Yadda Ake Sallar Idi

0
823

Sallar Idi babba da ƙarama sunna ce babba mai ƙarfi,a mazhabar Malik da Shifi’I, amma a mazhabar Abu Hanifa da Ahmad sallar idi wajibi ce, wannan shi ne zaɓin Shaihul Islam Ibn Taimiyya.

Sallar idi ana yin ta a bayan gari, raka’a biyu ce, ba a yi mata kiran salla, ballantana iƙama, ana ƙara kabbarori guda shida bayan kabbarar harama a raka’ar farko, da kuma kabbarori bayan raka’a ta biyu, a bayyane ake yin karatunta sannan ana yin huɗuba bayan an gama sallar.
Waɗannan su ne ingantattun nafiloli na sallah, Allah ya sa mu dace.

Domin karanta cikakken bayani a kan Nafilolin Azumi danna nan.

Wannan bayani anciro shine daga littafin Ingantattun Nafiloli Da Falalarsu wanda Usman Abubakar Muhammad (Shehu Mansur Dala) ya wallafa shi domin karanta cikakken littafin danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Sujjadar Godiya Ga Allah
Labarin na GabaFalalar Nafilolin Azumi