Tag: addu;a

  • Addu’ar Wanda Ya Ji Tsoron Zaluncin Wani Mai Iko

    Addu’ar Wanda Ya Ji Tsoron Zaluncin Wani Mai Iko

    اللهُمَّ رَبَّ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ ، وَرَبَّ الْعَرْشِ الْعَظِيمِ، كُنْ لِي جَاراً مِنْ (فُلَانِ بنِ فُلان) وَأَحْزَابِهِ مِنْ خَلَائِقِكَ ، أَنْ يَفْرُطَ عَلَيَّ أَحَدٌ مِنْهُمْ أَوْ يَطْغَى عَرَّ جَارُكوَجَلَّ ثَنَاؤُكَ ، وَلَا إِلَهَ إِلاأنت

    Allahumma rabbas samawatis sab’i wa rabbal arshil azeem, kun lee jaran min (fulan bin fulan) wa’ahzabihi min khala’iƙika, an yafruda alayya ahadun minhum au yadga, azza jaruka, wajalla sana’uka, wala’ila ha illa anta

    Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai, kuma Ubangijin Al’arshi mai girma, Ka kasance Mai tsari gare ni daga (wane ɗan wane), da dukkan rundunarsa daga cikin halittunka kar wani daga cikinsu ya yi gaggawar azaba a gare ni, ko ya ƙetare haddi. Kariyarka ta buwaya, kuma Yabonka ya girma, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai.

    اللَّهُ أَكْبَرُ، الله أعَزُّ مِنْ خَلْقِهِ جَمِيعاً ، اللهُ أَعَزُّ
    مِمَّا أَخَافُ وَأَحْذَرُ ، أَعُوذُ بِاللهِ الذي لا إلَهَ إلاّ هُوَ ، الْمُمْسِكِ السَّمَاوَاتِ السَّبْعِ أَنْ يَقَعْنَ عَلَى الأَرْضِ إِلا بِإِذْنِهِ ، مِنْ شَرِّ عَبْدِكَ (فَلان ، )وَجُنُودِهوَأَتْبَاعِهِ وَأَشْيَاعِهِ مِنَ الْجِنِّ وَالإِنسِ. اللهُمَّ كُنْلِي جَاراً مِنْ شَرِّهِمْ ، جَلَّ ثَنَاؤُكَ وَعَزَّ حَاَرُكَوَتَبَارَكَ اسْمُكَ ، وَلاَ إِلَهَ غَيْرُكَ (ثلاث مرات)

    Allahu akbar Allahu a’azzu min khalƙihi jami’an,Allahu a’azzu mimma akhafu wa ahzar, a’uzu billahil lazee la’ilaha illahu, almumsikis samawatis sab’i an yaƙa’ana alal ardi illa bi’iznih min sharri abdika (fulan)wajunudihi wa’atba’ihi wa’ashya’ihi minal jinni wal’ins. Allahumma kun lee jaran min sharrihim, jalla sana’uka wa’azza jaruka, watabarakas muka, wala’ilaha gairuka.(salasa marraat)

    Allah Shi ne Mafi girma. Allah Shi ne Mafi buwaya daga dukkanin halittarsa. Allah Shi ne Mafi buwaya daga abin da nake jin tsoronsa kuma nake shayinsa. Ina neman tsarin Allah, Wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, Mai rike sammai daga su ruguzo a kan kasa sai da Izininsa, daga sharrin bawanka wane (ya ambaci sunansa), da rundunarsa, da mabiyansa, da kungiyoyinsa na aljanu da mutane.

    Ya Allah! Ka zamo Mai tsari gare ni daga sharrinsu. Yabonka ya girma, kuma Kariyarka ta buwaya, kuma alherin Sunanka ya yawaita, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba. (Sau uku)

    Domin karanta Yadda Falalar Suratul Ƙulhuwallahu Ahad Take danna nan 

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Maganin Damuwa Da Baƙin Ciki

    Addu’ar Maganin Damuwa Da Baƙin Ciki

    اللّهُمَّ إِنِّي عَبْدُكَ ابْنُ عَبْدِكَ ابْنُ أَمَتِكَ، نَاصِيَتِيبيَدِكَ ، مَاضٍ فِيَّ حُكْمُكَ، عَدْلٌ فِيَّ قَضَاءُكَ أسْأَلُكَ بِكُلِّ اسْمٍ هُوَ لَكَ سَمَّيْتَ بِهِ نَفْسَكَ أَوأَنْزَلْتَهُ فِي كِتَابِكَ ، أَوْ عَلَّمْتَهُ أَحَداً مِنْ خَلْقِكَ أَوْ اسْتَأْثَرْتَ بِهِ فِي عِلْمِ الْغَيْبِ عِنْدَكَ أَنْ تَجْعَلَ
    الْقُرْآنَ رَبيعَ قَلْبِي ، وَنُورَ صَدْرِي ، وَحَلاءَحُزْنِي وَذَهَابَ هَمِّيَْ

    Allahumma inni abduka inbnu abdika ibnu amatika,nasiyatee biyadika,madin fiyya hukmuka, adlun fiyya ƙada’uka, as’aluka bi kulli ismin huwa laka sammaita bihi nafsaka au anzaltahu fee khitabika, au allamtahu ahadan min khal’ƙika awistaasarta bihi fee ilmil gaibi indaka an taj’alal ƙur’ana rabee’a ƙalbee,wa nura sadree wajala’a huznee wazahaba hammee.

    Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Makwarkwaɗata a Hannunka take, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma ƙaddararka gare ni mai adalci ce. Ina roƙon Ka da kowane Suna naka, Wanda Ka ambaci Kanka da Shi, ko Ka saukar da Shi a cikin Littafinka, ko Ka sanar da Shi ga wani daga cikin halittarka, ko Ka keɓance Kanka da saninsa a cikin ilimin da ke da ke wurin Ka, da Ka sanya Alkur’ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske ga ƙirjina, da kwaranyewa ga baƙin cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata.

    اللّهُم إنِّي أَعُوْذُ بِكَ مِنَ الْهَمِّ وَالْحُزْن، وَالْعَجْز وَالْكَسَلِ وَالْبَحْلِ وَالْجُبْنِ ، وَضَلْعِ الدَّيْنِ وَغَلَبَةِالرِّجَال

    Allahumma inni a’uzu bika minal hammi walhuzin, wal’ajzi walkasal walbukli waljubni, wadal’il deeni wagalabatir rijaal.

    Ya Allah! Ina neman tsarinka daga damuwa, da baƙin ciki, da gajiyawa, da lalaci, da rowa, da ragwantaka, da nauyin bashi, da rinjayen mazaje.

    Karanta Addu’ar Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    Edita@rumasau-kallamu

     

  • Zikiri Yayin Shiga Gida

    Zikiri Yayin Shiga Gida

    “Bismillaahi walajnaa, wa Bismillaahi kharajnaa, wa alal-laahi Rabbanaa tawakkalnaa”.

    {Da sunan Allah muka shiga, kuma da sunansa muka fita, kuma ga Allah kaɗai, Ubangijinmu, muka dogara}.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Tafiya Zuwa Masallaci danna nan.

    Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Tafiya Sujudah danna nan.

    Wannan bayanin an ciro shi ne daga littafin Garkuwar Musulmi Ta Addu’o’i Daga Alƙur’ani Da Sunna; wanda Sheikh Sa’id Ibn Ali Ibn Wahf Al-Kahdani ya wallafa shi; Domin karanta cikakken littafin danna nan.

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    Addu’ar Shiga Wata Karkara Ko Wani Gari

    اللهم رَبَّ السَّمَوَاتِ السَّبْع وَمَا أَظْلَلْنَ، وَرَب
    الأَرَضِينَ السَّبْعِ وَمَا أَقْلَلْنَ ، وَرَبَّ الشَّيَاطِينِ وَمَا أَضْلَلْنَ ، وَرَبَّ الرِّيَاحِ وَمَا ذَرَيْنَ ، أَسْأَلُكَ خَيْرَ
    هَذِهِ الْقَرْيَةِ وَخَيْرَ أَهْلِهَا وَخَيْرَ مَا فِيهَا ، وَأَعُوْذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ أَهْلِهَا وَشَرِّ مَا فِيهَا.

    Allahumma rabbas-samawatis-sab’i wama azlalna, warabbal- aradeenas-sab’i wama aƙlalna, warabbash-shayateeni wama adlalna, warabbar-riyahi wama zarayna, as-aluka khayra hathihil-qaryah, wakhayra ahlilha wakhayra ma feeha, wa- a’oozu bika min sharriha washarri ahliha, washarri ma feeha.

    Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da abin da suka rufe, kuma Ubangijin ƙassai bakwai da abin da suke ɗauke da shi, kuma Ubangijin shaiɗanu da waɗanda suka ɓatar, kuma Ubangijin iska da abin da ta yayyaɗa! Ina roƙon Ka alherin wannan alƙarya, da alherin mutanen da ke cikinta, da alherin abin da ke cikinta. Kuma ina neman tsari da Kai daga sharrinta, da sharrin mutanenta, da sharrin abin da ke cikinta.

    Karanta Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Addu’a Idan Mutum Ya Ga Wani Abu Mai Ban Mamaki

    Addu’a idan mutum ya ga wani abu mai ban mamaki, ko na farin ciki

    سُبْحَانَ اللهِ

    Subhanallah

    Tsarki ya tabbata ga Allah.

    الله أكبر

    Allahu akbar

    Allah ne Mafi girma.

    Danna nan don karanta Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    Addu’a Ga Wanda Yace Maka: Allah Ya Yi Maka Albarka

    وَفِيكَ بَارَكَ الله.

    Wa fi ka  barakallah

    Kai ma Allah ya yi maka albarka.

    Karanta Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Addu’a Ga Wanda Aka Zo Biyansa Bashinsa

    Addu’a ga wanda ya ba da bashi idan aka zo biyan sa bashinsa

    بَارَكَ اللهُ لَكَ فِي أَهْلِكَ وَمَالِكَ ، إِنَّمَا جَزَاءُ السَّلَفِ الْحَمْدُ وَالأَدَاء .

    Barakallahu laka fi ahlika wa malika. Inna ma jaza’u salafil hamdu wal’ada’i

    Allah ya yi maka albarka a cikin iyalinka da dukiyarka. Haƙiƙa sakamakon bashi shi ne godiya da biya.

    Karanta Addu’ar Ƙin Shu’umci

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Ƙin Shu’umci

    Addu’ar Ƙin Shu’umci

     

    اللهُمَّ لاَ طَيْرَ إِلا طَيْرُكَ وَلَا خَيْرَ إِلا خَيْرُكَ وَلاَإِلَهَ غَيْرُكَ

    Allahumma la ɗaira illa ɗairuka wala khaira illa khairuka wala ilaha gairuka

    Ya Allah! Babu shu’umci sai abin da Ka halitta, kuma babu alheri sai alherinka, kuma babu abin bautawa da gaskiya ba Kai ba.

    Ƙarin Bayani; Shu’umci shi ne mutum ya kudurce cewa wani abu mummuna zai faru gare shi saboda ganin wani abu ko jin sa. Wannan haramun ne, saboda abin da ke cikinsa na jingina tasiri ga wanin Allah, da kuma munana zato ga Allah. To wanda irin wannan ya afku gare shi, kar ya bar aikata abin da ya yi nufin yi; sai ya tuba ga Allah, sannan kaffararsa ita ce ya faɗi wannan addu’ar. [Bayanin mai tarjama].

    Don karanta Addu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa danna nan

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa

    Addu’ar Wanda Ya Ji Wani Ciwo A Jikinsa

    Annabi, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya ce: ‘Ka sanya hannunka a wajen da yake maka ciwo a jikinka, ka ce:

    بِسْمِ اللهِ

    ثلاثاً

    Bismillah. Da sunan Allah (nake neman waraka). (sau uku)

    Sannan ka ce:

    أعُوْذُ بِاللهِ وَقُدْرَتِهِ مِنْ شَرِّ مَا أَجِدُ وأَحَاذِر

    (سبع مرات)

    A’uzu billahi wa ƙudratihi min sharri ma ajidu wa uhadir

    Ina neman tsari da Allah da kuma Ikonsa daga sharrin abin da nake ji (na ciwo) kuma nake jin tsoransa (sau bakwai)

    Karanta Addu’ar Tafiya (Wadda Matafiyi Yake Yi)

    Edita@rumasau-kallamu

  • Addu’ar Tafiya (Wadda Matafiyi Yake Yi)

    Addu’ar Tafiya (Wadda Matafiyi Yake Yi)

    الله أكبر، الله أكبر، اللهُ أَكْبَرُ سُبْحَانَ الذي سَحْرَ لَنَا هَذَا وَمَا كُنَّا لَهُ مُقْرِنِينَ وَإِنَّا إِلَى رَبَّنَا لَمُنْقَلِبُونَ ، اللهُمَّ إنا نسألُكَ فِي سَفَرنَا هَذَا الْبِرَّ والتّقْوَى ، وَمِنَ الْعَمَلِ مَا تَرْضَى ، اللهُمَّ هَون عَلَيْنَا سَفَرَنَا هَذَا وَاطوِ عَنَّا بُعْدَهُ ، اللهُمَّ أَنتَ الصَّاحِبُ في السَّفَرِ، وَالْخَلِيفَةُ في الأَهْلِ، اللهُم إِنِّي أَعُوْذُ بِكَ مِنْ وَعْنَاءِ السَّفَرِ ، وَكابَةِ الْمَنْظَرِ وَسُوءِ الْمُنقَلبِ فِي الْمَالِ وَالأَهْلِ.

    Allahu akbar, Allahu akbar, Allahu akbar, subhanallazi sakkara lana haza wama kunna lahu muƙrineen wa ina ila rabbina lamun ƙalibun allahumma ina nas’aluka fi safarina haza al-birra wattaƙwa, wa minal amali ma tarda, Allahuma hauni alaina safarana haza wadwi anna bu’udahu, Allahuma anta sahibu fil safari wal kalifatu fil ahli allahuma inni a’uzubika min wana’i safari wa kabatil wanzari wa su’il mun ƙalibi fil mali wal ahli

    Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma, Allah ne Mafi girma. Tsarki ya tabbata ga (Ubangiji) Wanda ya hore mana wannan (abin hawa); ba mu kasance masu ikon sarrafa shi ba. Haƙiƙa mu masu komawa ne zuwa ga Ubangijinmu. Ya Allah! Muna roƙon Ka nagarta da tsoron Allah a cikin wannan tafiya ta mu, da kuma aiki wanda Kake yarda da shi. Ya Allah! Ka sauƙaƙe mana wannan tafiya ta mu, kuma ka naɗe mana nisanta. Ya Allah! Kai ne Ma’abocinmu a cikin wannan tafiya, kuma Halifanmu a cikin iyalanmu. Ya Allah! Ina neman tsari da Kai daga wahalar tafiya, da abin gani mai sanya ɓacin rai, da kuma komawa mummuna ga iyali da dukiya.

    Domin karanta Yadda Ake Addu’ar Hawa Abin Hawa danna nan

    Edita@rumasau-kallamu