  • Addu’ar sanya sabon Kaya A Musulunci

    Addu’ar sanya sabon Kaya A Musulunci

    An rawaito daga Abu Sa’eed Allah ya ƙara masa yarda yace: Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance idan ya yi sabon tufa ya kan kira shi da sunan shi sannan yace:

    اللَّهمَّ لك الحمدُ أنت كسوْتنِيهِ أسألُك من خيرِه وخيرِ ما صُنِعَ له ، وأعوذُ بك من شرِّهِ وشرِّ ما صُنِعَ له

    Allahumma lakal hamdu Anta kasautanihi, As’aluka min khairihi wa khairi ma suni’a lahu, wa A’uzu bika min sharrihi wa sharri ma suni’a lahu

    Abu dawud: 4020  Turmidhi: 1727

    Sharhin Addu’ar:

    Ubangijina ina maka godiya kai ne ka azurta ni da wannan tufafi, ba tare da iyawa ta ba, ina roƙon ka ka sanya wannan tufafi ya zamto mai taimako na wurin aikata alheri, Ka haɗa ni da alherinsa, ina kuma neman tsarinka daga sharrinsa sa: ka kiyaye ni kada ya zamto wannan tufafi ya zamto sanadiyyar saɓa maka.

  • Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Hanyar Korar Aljanu Da Kariya Daga Dawowar Su

    Kamar yadda muka sani aljani wata halitta ce da Allah ya yi ta ya kuma ɓoye ta ba za mu ganta ba; amma ita Allah ya hore mata za ta ganmu. Kamar yadda Allah (Subhanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Alƙur’ani mai girma a suratul A’araf aya ta ashirin da takwas (28).

    Sannan Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace aljanu sukan shiga jikinmu kamar yadda jini ke gudana a cikin jikinmu; da haka muke sanin cewa aljanu suna ma da haƙuri dan sun fi mu haƙuri. Don da mu ke ganinsu, su ba sa ganinmu, kuma mu shiga cikin jikinsu kamar yadda Allah ya hore musu su shiga cikin namu, da mun cutar da su fiye da yadda suke cutar da mu. Da haka ne za ka gane lallai aljanu suna da haƙuri fiye da mu mutane. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Nau’ikan Aljanu Suke danna koren rubutun nan. Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Za A Gane Matsalolin Aljanu Tare Da Magance Su danna koren rubutun nan. Edita; Rumasa’u Muhammad kallamu
  • Yadda Alamomin Jinnu Yake

    Yadda Alamomin Jinnu Yake

    Za mu ɗauki kaɗan daga cikin jinnu mu bayyana alamominsa da kuma magungunansa.

    Jinnul Gawas

    Waɗannan jinnu sun yi zamani da Annabi Suleiman (Alaihis Salam). Kamar yadda Allah (Subahanahu Wata’ala) ya faɗa a cikin Al Ƙur’ani mai girma a cikin suratus Saad, aya ta 37:

    “Wash shayaɗina kulla banna’in  wa gawwas”

    Akasarin wannan aljanun suna daɗewa a duniya kuma akasarinsu musulmai ne amma duk da yake akwai kafirai a cikinsu kaɗan. Kuma akasarinsu sun fi rayuwa a cikin ruwa ko cikin tafki ko kuma rijiya. Kuma sukan yawan shiga jikin yara.

    Alamominsu Jinnul Gawas :

    Mutum zai ji yana yawan zama a cikin bayi shi kaɗai, ko ka ga yana yawan wasa da ruwa ko kuma ya yi alwala sau da yawa ya ɗauka duk alwalar ba ta yi ba. Ko da tsananin sanyi ake yi shi zai iya yin wasa da ruwa ba tare da ya samu wata matsalar ba. Zai so ya rinƙa jiƙa jikinsa kuma za ka ga yana yawan wasa da dabbobi, ko kuma ya rinƙa yawan ganinsu a cikin mafarkinsa sannan a cikin barci zai dinga firgita ko ya rinƙa yawaita mafarkin kifi. Sannan wani lokacin idan ya yi tsanani, yakan kai da mutum yarinƙa faɗuwa.

    Hanyar Da Ake Bi A Magance Su

    Akan samu ruwa mai kyau tsaftatacce ko ruwan sama ko na rijiya sai a karanta surorin nan kamar haka, kowacce ƙafa ɗaya sai a tofa a cikin ruwan. Ga surorin kamar haka;
    • Suratul baƙarah
    • Suratul Yunus
    • Suratu dukhan
    • Ayatul azab wal ƙahar
    • Ayatul garaƙ wal bahar
    Waɗannan su za a tofa a cikin ruwa a ba shi ya sha da safe da yamma. Sannan akan so a ɗebi ruwan da aka yi wannan addu’ar ana dafa masa kifi da shi har sai ya samu lafiya. Sannan a karanta waɗannan ayoyin a cikin muski yana shafawa a ƙirjinsa da kansa. In Sha Allah zai samu lafiya.

    Jinnul Ashiƙ

    Wannan jinnu ya fi takurawa mutane, musamman mata, ko matan aure, ko bazawara, ‘yan mata ya hanasu aure, matan aure ya raba musu aure kuma bazawara ya daƙile duk abinda zai sa su yi aure. Shi jinnu ne da yake auran mace ya zame mata tamkar mijinta, in kuma tana da miji ya haramta mata duk wani jin daɗin aure ta zama kurum gata nan kamar hoto a gidan mijin. Duk da ana samun jinnul ashiƙa ta auri mutum, namiji ko da yana da aure ta cire masa son matarsa; zai iya shafe shekara da shekaru suna kwanciya ɗaki ɗaya, gado ɗaya amma ba tare da ya yi sha’awarta ba. Amma da ya kwanta sai wannan aljanar ta rinƙa zuwar mishi a cikin bacci yana mu’amalantarta ta zama tamkar matarsa. In kuwa aka yi rashin sa’a ta auri wanda bai taɓa yin aure ba; to in ba an yi da gaske ba takan zama matarsa ce har lokacin da zai bar duniya. Ta cire masa duk ƙaunar aure ko kuma ƙaunar wata mace ya gwammace ya yi ta zama a haka har ya bar duniya; ba ya so wani ya yi masa maganan aure shi kuma ba zai yi ba.

    Alamomin Jinnul Ashiƙ

    Mace ta rinƙa yawan samun faɗuwar gaba, yawan fushi ba gaira babu dalili; mace ta ji ta tsani kowa ko mijinta ba ta son gani, ta rinƙa keɓe kanta daga cikin mutane ta ji ta fi so ta rinƙa zama ita kaɗai. Ta rinƙa jin wasi-wasi a cikin zuciyarta ana raɗa mata mutuwa za ta yi; mace ta rinƙa ji kamar ta bar gidan da take zaune ko ta ƙwalla ihu, wata ma haka kawai za ka ga tana hawaye ko tana kuka ba tare da an mata laifi ba, ga yawan mafarkai daban-daban. Kamar mafarkin saduwa ko mafarkin taron biki ko mafarkin kin ɗau ciki; ko kuma ki yi mafarkin kin haihu ko ki yi mafarkin ga ki kina shayarwa. Wata ma za ta ga mijin nata a mafarkin babanta ne wata kuma ta ga yayanta ko wani mutumin da take jin kunyarsa; sai ta gan shi yana saduwa da ita. Wata kuma sai ta ga ga mata ‘yan uwanta suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi; ko ta ga maza suna saduwa da junansu tana kallo tana jin daɗi. Za ta ji daɗi a mafarkin in ana saduwa da ita amma in mijinta ya zo kusa da ita, sai ta ji kamar an sa mata wuta ta ji kamar an aiko mata mala’ikan mutuwa; duk yadda mijinki zai faranta miki ba ya burgeki, za ki ji ba kya son sa kwata-kwata, ba kya san ganinsa ko kaɗan. Abin lura a nan shi ne duk mafarkin da kika yi a gurin gaskiya ne. Domin karanta cikakken bayani akan Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Addu’ar Matafiyi

    Addu’ar Matafiyi

    Wannan addu’a ce ga wanda zai yi tafiya kuma yana tsoron kada wani ya cutar da shi ko ya cutar da iyalinsa bayan ya tafi; ko kuma a rasa masa wani abun, to zai iya yin wannan addu’ar. Har ya je ya dawo Allah ba zai bari a cutar da shi ko kuma iyalinsa ba. Yayin da ya shirya zai tafi sai ya karanta wannan addu’ar;

    Ga Addu’ar kamar haka;

    “Allahumma inni a’uzhubika min wa’tha’is safar wakabatil manzar, wa su’il munƙalab; fil mali wal ahli wal walad, ya man huwa aƙrabu min habil warid; ya fa’alan lima yurid; ya man yahulu bainal mar’i wa ƙalbihi hul bainana (idan mutum ɗayane sai yace baini wa baina.. inda za a kira sunansa; idan kuma sunfi haka sai ace baini wa bainana tare da ambatar sunansu); wa baina man yu’zina bi haulika wa ƙuwwatika ya kafi kulla shai’in wala yakfi minhu shai’in; ikfina ma yuhimmuna min amrid dunyan wal akhirati ya arhamur rahimin”

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Yaye Damuwa danna koren rubutun nan. Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutun nan. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu
  • Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Matakan Da Za A Bi Domin Rabuwa Da Jinnu

    Akwai hanyoyi da yawa wajen rabuwa da irin waɗannan aljanu da ma wasu ba irin wannan ba. Ya zama duk inda aljani yake ajikin mutum sai ya gudu ya bar shi.

    Matakan Rabuwa Da Jinnu: Matakin farko akan so mara lafiya ta cire duk wani hoto a ɗakin da take kwana sannan ta kiyayi yawan kalle-kalle. Sannan ta sabarwa kanta kwanciya da alwala, idan za ta iya yi wa kanta ta yi da kanta, in kuma za ta sa ne a yi mata shi kenan, abinda dai ake so a yi shi yadda ya kamata. Duk lokacin da za ta kwanta bacci bayan ta yi alwala sai ta karanta waɗannan ayoyin kamar haka; 1. Aya ta ɗaya zuwa goma cikin suratul Kahf 2. Sai kuma ƙarshen suratul Mu’minun 3. Aya ta 54 zuwa ta 56 a cikin suratul A’araf Sannan ta karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Allahumma inni auzhubika min su’i ahlami, wa’astajiruka min talaubish shaidan fil yaƙzati wal manami”

    In kika karantata shi kenan sai ki yi baccinki. In Sha Allah muddin za ki kikayi wannan shawarar ba ki da matsala.

    Haɗin Turare

    Wannan turare aljani ba ya sonsa, duk inda ka turara aljani ba zai so wajenba In Sha Allah. Hannit Lubazzakar Habbatussaud Tafarnuwa Kajiji

    Waɗannan su ne za a haɗa su guri ɗaya sai a rinƙa turarawa. In kika yi haka ba ke ba aljanu In Sha Allah.

    Daddawar batso Habbatus sauda Kajiji Kustul hindi Al-mum Su ma turarawa za ayi da yardar Allah aljani zai bar jikin mutum da kuma gida. Sannan za a samu ruwa mai kyau, an fi son na zam-zam in ba a samu ba sai a yi amfani da ruwan rijiya ko kuma ruwan sama, ya zamo dai ruwan mai tsafta ne. Sai a yi alwala a nemi za’afaran mansa ko kuma garinsa sannan a samu ma’ul wardi sai kuma jan muski kaɗan sai kuma a samu ganyen magarya a niƙa shi a zuba kaɗan a ciki sannan a karanta wannan ayoyin kamar haka kowacce ƙafa bakwai ana yi ana tofawa cikin ruwa ko kuma numfashin na sauka cikin ruwan.

    Ga ayoyin kamar haka;

    Suratul Fatiha Suratul Baƙarah aya ta 1-5 Suratul Baƙarah aya ta 101-102 Suratul Baƙarah aya ta 255-256 Ƙarshen Suratul Baƙarah aya ta 273-277 Suratul A’araf aya ta 54-56 Suratul Yunus aya ta 90-92 Suratul Isra’i aya ta 109-111 Suratul Mu’minun aya ta 113-118 Suratul Kahfi aya ta 1-10 Suratul Saffat aya ta 1-11 Suratul Mulk Suratul Jinn Suratul buruj aya ta 1-3 Suratul Kafirun Suratul Ikhlas Suratul Falaƙ Suratul Nas Waɗannan ayoyin su za a karanta a tofa a cikin ruwan sai a ba wa mara lafiya tasha da safe kafin ta ce komai, ta shafe kanta da ruwan kaɗan, sai kuma da daddare kafin ta kwanta bacci ya zama shi ne ƙarshen abin da za ta sha ta kuma shafe jikinta gaba ɗaya.

    Sannan waɗannan ayoyin za a karanta su kamar yadda suke, a samo mayuka kamar haka;

    Man habba Man kwakwa Man alayyadi Man zaitun Jan Muski (ɗan kaɗan) Man ridi A haɗe su wuri guda a karanta waɗannan ayoyin a tofa a ciki ta rinƙa shafawa a jikinta musamman in za ta kwanta bacci. Duk irin taurin kai da aljani yake da shi to zai bar jikinsa da yardar Allah. Domin karanta cikakken bayani akan Hanyar Ƙona Aljani Ajikin Mutum danna koren rubutu. Domin karanta bayani akan Addu’a A Lokacin Da Mutum Ya Fitinu Da Wasuwasi A Cikin Sallah danna koren rubutu. Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu