Tag: addu;a

  • Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Tashin Hankali

    Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Tashin Hankali

    Wannan addu’ar za a iya karanta ta idan mutum na cikin mawuyacin hali; ko kuma mace ta rasa mijin aure; ko kuma mutum na cikin yawan bashi ko bashin gidan haya da dai sauran su. 

    An ruwaito daga Hassanul-al-basari, yace wata rana yana cikin tafiya a cikin garin Iraƙ, sai ya ga wani mutum kamar an ciro shi daga ƙabari, hankalinshi a tashe, sai Hassanul-al-basari yake tambayarshi me ya same ka? 

    Sai mutumin yake cewa; labarina akwai tashin hankali a cikinsa, da firgitarwa, amma ka yi alƙawari za ka ɓoye sirrina ba za ka sanar da kowa ba. Sai yace Hajjaj ne ya tsare ni a gidan yari shekaru uku; kuma aka hukunta za a kashe ni tare da wasu.

    Yace ina zaune wata rana a cikin gidan yari sai aka zo aka tafi da wasu mutanen da za a kashe. Bayan an zo an sare musu kai, sai aka dawo aka ce da mu gobe kuma za a kashe ku. Sai na gigice hankalina ya tashi, abinci na kasa ci saboda na san gobe kwana na zai ƙare. Ina cikin tashin hankali har na kasa bacci. Sai gab da asuba bacci ya ɗauke ni, sai na yi mafarki a cikin baccin an ce da ni; tashi ka yi sallah raka’ah biyu 2, idan ka idar da sallar ka karanta wannan addu’ar;

    “Ya manla yashgaluhu shai’un an shai’in, ya man a hada ilmuhu bima zara’a wa bara’a, anta aliun bi khafayatil umuri, muhsy wa sawisus sudur, waanta bil manzalil a’ala, wa ilmuka bil manzilil adna, ta’alaita uluwwun kabira, ya mugithu agithni, wa fukka asri, wakshif durri faƙad naƙida sabri”

    Yace sai na tashi na yi alwala a cikin halin da nake ciki na fargaba, na yi sallah raka’ah biyu 2 kamar yadda na ji a mafarkina, na haddace abinda aka faɗa min a mafarkina, ban bar kalma ɗaya ta kuɓuce min ba daga ciki abin da aka gaya min.

    Wallahi ban kai ƙarshe ba daga cikin kalmomin da na sani sai na ga wani haske, sai na ga wani mutum. Yace koda na kalla, sai na ga ƙofar gidan yarin an buɗe ta, sai kawai na ji an ce tashi ka fita. Shi ne na taso na kama tafiya, Allah ya kawo min mafita, Allah ya warkar da ni damuwa ta, sannan na samu wadata a rayuwa ta.

    Wannan addu’ar duk mutumin da ya samu kansa a cikin wata damuwa ko wani tashin hankali, ko al’amura sun caɓe masa, ya rasa yadda zai yi da kansa, to ya dinga tashi cikin dare ya yi nafila ya karanta wannan addu’ar. Da yaddar Allah, Allah zai kawo masa ƙarshen damuwarsa In Sha Allah.

    An samo wannan addu’ar a cikin littafin MUFATIHUL FARAJ shafi na 108.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’a Idan Mutum Yana Cikin Damuwa danna koren rubutu.

    Don karanta bayani a kan Addu’a Gatan Mumini danna koren rubutu.

    Edita:@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Neman Falala

    Addu’ar Neman Falala

    Wannan addu’a ana yin ta domin neman falala da buɗi akan abinda ka sa a gaba, karatu ko kasuwanci.

    Akan so ka zama mai yawan salatul-duha; kamar yadda aka ruwaito daga Abu Hurairah (Radiyallahu Anhu) yace; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya min wasicci da abubuwa guda uku (3) su ne salatul-duha, sallah raka’ah huɗu lokacin da rana ta fito (da ƙarfe 9 zuwa 10 na safe); Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) yace; ta fi duniya da abunda ke cikinta da kuma yin azumi uku a kowane wata; da kuma salatul-witr, shafa’i da witr kafin a kwanta bacci.

    A yi sa’a ma’abocin yin salatul-duha ne kafin ka fita harkokin ka ka yi sallar raka’ah biyu ko huɗu. Bayan ka yi sallama, kayi salatin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) da hailala sai ka karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Allahummaj al awwala hazan nahar salaahan, wa ausadahu falaahan, wa akhiruhu najaahan, as aluka khaira dunya wal akhira, ya arhamur rahimin. Labbaika lahumma labbaik, wa sa’daika wal khairu fi yadaka, wa minka ilaika”

    Wannan Addu’ar Neman Falala; An samo ta ne daga littafin DUA’U YARFA’U BALA’I, shafi na 49.

    Don karanta bayani akan Falalar Tafiya Masallaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Addu’ar Da Abi Zaril Gaffari Yake Yi danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Tashi Daga Bacci

    Yadda Ake Addu’ar Tashi Daga Bacci

    An karɓo daga Aisha (Radiyallahu Anhu) tace Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam); ya kasance yana tashi daga bacci zai karanta wannan addu’a;

    Ga Addu’ar Tashi Daga Bacci kamar haka:

    “La ilaha illa anta subhanakallahumma astagfiruka li zhanbi; wa as’aluka rahmatikallahumma zidni ilman, wala tazig ƙalbi ba’ada iz hadaitani; wahab min ladunka rahmatan innaka antal wahhab” (Abu Dawud)

    Ana so duk wanda ya tashi daga bacci, na safe ne ko na rana ko kuma na yamma to ya karanta wannan addu’ar yayin da ya farka, to Ubangiji zai ba ka kariya daga duk wani abu da zai cutar da kai a ranar kuma Allah zai sa ka samu nutsuwa da wadatar zuciya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Sauƙin Bashi danna nan.

    Domin karanta bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Neman Biyan Bashi danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Biyan Bashi

    Yadda Ake Addu’ar Biyan Bashi

    Addu’ar Biyan Bashi – Wannan addu’a ce ga wanda bashi ya yi wa yawa, yana so ya biya, ko kuma mutum na cikin tsanannin ƙuncin rayuwa.

    Akan so ka tashi cikin dare, ko kuma wani lokacin ka yi alwala, ka yi sallah raka’a biyu; sannan ka karanta wannan addu’a;

    Bismillahir rahmanir rahim, allahummag firli zanbi, wa was’is khulƙi, wa ɗayyib li kasbi, wa ƙanni’ni bima razaƙtani, wala tuzhib ƙalbi ila shai’in sarraftahu anni”.

    Sannan ana so duk lokacin da ka idar da sallar asuba, ko kuma wata sallah cikin salloli biyar, to ka yawaita karanta wannan addu’ar. Yawaita karanta wannan addu’ar yakan sa Allah (Subhanahu Wata’ala) ya warware maka dukkan bashin dake kanka. Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ne ya bai wa Sayyidina Aliyu (Radiyallahu Anhu). Ya ce da shi; “Shin ina so in ba ka tumaki guda dubu biyar, ko kuma na ba ka wasu kalmomi biyar. Sai sayyidina Aliyu ya ce,” Ya Rasulullahi ka ba ni kalmomi guda biyar, sai sun fi dabbobi dubu biyar”.

    Addu’ar Biyan Bashi – An samo wannan addu’ar ne a cikin littafin Miftahul Farj, shafi na 110.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Biyan Buƙata A Wajen Allah (S.W.T) danna nan.

    Don karanta bayani a kan Lokuta Zaɓɓaɓu Na Karɓan Addu’a danna nan

  • Falalar Tafiya Masallaci

    Falalar Tafiya Masallaci

    Tafiya masallaci domin yin ɗaya daga cikin salloli biyar bayan alwala. A lokacin da mutum ya ƙare alwala, idan namiji ne, duk takun da zai yi ko ɗaga ƙafa yayin tafiyar; sai an ɗaga darajarsa, an yafe masa zunubansa; haka ma kuma mace lokacin da take tafiya wajen da za ta yi sallah, ita nan ne masallacinta.

    Ana so mutum ya yi tafiya cikin nutsuwa domin tara lada mai yawa. Isowar sa masallaci ko kuma isowar ta wajen da take yin sallah, idan da dama, ana so a yi nafila raka’a 2 kafin sallar farilla.

    Ga sunayen nafilfilin salloli biyar da yadda ake gabatar da su.

    Ana kiran su da Larabci (Assunanur rawaatibi, Assunanun attabi’atu lil fara’idi). Ma’anar su a harshen Hausa ita ce, jerarrun sunnoni.

    Idan da Asuba ne ana yin raka’a biyu, wacce ake kiranta da Larabci (raka’ataanil fajri) ma’ana raka’a biyu lokacin fitowar alfijir, in Azahar ne ana yin raka’a biyu ko huɗu kafin sallar Azahar, sannan kuma raka’a biyu bayan sallar azahar.

    Idan da La’asar ne kuma raka’a biyu kafin sallar La’asar; in Magriba ce raka’a biyu bayan sallar Magriba, da isha’i kuma raka’a biyu bayan sallar Isha’i.

    Shi ne yawan su ya kai raka’a 14 idan mutum ya yi huɗu kafin Azahar, idan kuma biyu ya yi, sun tashi raka’a 12 kenan.

    Idan mutum ya yi sallama, yana zaune inda yake bayan nafila kafin sallar farilla; mala’iku za su dinga masa addu’a suna cewa Allah ya masa rahama; ya masa gafara, ya yi sallah masa afuwa matsawar bai yi hadasi ba kuma bai cuci wani a lokacin;wannan falalar duk ɗaya ne ga mace ko na miji.

    Domin karanta bayani a kan Fa’idojin Da Sallar Nafila Ta Ƙunsa danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Sallar Tahajjudi danna nan

  • Addu’o’in Neman Tsayar Da Ruwan Sama

    Addu’o’in Neman Tsayar Da Ruwan Sama

    “Allaahumma hawaalainaa walaa alainaa, Allaahumma alal akaami wazziraabi, wa buɗuunil waudiyati, wa manaabitis shajari”.{Ya Allah! Ka sanya shi ya zuba a kewayenmu, ba a kanmu ba. Ya Allah! Ka sanya shi a kan jigayi da duwatsu, da cikin rafuka, da wajen saiwoyin itatuwa}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Ganin Jinjirin Wata danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Ganin Jinjirin Wata

    “Allahu akbar, Allaahumma ahillahu alainaa bil amni wal imani, was salaamati wal Islami, wat taufiiƙi lima tuhibbu Rabbana wa tardhaa, Rabbanaa wa Rabbukal laahu”.
    {Allah ne Mafi girma. Ya Allah! Ka sanya tsayuwarsa a gare mu ta zamo kwanciyar hankali ce da imani, da aminci da Musulunci, da kuma gamon Ƙatar da abin da kake so, ya Ubangijinmu, kuma kake yarda da shi. Ubangijinmu da Ubangijinka (ya kai wannan jinjirin wata!) shi ne Allah}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Cin Abinci danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunnah wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi.

  • Ladubban Addu’a A Musulunci

    Ladubban Addu’a A Musulunci

    WAƊANDA ALLAH KE GAGGAUTA AMSA ADDU’ARSU

    1. Addu’ar Annabawan Allah.
    2. Addu’ar mala’ikun Allah
    3. Addu’ar wanda aka zalunta.
    4. Addu’ar mai Ƙarfin imani da tsoron Allah.
    5. Addu’ar da mai biyayya ga iyayensa.
    6. Addu’ar mai Azumi.
    7. Addu’ar shugaba adali.
    8. Addu’ar iyaye (nagartattu) ga ‘ya’yansu.
    9. Addu’a ga ɗan uwa avbayan idonsa.
    10. Addu’ar mai jihadi.
    11. Addu’ar mai hajji ko umrah.
    12. Addu’ar mai dauwama cikin zikirin Allah.
    13. Addu’a ga mai karatun AlQur’ani.
    14. Addu’ar matafiyi (tafiya ta halal).
    15. Addu’ar mai taka tsantsan wajen haram;abincinsa,abin shansa,tufafinsa da mazauninsa.

    ABUBUWAN DA SUKE KAWO JINKIRIN AMSA ADDU’A

    1. Shirka ƙarama da babba.
    2. Ta’amuli da haram ci, sha ko tufafi.
    3. Nauyin zunubai da ƙeƙashewar zuciya.
    4. Barin umarni da kyakkyawa da hani ga mummuna.
    5. Tafseel (Dalla-dalla) a cikin addu’a
    6. Wasa da wargi a cikin addu’a.
    7. Addu’a da zuciya gafalalliya mai shagala.
    8. Rashin ladabi a gaban Allah Jalla Wa’ala.
    9. Ta’allaƙa addu’a ga mashi’ah (In ka so)
    10. Gaggawa a cikin addu’a.
    11. Al-Istihsaar( Shi ne mutum ya bar addu’a saboda gajiya da kosawa)
    12. Rokon abin da hukuncin Allah ya gama da shi.
    13.Saja’i a cikin addu’a (shi ne mutum ya tilasta wa kansa daidaita harafin ƙarshen jumlolin addu’a )
    14. Bidi’o’i a cikin addu’a.
    15. Roƙon wani abu da ya shafi saɓon Allah ko yanke zumunta.

    Duba:
    1. TAS’HIHUD DU’A na Dr.BAKR
    2 ARRIYADUN NAZIRAH na Shk.Abdur Rahman Nasir Sa’adiy

    Domin karanta nasbar Manzo allah danna nan

  • Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    Yadda Za A Ci Jarrabawar Bala’in Da Ya Tsananta A Cikin Sauƙi

    A duk lokacin da ka samu kanka cikin wani hali na matsi a rayuwa, to ka tuna daman can Allah yana jarrabar bayinsa da masifu daban-daban.

    Allah Ya ce:

    “Wallahi sai mun jarraba ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da tawayar dukiya, da asarar rayuka da na kayan marmari, kuma albishir ga masu haƙuri”.
    (Baqara:115).

    Ka ga tunda mun fahimci kowane irin tsanani daga Allah ne; To, ka ga mun san babu mai yaye mana, sai Allah Maɗaukakin Sarki.

    Mene ne abin yi kenan?

    Abin yi shi ne mu rungumi wannan ƙaddara, da yin haƙuri, da koyi da yadda Annabi (S.A.W) ya ce mu yi.

    Jarrabawa na iya zama mabambanta a tsakaninmu. Wani rashin iyaye, wani cuta, wani talauci, wani rashin ‘ya’ya da dai sauransu.

    Wani lokacin kuma, ya zama Annoba ce da Allah ya jarrabi dukkanin al’umma. Wato kamar ciwon sarƙewar numfashi (Corona).

    Shi Musulmi duk abin da ya same shi na sharri da wahala ba za ka same shi yana raki ba. Kuma yai ta mita ko laƙanawa wani shi ya ja masa. Koda yake rauni irin na ɗan Adam ba a hana mutum baƙin ciki ba. Amma dai zai zama mai dogaro ga Allah.

    Matakan cin jarrabawar bala’in da yayi tsanani

    • Mu ƙasƙantar da kawunanmu. Mu tuba, mu yi nadama. Mu yawaita istigfari.
    • Mu yawaita karatun Ƙur’ani.
    • Mu bincika tsakaninmu da iyayenmu mu gyara. Mu dinga kyautata musu.
    • Ma’aurata su gyara tsakaninsu.
    • Mu yawaita sadaka.
    • Mu yawaita addu’a Allah Ya yaye mana. Ya kawo mana mafita.
    • Mu yawaita: Hasbunallahu wa ni’imal wakeel.
      Lahaula wala quwwata illa billah.
      La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimn.

    A ƙarshe mu sani, mai sauƙi ne a wajen Allah ya yaye mana kowanne irin bala’i. Saboda haka, mu gaggauta gyara tsakaninmu da Mahaliccinmu. Sannan kuma ga dukkanin jarrabawa irin ta Annoba; Mu bi shawarar malamai, da shugabanni, da ma’aikatan lafiya.

    Da bin waɗannan in sha Allahu sai ka ga mun yi nasara. Mun ci jarrabawar bala’in da ya tsananta cikin sauƙi.

    Wallahu A’alam.

    Duba Yadda Ake Tsaftace Baki