Tag: addu;a

  • Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya

    Yadda Ake Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali Da Wadatar Zuciya

    Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali – An ruwaito daga Shaddad Ibn Aws, Annabi (Sallallaahu Alaihi Wasallam) ya ce; “Ya Shaddad, idan ka ga mutane suna tara azurfa, zinare ko kuma yaƙutu, to suna tarawa ne don kada su yi talauci “.

    Sai ya ce; “Kai Shaddad, ka da ka tara komai, ka riƙe wannan addu’ar kawai, Allah (Subahanahu Wataa’ala) zai tsare mutuncinka ya rufa maka asiri, ka fi ƙarfin abin da za ka ci, kuma ka zauna lafiya, ni ma a duk lokacin da na yi sallah ina karanta wannan addu’ar;

    “Allahumma inni as’alukath Sabbath fil amr, wal azimatu alar rushdi, wa as’aluka shukra ni’matika wa husna ibdatika, wa as’aluka ƙalban saliman wa lisaanan sadiƙan, wa as’aluka min khairi ma ta’alam, wa a’uzubika min sharri ma ta’lam, wa astgfruka lima ta’lam innaka anta allumul gayub”.

    Wannan Addu’ar Samun Nutsuwa Da Kwanciyar Hankali; an samo ta ne daga WABILUS SAYYIBU MIN KALAMUD DAYYIB.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira danna nan

  • Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira

    Kalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira

    Wannan addu’ar; ana so a dunga karanta ta a duk lokacin da mutum ya tashi daga barci, da kuma lokacin da zai kwanta barci. Insha Allah, Allah zai tsare shi Duniya da Lahira.

    Idan ka karanta, Allah (Subahanahu Wata’ala) ba zai ba da dama wani ɗan Adam ya yi nasara a kanka ba; zai tsare ka daga sharrin dukkan maƙiya da mahassada; Duniya Da Lahira. Sannan Allah (Subahanahu Wata’ala) zai sa ka yi kyakkyawan ƙarshe a rayuwarka.

    Ga Addu’ar Kamar Haka;

    Na Duniya

    1. Hasbiyallahu lidini
    2. Hasbiyallahu liman ahammani
    3. Hasbiyallahu liman baga alayya
    4. Hasbiyallahu liman hasadani
    5. Hasbiyallahu liman kadaniy bisu’in.

    Na Lahira

    1. Hasbiyallahu indal mawt
    2. Hasbiyallahu indal mas’alatu fil ƙabar
    3. Hasbiyallahu indal mizan
    4. Hasbiyallahu indas siraɗi
    5. Hasbiyallahu la’ilaha illallahu alaihi tawakkaltu wa’ilahi unib.

    Wannan addu’ar an samo tane daga cikin littafin MAƘALIDUS SAMAWATI WAL ARDI MA’A HUSNUL MU’MIN.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa danna nan

  • Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa

    Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa

    Wannan addu’a ita ake kira “gaya wa jini na wuce”; domin biyan buƙata, Wato duk wata buƙata da kake nema wajen Allah (Subahanahu Wata’ala); ko kuma kake son Allah ya biya maka buƙatunka cikin gaggawa; sai ka dage ka ɗauki wannan addu’ar.

    Domin samun biyan buƙata, Za ka tashi cikin dare ka inganta alwalarka sannan ka yi nafila raka’ah biyu 2 ko huɗu 4 ko shida 6 ko takwas 8, sannan ka yi istigfari da salatin Annabi da hailala duk adadin da ya sawwaƙa, sai ka yi sujjada sannan ka karanta; 

    La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin” – (71)

    A cikin sujjada sai ka gaya wa Allah damuwarka sannnan sai ka ɗago ka zauna, sai ka sake istigfari da salatin Annabi da hailala, sai kuma ka karanta suratul Hadid; aya ta ashirin da ɗaya zuwa ta ashirin da huɗu (21-24). Sannan ka karanta wannan addu’ar kamar haka:

    Allahumma inni as’aluka bi’ismukal makhzun walmaknun, addahirul muƙaddis; Alhayyul Ƙayyum, Ar-rahmanur Rahim Zil Jalalu Wal Ikram, An Tusalliya Ala Sayyidin Muhammadin (Sallallahu Alaihi Wasallam); wa’an taf’al bi kasha wa kasha (inda zaka faɗi dukkan buƙatunka), birahmatika ya arhamur rahimin”.

    Wannan addu’ar an samo ta ne a cikin littafin MIFTAHUL KHAIR shafi na ashirin (20).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Shiriyar Ubangiji danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Shiriyar Ubangiji

    Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Shiriyar Ubangiji

    Shiriyar Ubangiji – Ga wanda yake son Allah (Subahanahu Wata’ala) ya shirya masa yaransa su kintsu, su shiryu, su zama suna kiyaye umarnin ubangiji da kuma sharuɗan da ya gindaya musu.

    Sai ka lazumci karanta musu wannan addu’ar a duk lokacin da ka gabatar da aikin alkhairi: azumi ne ko sallah ko kuma wani aikin alkhairi, sai kasanya su ciki, ka yi wannan addu’ar kamar haka;

    “Allahumma baarik lifi awlaadi warzuƙnibirrahun, allahumma ya mu’alimu Musa allimhum, waya mufahhima Suleimana fahhamhum; waya mu’ti Lukmanal hikimata aatihimul hikmah wa fasla kidab; Allahumma allimhum hikmah wa faslal kidab, allahumma allimhu ma jahilu; wazakkirhun manasu, waftah alaihim min barakatis samawati wal ardi; innaka sami’ul mujib. Allahumma inni as’aluka lahumut tawfiƙ, waƙuwwatul hifzi, wasur’atul faham; wasifa’an nahan, allahummaj’al huddatan muhtadin, la dhalina wala mudhallin; allahumma habbib ilaihimul imana wazayyanahu fi qulubihim akarrahu ilihimul kufra wal fasuwa wal isyaan; waja al hum minar rashidina”.

    Idan har ka karanta wannan addu’ar, da yardar Allah; ‘ya’yanka za su samu shiriyar Ubangiji.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba su Da Abokanan Banza danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza

    Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Samun Karatu Da Raba Su Da Abokanan Banza

    Wannan ita ma addu’a ce da ake karantawa domin nema wa yara shiriyar Ubangiji da samun karatu. Duk mai son Allah ya kintsa masa yara su shiryu, su zama abin koyi a wajen al’umma.

    To sai ya dinga lazumtar karanta musu wannan addu’ar a duk lokutan da ya yi aikin alkhairi; ko kuma bayan sallar asuba, sai ka karanta wannan addu’a ta Nema Wa Yara Samun Karatu Da Rabasu Da Abokanan Banza.

    Ga addu’ar kamar haka:

    Allahumma ahsin ƙulubu awladina wa akhlawahum, wa amla ƙulubahum nuran wa hikmah, allahumma dahhir ƙulubahum minar riya, allahumma hafiz farujahum minaz zina, walluwadi, wassihaƙi wa kullil jara’im. Allahummaj’alhum hafzatan likitabika, wasunnati mabiyyuka (Sallallahu Alaihi Wasallam). Allahummar zuƙ humul ƙana’ata, war ridha. Allahummar zuƙ hubbuka wa hubbub nabiyyuka (Sallallahu Alaihi Wasallam), wa hubbub kullu man yuhibbuka, allahummaftah alaihim abwaba rizƙukal halalu miin wasi’u fadlika wakfihim bihaluka an haramika wa agnihim bifadlika. Allahumma jannibhum rufaƙa’is su’i wal fawaahisha ma zahara minhu wama badan. Allahumma aafihim fi abdanihim wa asma’ihim, wa anfusihim, wa absarihim, wa jawarihim ya arhamur rahimina”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim

    Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim

    Ismullahil A’azim – Ana so a karata wannan addu’ar a duk lokacin da mutum ya samu kansa cikin tsanani ko kuma damuwa.

    An samu wani sahabi a zamanin Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam); ɗan kasuwa, wanda yana cikin tafiya daga Madina zuwa Makkah, domin kasuwanci sai ya gamu da wani ɗan fashi, inda ya kama shi zai halaka shi; sai ya nemi izinin da ya bar shi ya yi alwala ya yi sallah raka’ah biyu, sannan duk abin da zai masa ya yi masa.

    Sai ya ba shi dama, sai ya tashi ya yi alwala ya yi nafila raka’ah biyu (2); a sujjadar ƙarshe sai ya karanta wannan addu’a ta Ismullahil A’azim

    Ga addu’ar kamar haka:

    Bismillahir Rahmanir Rahim; Allahumma inni as’aluka bil’izzati lati la taraam, wal mulkul lazhi la yadam, wal aynul lati la tanaam, wan nurul ladhi la yadfa’a, wabil wajhil lazhi la yubla, wabiddaymumatil lti la tafna, wabil hayatul lati la tamut, wabis samdiyyatul lati la taƙhar, wabirrububiyyatul lati la tastazil an taj’al lana min umurina farjan wa makhrijan hatta la narju gairuka ya arhamur rahimin”.

    Bayan da ya karanta wannan addu’a; ko da ya ɗago sama sai ya ga wata halitta a saman doki tana gudu ɗauke da takobi a buɗe ya zo ya sare kan wannan ɗan fashin. Bayan haka, sai ya tambaye shi; “Wane ne kai ka kawo mini ɗauki daga inda ban yi tsammani ba?”

    Sai yace da shi, “Ka kira Allah (Subahanahu Wata’ala) da sunaye cikin sunayensa zaɓaɓɓu; wanda ba wata buƙata da za ka roƙi Allah (Subahanahu Wata’ala) bai biya maka ba; don haka Ubangiji ya umarce ni da na kawo maka ɗauki”.

    Saboda haka; duk halin da mutum yake ciki in har ya roƙi Allah (Subahanahu Wata’ala) da sunayen nan; Allah (Subahanahu Wata’ala) zai taimaka masa.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba danna nan.

  • Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba

    Yadda Ake Addu’a Ga Cututtuka Ko Kuma Wata Annoba

    Addu’a Ga Cututtuka; Wannan kuma addu’a ce da aka ce a dunga karanta ta a duk lokacin da wata annoba ta shigo.

    Idan har kana karanta wannan addu’ar, Allah zai tsare shi daga ciwon annoba na zamani, wanda aka sani da wanda ba a sani ba. Duk sanda mutum ya yi sallah ko wani aikin alkhairi, ya dunga karanta wannan addu’a (Addu’a Ga Cututtuka) kamar haka, Allah (Subahanahu Wata’ala) zai kare shi;

    Allahumma inni a’uzhubika minal barasi, wal jununi, wal juzami, wamin sayy’il asqam”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Nauye-nauyen Rayuwar Aure danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya danna nan.

  • Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya

    Yadda Ake Addu’ar Bushewar Zuciya

    Addu’ar Bushewar Zuciya – Wannan addu’ar ma akan karanta ta domin Ubangiji ya ba ka kariya daga dukkan cututtukan zamani da kuma bushewar zuciya.

    Muddin za ka yi wannan addu’ar Bushewar Zuciya; Allah (Subahanahu Wata’ala) ba zai bari ka shiga cikin wani hali na ƙunci a cikin rayuwarka ba, kuma zai tsare ka daga dukkan cututtuka na zamani wanda aka sani da kuma wanda ba a sani ba.

    Ga addu’ar kamar haka:

    Allahumma inni a’uzhubika minal ajzi, wal kasali wal jubni, wal bukhli, wal harami; wal gaflati, wal qaswati, wal ilati, waz zillati, wal maskanati; wa a’uzhubika minal faqari, wal kufri; wal fusuqa, wash shiqaq, wan nifaq, was sum’ati, war riya’a, wa a’uzhubika minas sumami; wal bukami, wal jununi, wal jazami, wal barasi wa sayyi’il asqaam”.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Aure danna koren rubutu.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Za ki San Kanki Kafin Ki yi Aure danna koren rubutu.

  • Addu’a Ga Yaran Da Ba Sa Ji

    Addu’a Ga Yaran Da Ba Sa Ji

    Yaron da ake gani ya ɗauko hanyar lalacewa ba ya jin magana; ba a sa shi ya yi kuma ba a sa shi ya bari, to ga wata tajriba da ya kamata uwa ta yi wa yaranta.

    Ranar Juma’a rana ce mai tsada. Shi ne lokacin sallar la’asar, duk addu’ar da kika yi a lokacin tana da tasiri ga wanda aka yi wa. A wata ruyuwar ma an ce Annabi Yaƙuba (Alaihis Salam) ya yi wa ‘ya’yansa addu’ar neman gafarar kuskuren da suka aikatawa ɗan uwansu Yusuf bayan Allah ya bayyanar da shi, don haka lokaci ne mai daraja.

    Ana son bayan kin yi sallar la’asar ki sami ruwan zamzam ko kuma na rijiya ko kuma wanda kika yi alwala kika rage.

    Bayan kin idar da sallarki cikin addu’arki sai ki karanta wannan addu’ar kamar haka;

    “Ya maliku yaumud din, iyyaka na’abudu wa iyyaka nasta’in, ihdina siraɗal mustaƙim, siraɗal ladhina an amta alaihim, gairil magdubi alaihim waladdaaliin”

    Sai ki roƙi Allah ya tsare miki yaranki ko yarinyarki tare da kiran sunanta ko sunanshi. Ki yi shi adadi mai yawa kya iya yin ɗari 100, kina karantawa kina tofawa cikin ruwan. In kin gama sai ki ƙara tahiya ita ma ƙafa ɗari 100 ki tofa cikin ruwan. Akan so kullum ki yi wannan har sai wata Juma’ar ta zagayo, kina yi kina tara ruwa. In kin gama sai ki rinƙa ba shi ruwan yana sha da safe kafin ya ci abinci haka da daddare kafin ya kwanta bacci. Inkuma ya yi kangarewar da ba zai sha ba, sai ki sarrafa masa a cikin abinci ya ci ya sha. Za ki ga mamaki yadda yaronki zai koma In Sha Allah.

    Domin karanta cikakken bayani akan Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye danna nan.

    Don karanta Hukunce-hukuncen Ƙananan Yara danna nan 

     

     

    Edita; Rumasa’u Muhammad Kallamu

  • Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Matakan Da Za A Bi Domin Hana Yara Shaye-shaye

    Akan kai wani mataki duk irin kulawar uwa ko kuma kulawar uba ya zamto yaransu ko yarinyarta ta fanɗare.

    Ka ga yaro ya jefa kansa cikin wannan hatsarin rayuwa, yaro ya rinƙa shaye-shaye sakamakon abokai da ya gamu da su.

    Ga matakan da ake bi In Sha Allah zai daina:

    1. Matakin farko raba shi da abokan hurɗarsa a sama masa wajen sana’a.

    2. Mataki na biyu shi ne ana ɗaukan ayoyin sakina na Al ƙur’ani gaba ɗaya da kuma ayatus Sam, a karanta su a tofa a ruwan sama ko na rijiya, sannan a samu za’afaran da ganyen magarya da muski ɗan kaɗan sai a ba shi ya rinƙa sha da safe da kuma dare.

    Sannan za a iya ɗaukan dukkan nau’in kayan mayen da yake sha a haɗa su guri guda; anemo garin kustul hindi cokali uku da kuma man zaitun da man habba da kuma man kwakwa da na tafarnuwa da na’a na’a a haɗa su guri guda da kayan shaye shaye sannan a rufe a bar su su kwana.

    In gari ya waye a girgizasu sosai, sai a tace sannan a ba shi kafin ya ci abinci. Ana so da ya sha ya yi amai. Wannan haɗin ana so a rinƙa ba shi duk bayan sati uku ko kuma wata ɗaya. Sannan a haɗa da wannan ruwan da aka yi tofin ayoyin a ciki. Insha Allah duk abinda yake sha zai fita daga ransa ya dawo cikakken mutum.

    Minhaj 274
    Ayatus Sakina: Minhaj 255

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Haddar Karatu danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Karatun Manzon Allah danna nan

    Edita@rumasau-kallamu