Tag: addu;a

  • Falalar Ƙulhuwallahu Ahad

    Falalar Ƙulhuwallahu Ahad

    Falalar Ƙulhuwallahu Ahad – An karɓo hadisi daga Abu Sa’idil Khudri, Allah ya yarda da shi ya ce: Ɗan ‘uwana Ƙatada ɗan Nu’uman ya ce:

    Haƙiƙa wani mutum ya yi tsayuwar dare a lokacin Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam), sai ya yi ta karanta ƙulhuwallahu Ahad (Bayan Fatiha), bai ƙara wata sura ba.

    Da gari ya waye sai ya zo wajen Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ambata masa tsayuwar daren da ya yi da ƙulhuwallahu Ahad, yana ganin kamar surar ta yi kaɗan. Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ya ce: “Na rantse da wanda raina yake hannunsa tabbas tana daidai da ɗaya bisa uku (1/3) na Alƙaur’ani”. (Wato wajen samun lada). Bukhari ne ya rawaito shi.

    Kuma an Karɓo daga Anas ɗan Malik, Allah ya yarda da shi ya ce; Ya Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) Ina matuƙar son wannan sura: “Ƙulhuwallahu Ahad”. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: “Son da kake yi mata ya shigar da kai Aljanna”. Tirmizi da Ibn Hibban ne suka rawaito shi.

    Sannan an karɓo wani hadisin daga Buraida ɗan Husayyib Allah ya yarda da shi ya ce; “Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ji wani mutum yana cewa:

    “Ya Allah ina roƙon ka, ina mai tabbatar da na shaida tabbas kai kaɗai ne abin bauta; babu wani abin bautawa bisa cancanta (na gaskiya) sai kai kaɗai; ɗayan da ake nufa da buƙata, wanda bai haifa ba; kuma ba a haife shi ba, kuma babu wani wanda ya yi daidai da shi”.

    Sai Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Tabbas ka roƙi Allah da sunansa wanda in har aka roƙe shi, to zai bayar da abin da aka roƙa; kuma idan aka kira shi da shi, to zai amsa”. Imam Ahmad, Abu Dawud, Tirmizi da wasunsu ne suka rawaito shi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sahihin Sirrin Ƙulhuwallahu Ahad danna nan

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Surah A Cikin Sallah danna nan

  • Ɗagowa Daga Ruku’u

    Ɗagowa Daga Ruku’u

    Ɗagowa Daga Ruku’u: Bayan kowacce gaɓa ta koma mazauninta; ya tsaya daram kar ya mayar da hannuwansa kan ƙirjinsa, wato; (Qabdu) su ne kaɗai zai bar su a sake kamar yadda mafi yawan malamai suka ce.

    Sannan sai ya yi kabbara, ya tafi sujuda; zai tafi sujuda ne da hannuwansa a wajan wasu malamai; ko da gwuiwar kafafunsa, a wajan wasu malamai ana so ya saɓawa yadda raƙumi ke faɗuwa idan zai kwanta.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Yin Sallar Istihara danna nan.

  • Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai

    Addu’o’i Domin Neman Tsari Daga Azzalumai

    Addu’o’in Tsari Daga Azzalumai; An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas’ud (Radiyallahu Anhu) ya ce; Idan ɗayanku yana jin tsoron wani azzalumin shugaba sai ya ce:

    Allahumma rabbussamawatis sab’i, wa rabbul arshil azim, kun li jaran min wa atba’ihi min halƙika minal jinni wal insi an yafruɗa alayya ahadun minhum au an yaɗga, azza jaruka wa jalla sana’uka wa la’ilaha illan anta”.

    Asbahani ne ya ruwaito shi daga Ibn Mas’ud danganta maganar ba ga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam) (Mauƙuf).

    An karɓo daga Abdullahi Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu) ya ce; “Idan ka je wurin wani shugaba mai kwarjini wanda kake jin tsoron zai afka maka sai ka ce:

    Allah Akbar Allah a’azzu min khalƙihi jami’an, Allahu a’azzu mimma akhafu wa ahzaru, a uzu billahillazi laa ilaaha illaa huwa almumsikus samawati an yaƙa’a na alal ardi illa bi iznihi min sharri abdika wa junudihi wa atba’ihi wa ashya’ihi minal jinni wal insi. Allahumma kun li jaaran min sharrihim jalla sana’uka wa azza jaruka wa tabarakas muka, wa laa ilaahha gairuka”(sau uku).

    Ibn Abi Shaiba ne ya ruwaito shi, daga Ibn Mas’ud.

    Ƙarin Bayani

    Wannan hadisi sahihi ne mauƙufan wato zuwa ga Ibn Mas’ud, amma bai inganta ba zuwa ga Annabi. Haka kuma addu’a ta biyu ta inganta daga Ibn Abbas (Radiyallahu Anhu).
    Addu’o’i ne kyawawa da mutum zai iya yi duk lokacin da ya ji tsoron zaluncin wani azzalumin shugaba. A wurin da babu komai sai a faɗi sunan shugaban.

    Fassara

    Fassarar addu’a ta farko:

    Ya Allah Ubangijin sammai bakwai, Ubangijin Al’arshi; mai girma ka kare ni daga sharrin wane ɗan wane da dukkan mabiyansa daga halittunka aljanu da mutane; kada ka ba wa ɗaya daga cikinsu dama ya afka min ko ya yi min ta’addanci; kariyarka ta buwaya, yabonka ya girmama. Babu wanda ya cancanta a bautawa sai kai.

    Ita kuwa addu’a ta biyu ga fassararta:

    Allah shi ne mafi girma, Allah shi ne mafi buwaya daga halittunsa gaba ɗaya. Allah shi ne mafi buwaya daga abin da nake tsoro da fargaba. Ina neman tsari da Allah wanda babu wanda ya cancanta a bauta wa sai shi; wanda yake riƙe da sammai kada su faɗo kan ƙasa sai da izininsa. Ka kare ni daga sharrin bawanka wane da jami’an tsaronsa da mabiyansa da ma magoya bayansa mutane da aljanu.
    Ya Allah ka kasance mai kariya a gare ni daga sharrinsu, yabonka ya girmama, wanda ka baiwa kariya ya buwaya, sunanka ya yi albarka babu wanda ya cancanta a bautawa sai kai.

    Domin karanta cikakken bayani akan Sahabban Da Suka Fi Kowa Rawaito Hadisai danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Hadisi Na Ɗaya A Kan Haramcin Goyon Bayan Azzaluman Shugabanni danna nan.

  • Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya Yi Bayan Ya Tafi Sujudah

    Abin Da Ya Kamata Mai Yin Sallah Ya Yi Bayan Ya Tafi Sujudah

    Idan zai yi sujudah, ya tabbatar ya yi ne a kan gaɓoɓinsa guda 7.

    1-2 tafukan hannuwansa biyu, idan yana da su.
    3-4 guiwowin ƙafafunsa biyu, idan yana da su.
    5-6 wasu daga cikin yatsun digadigan ƙafafunsa biyu.
    7-tun daga goshinsa har zuwa hancinsa gaɓa ce guda ɗaya.

    Ba aso ya ware yatsun tafikan hannayensa ldan ya yi sujudah; kuma kar ya ajiye tsintsiyar hannuwansa biyu a ƙasa; kar ya boƙalo hannuwansa, kuma kar ya choge su a jikin haƙarƙarinsa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Surah A cikin Sallah danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Sallar Kisfewar Rana Da Wata (Zazzaɓin Rana Da Wata) danna nan.

  • Yadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita

    Yadda Ake Warkar Da Kambun Baka Ko Maita

    Yayin da aka tabbatar da mayu sun kama mutum; ko kuma kambun baka ne ya kama mutum; akan umarce shi da ya yi wanka; sannan ya yi alwala sai ya karanta waɗannan ayoyin kamar haka;

    • Fatihatul kitab
    • Ayatul kursiyyu
    • Ƙarshen suratul ? Baƙarah wato Amanar rasul
    • Suratun Nas
    • Suratul Falaƙ
    • Sannan ya tofa a cikin ruwa ya sha sai kuma ya tofa a hannunsa ya shafe jikinsa. Sannan zai iya karanta su a cikin man zaitun sai ya rinƙa shafawa. Da yardar Allah nan take zai samu lafiya.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Addu’ar Kariya Daga Sharrin Maƙiya danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Farin Jini Da Kwar Jini A wajen Al’umma danna nan 

    Edita; Rumasa’u Muhammada Kallamu

  • Guraren Da Aljanu Sukafi Zama

    Guraren Da Aljanu Sukafi Zama

    A wajen zama mun bambanta, sai dai da yawan mu muna rushe musu wurin zamansu sannan mu gina namu, kuma muna sare musu wajen zamansu mu dasa namu.

    Aljanu sun fi zama a cikin daji, saman dutse, saman ɗaki, cikin bola, cikin garken raƙuma, jikin shuri da dai sauransu. Da yawa akwai hatsari da mutum ya ga an share fili a daji ya tsugunna ya yi fitsari ko kashi.

    Akasarin irin wajejen nan aljanu ne suka yi jinya suka warke suka tashi a wajen don haka sai a kiyaye. Akwai waɗanda suke mu’amalantar mu a cikin gida, waɗanda su suke zama a cikin gida kamar yadda muke zama, haka kuma wasu daga cikinsu a hanya muke gamuwa da su, su rako mu har gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu addu’ar da za mu yi in za mu shiga gida da in za mu fita. Ya kamata in za ka bar gida sai ka ce;

    “Bismillahi tawakkaltu alallahi wala haula wala ƙuwwata illa billah, allahumma inni a’uzhu bika an adilla aw udilla, aw azilla aw uzalla, au azlima aw uzlama, aw ajhala aw yujhala alayya”

    Sannan in za ka shiga gida sai ka ce;

    “Bismillahi walajna, wa bismillahi kharajna wa’alal lahi rabbana tawakkalna”

    Amfanin addu’ar nan shi ne ko da aljanu sun biyo ka gida idan ka karanata wannan addu’ar za su ga babu ƙofa a gidanka, ba wurin zama sai su koma. Idan kuma ka yi sakaci wurin karanta ta, to za ka ga ka shiga gida cikin damuwa, da ƙunan rai da tashin hankali da jin haushin mutanen gidan.

    Daga lokacin shi kenan sun sami abinda suke so, ka yi ta faɗa da mutanen gida. Shi yasa musulunci ya koyar da mu hatta abinci in za ka ci ka ce bismillah, Allah ba zai ba su ikon su sa hannu su ci ba. In kuma ka gama cin abincin sai ka karanta wannan addu’ar;

    “Allahumma barik lana fi hi wa ta’amna khairan minhu”

    Idan ka yi wannan addu’ar Allah zai ba ka lada sannan kuma ya sa wa abincin da za ka ci albarka.

    Hatta kaya idan za ka cire, musulunci ya koyar da mu addu’a da ya kamata ka yi don ka samu kariya daga sharrin aljanu da sheɗanu. Don haka in za ka cire kayanka ka ce “bismillah” Allah zai rufe idanun aljanu ba za su ga tsiraicinka ba.

    Haka ɗakin da ya dade a rufe hatsari ne a shiga ba tare da an yi addu’a ba. Ko da shimfiɗa ce aka gyara ta domin a kwanta, musulunci ya koyar da mu ka karkadɗeta sau uku sannan ka yi addu’a ka kwanta. Kuma mu kiyaye zama a kofar ɗaki don wannan ma wurin zamansu ne.

    Sai a kiyayi zubar da ruwan zafi a makwarara, saboda nan ma wajen zamansu ne. Kuma a kiyayi zama a cikin ɗaki mai duhu da kuma yin surutu a bayi da zama kai ba ɗankwali da jiki a bude. Sai mu raba kanmu da yawan kalle-kalle marasa amfani ko jin kade-kade.

    Sannan uwar gida ki tattare kayanki da zarar magariba ta doso kai, ki killace yaranki, ki hana su zama ba riga, sannan a rufe kwanukan da aka ci abinci har dai za a bar su a waje. Wannan duk musulunci ya koyar da mu ne don kulawa da kanmu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Kalolin Aljanu Suke danna koren rubutun nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Kowane Irin Ciwo danna koren rubutun nan.

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Hanyar Ƙona Aljani A Jikin Mutum

    Hanyar Ƙona Aljani A Jikin Mutum

    Akan samu aljanu sun yi taurin kai a jikin mutum a yi ta yi su fita su ƙi ko kuma in sun fita su dawo. Ga wani mataki shi ma da za a ɗaukar musu.

    Ana samun ganyen auduga a sami ruwa mai kyau a zuba ganyen a ciki, sannan a karanta surorin nan kamar haka; 

    Suratul Fatiha
    Suratul Baƙarah gaba ɗayanta
    Suratul Saffat ayata 1-10
    Suratul yasin
    Suratul jinn
    Suratul kafirun
    Suratul ikhlas
    Suratul falaƙ
    Suratul nas

    Za a karanta a tofa a cikin ruwa a rinƙa ba wa mara lafiya tana sha sau biyu a rana, da safe bayan ta ci abinci da kuma dare kafin ta kwanta bacci. Sannan a cire ganyen audugan a ƙona su ta rinƙa turare da su a jikinta. Za ta rabu da shi In Sha Allah. Sannan a rinƙa sa wa mara lafiya ƙira’ar Suratul Baƙarah da Al-Imran da yasin tana saurara kodayaushe.

    Ana so idan mutum ya yi sallah sai ya karanta ta, tare da istigfari mai yawa da faɗin la’ilaha illallahul malikul haƙƙul mubin. A ƙalla ya karanta ƙafa ɗari idan bashin ya tsananta. To ubangiji Allah zai hore masa abunda zai biya bashin sannan ya kau da masa duk wata damuwa kuma ya wadata shi.

    Domin karanta cikakken bayani akan Shin Menene Sihiri danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mummunan Ƙarshe Da Kyakkyawan Ƙarshe. danna nan

  • Yadda Kalolin Aljanu Suke

    Yadda Kalolin Aljanu Suke

    Aljanu kala-kala ne kamar yadda muke nau’in mu kala-kala:

    Ga kalolin Aljanu kamar haka:

    • Jinnul gawas
    • Jinnul ɗayyar
    • Jinnul bait
    • Jinnul jalab wal tahdir
    • Jinnul majus
    • Jinnul yahudi
    • Jinnul nasari
    • Jinnul muslim
    • Jinnul ashiƙ
    • Jinnul kamil
    • Jinnul tabdil
    • Ifritu minal jinn

    Waɗannan su ne kaɗan daga cikin kalolin aljanu, kuma kowanne aljani akwai alamominsa sannan akwai irin nau’in magungunansa. Akwai jinnu da yake kama da mutane sannan akwai jinnu da ake tura shi ya shiga mutum.

    Domin karanta cikakken bayani akan Yadda Alamomin Jinnu Yake danna koren rubutu.

    Domin karanta cikakken bayani akan Mutane Biyar Da Suka Yi kama Da Manzon Allah (S.A.W)

  • Yadda Nau’ikan Aljanu Suke

    Yadda Nau’ikan Aljanu Suke

    Kamar yadda muke da mata da maza, haka ma aljanu suke da mata da maza, yara da manya, tsoho da tsohuwa, sarakuna da talakawa, masu arziki da kuma matsiyata kuma musulmai da kafirai.

    Kamar yadda Allah (Subahanahu Wata’ala) ya faɗa acikin Al Ƙur’ani mai girma a cikin suratul jin;

    “Wa’anna minnas salihuna waminna du na zalika kunna ɗara’iƙa ƙidada”

    Domin karanta cikakken bayani akan Guraren Da Aljanu Sukafi Zama danna nan.

    Domin karanta bayani akan Addu’ar Da Ba ta Dawowa In An Yi Ta danna nan

  • Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka

    Yadda Ake Addu’ar Samun Lafiya Ga Cututtuka

    Addu’ar Samun Lafiya – An ruwaito daga A’isha (Radiyallahu Anhu), ta ce; Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya kasance idan mara lafiya ya zo wurinsa da koke na rashin lafiya; yakan ɗauko hannunsa na tsakiya ya sanya a bakinsa.

    Sannan ya dangwali ƙasa, sannan ya ɗaura a inda kewa mutumin ciwo, sai ya karanta wannan addu’ar samun lafiya; kamar haka:

    “Bismillahir turbati ardina biriqati ba’dina yashfa taqmuna bi’izni rabbina”

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga Littafin Da Haka Na Gagara wanda Yahaya Ishaq ya wallafa shi domin karanta cikakken Littafin danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya danna nan