Tag: addu;a

  • Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke

    Yadda Falalar Karanta Ayatul Kursiyyi Ya Ke

    An karɓo daga Ubayyu ɗan ka’ab (Radiyallahu Anhu) ya ce: “Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) yace; “Ya baban Munzir, Shin kasan wacce aya ce mafi girma a cikin Al-ƙur’ani?

    Sai na ce: Allahu laa’ilaha illa huwal hayyul ƙayyum” yace: Sai ya bugi ƙirji na ya ce; ” Ina taya ka murnar ilimi, ya baban Munzir (Wato yana taya shi murnar sanin hakan).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Karanta Amanar Rasulu Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Buɗe Karatun Alƙur’ani Da Bismillah A Cikin Sallah danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya walfa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Yadda Falalar Karatun Al-Ƙur’ani Ya Ke

    Karatun ƙur’ani ibada ce babba wacce babu sama da ita; musamman in ta haɗu da ikhlasi da lura da ma’anoni da manufofin abinda ake karantawa (Tadabbur) da karantawa dai-dai da ƙa’idodin karatun (Tajwidi); da kuma abinda ya fi komai muhimmanci wato aiki da abinda ake karantawa.

    Hadisai da dama sun zo kan bayanin Falalar Karatun Al-Ƙur’ani a jumlace; da kuma falalar karanta waɗansu keɓaɓɓun surori da ayoyi.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Koyo Da Koyarwar Da Al-Ƙur’ani Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Zikiri danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    Yadda Ake Zikiri Yayin Fita Daga Gida

    “Bismillaahi Tawakkaltu alallaahi walaa haula walaa ƙuwwata illaa bil-laahi”.

    {Da sunan Allah (nake fita), na dogara ga Allah, kuma babu dabara, babu ƙarfi sai da Allah}.

    “Allahumma inni A’uzu bika an adhilla au udhilla, au azhilla au uzhalla, au azlima au uzlama au ajhala au yujhala alayya”.

    {Ya Allah! Ina neman tsarinka daga na ɓata ko a ɓatar da ni, ko na zame ko a zamar da ni, ko na yi zalunci ko a zalunce ni, ko na yi wauta ko a yi mini wauta}.

    Domin karanta cikakken bayani akan Zikiri Yayin Shiga Gida danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani akan Ladubban Addu’a A Musulunci danna nan.

    Wannan bayanin anciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Addu’ar Da Ake Yi Idan Za a Yanka Dabba Ko Soke Ta

    Addu’ar Da Ake Yi Idan Za a Yanka Dabba Ko Soke Ta

    Abin da ake faɗa idan za a yanka dabba, ko za a soke ta (Raƙumi)

    بشم الله واللهُ أَكْبَرُ اللَّهُمَّ مِنْكَ ولَكَ اللَّهُمَّ تَقَبَّلْ مِنِّي

    Bismillah wallahu Akhbar, Allahumma minka walaka, Allahumma taqabbal minnee.

    Da sunan ALLAH, Kuma ALLAH ne Mafi girma.Ya ALLAH wannan dabba daga gareka take, kuma mallakar ka ce.Ya ALLAH Ka karɓa daga gareni.

    Sannan anfiso mutum ya yanka abin layyarsa da kansa, idan kuma bazai iyaba saiya wakilta a yanka masa.

    Danna nan don karanta Addu’a Yayin Da Mutum Ya Juya A Cikin Bacci

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Yayin Da Mutum Ya Juya A Cikin Kwanciyar Bacci

    Addu’a Yayin Da Mutum Ya Juya A Cikin Kwanciyar Bacci

    لا إِلَهَ إِلَّا اللهُ الوَاحِدُ القَهَّارُ، رَبُّ السَّمَوَاتِ وَالْأَرْضِ وَمَا بَيْنَهُمَا ، العَزِيزُ الغَفَارُ

    La ilaha illal-lahul-wahidul-qahhar, rabbus- samawati wama baynahuma, al’azeezul- ghaffar”.

    Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, makaɗaici, mai rinjaye, ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu, mabuwayi, mai yawan gafara.

    Danna nan don karanta Abin Da Ake Faɗa Idan Aka Firgita

    Edita@rumasau-kallamu

  • Abin Da Ake Faɗa Idan Aka Firgita

    Abin Da Ake Faɗa Idan Aka Firgita

    لاَ إلَهَ إلا الله

    La ilaha illal-lah

    Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.

    Don karanta Addu’ar Da Ake Faɗa Don Kawar Da Kaidin Shaiɗanu Masu Taurin Kai danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Da Ake Faɗa Don Kawar Da Kaidin Shaiɗanu Masu Taurin Kai

    Addu’ar Da Ake Faɗa Don Kawar Da Kaidin Shaiɗanu Masu Taurin Kai

    أَعُوذُ بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّاتِ الَّتِي لا يُجَاوِزُهُنَّ بَةٌ ولا فَاجِرٌ مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ، وبَرَأَ وذَرَأَ ومِنْ شَرِّ مَا يَنْزِلُ مِنَ السَّمَاءِ ومِنْ شَرِّ مَا يَعْرُجُ فيهَا ، ومِن شَرِّ مَا ذَرَأَ فِي الْأَرْضِ وَمِنْ شَرِّ مَا يَخْرُجُ مِنْهَا ، ومنْ شَرّ فِتَنِ اللَّيْلِ والنَّهارِ، ومِنْ شَرِّ كُلِّ طارِقٍ إِلَّا طَارِقاً يَطْرُقُ بِخَيْرٍ يَا رَحْمَن.

    A’oozu bikalimatil-lahit-tammat, allatee la yujawizuhunna barrun wala fajir min sharri ma khalaq, wabara’a wazara’a, wa min sharri ma yanzilu minas- sama’, wamin sharri ma ya’aruju feeha, wa min sharri ma zara’a fil-ard, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min sharri fitnanil-layli wannahar, wa min sharri kulli tarikin illa tarikan yatruku bikhayrin ya Rahman.

    Ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku, waɗanda wani (bawa) nagari ko fajiri ba ya ƙetare su, daga sharrin abin da (Allah) Ya halitta, Ya samar da shi daga babu, Ya fari halittarsa, daga kuma sharrin abin da yake saukowa daga sama, da sharrin abin da yake hawa cikinta, da sharrin abin da Ya halitta a cikin ƙasa, da sharrin abin da yake fitowa daga gare ta, da sharrin fitinun dare da na rana, da kuma sharrin duk wani mai zuwa cikin dare, sai dai mai zuwa da alheri, ya (Allah) mai yawan rahama!

    Danna nan don karanta Addu’ar Buɗe Sallah

    Edita@rumasau-kallamu

  • Nafilolin Aikin Hajji

    Nafilolin Aikin Hajji

    Kamar yadda aka sani, aikin Hajji rukuni ne na musulunci ga wanda ya ke da iko.

    Malamai sun yi saɓani dangane da matsayin Umara shin farilla ce ko nafila? Malaman Mazahabar Hanafiyya da Malikiyya suna ganin Umara ba wajibi ce; yayin da Malaman Mazahabobin Shafi’iyya da Hambaliyya da zahiriyya suna ganin Umara wajibi ce kamar aikin Hajji. Kowane ɓangare suna da hujjojinsu da suka dogara da su a ayoyin Ƙur’ani da hadisai; waɗanda suna nan cikin littattafan fiƙhu1.

    Manzon Allah (Sallallahu alaihi wasalam) ya ce; “Ku jeranta hajji da Umara saboda jeranta su yana kore zunubai da talauci kamar yadda ƙira yake kawar da tsatsar ƙarfe.” (Tirmizi 738, Nasa’I 2585).

    Wannan hadisin yana nuna cewa yin Umara bayan aikin hajji a kai-a kai yana maganin talauci, yana kankare zunubai.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Falalar Yin Umra A Watan Ramadan danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Ismullahil A’azim danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Yadda Falalar Zikiri Ya Ke

    Yadda Falalar Zikiri Ya Ke

    Zikiri shi ne ambaton Allah Ta’ala da kalmomin yabo da kirari da girmamawa da godiya; bisa ni’imominsa tare da nutsuwa da ƙasƙantar da kai da nuna gajiyawa; da ƙwadayin rahamarsa da neman tsari daga azabarsa.

    Zikiri kalma ce mai faɗi wacce ta ƙunshi ambaton Allah da harshe da biyayya a gare shi da gaɓoɓi; da kuma sanya Allah Ta’ala a cikin zuciya ta hanyar tunani kan ni’imominsa da falalarsa ga bayinsa da ƙoƙararin fahimtar hukunce- hukuncen addininsa da ma’anonin littafinsa.

    A kan haka za mu fahimci zikiri yana da nau’o’i daban-daban wanda ya ƙunshi karatun alƙur’ani, ibadu; zikiran safe da yamma, zikiran lokuta da halaye daban-daban, karatun ilimin addinin musulunci; da kuma dukkanin wani nau’i na zikiran harshe kamar hailala, salati ga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasalam) Istigfari, Tasbihi, lahaula wala kuwwata illa billahi da sauransu.

    Zikiri yana da falala mai ɗimbin yawa, ga kaɗan daga cikin irin waɗannan falala da darajoji:

    1- Allah Ta’ala yana yabon masu zikiri a cikn mala’iku.

    2- Allah Ta’ala Mala’ikunsa suna yin salati ga masu yin zikiri.

    3- Allah yana gafarta zunuban masu zikiri

    4- Mai yawan zikiri yana samun taimakon Allah.

    5- Zikiri yana sanya nutsuwa da sanyin rai ga mai yinsa.

    6- Zikiri yana raya zukata.

    7- zikiri yana sanya mutum ya samu kariya da ga wasiwasin shaiɗanu.

    8- Zikiri yana sanya a samu alkhairin duniya da lahira.

    9- A cikin kowacce ibada akwai zikiri.

    10- Allah yana sanya kwarjini da farin jini ga mai zikiri.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikiri Bayan Sallar Asuba Har Zuwa Ɓullowar Rana Ya Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Zikirin Tashi Daga Majalisa Yake danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; Wanda Usman Abubakar (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

  • Falalar Suratul Tabarakallazi Biyadihil Mulku

    Falalar Suratul Tabarakallazi Biyadihil Mulku

    An karɓo daga Abu Huraira (Radiyallahu Anhu) daga Annabi (Sallallahu Alaihi Wasalam) ya ce: haƙiƙa wata sura a cikin Alƙur’ani mai ayoyin talatatin ta ceci wani mutum har sai da aka gafarta masa, ita ce:-

    “Tabarakallazi biyadihi mulku” (Abu Dawud, Tirmizi, Nisa’I Ibn Majah, Sahihul Jami’i 2091).

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Ta Ke danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Ma’anar Sallar Tuba Da Falalarta danna nan.

    Wannan bayani an ciro shi ne daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu; wanda (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.