Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Cut Short - A turance tana nufin guntule.
Misali; A musulunci hukuncin sata shi ne guntule hannu.
HAU; Guntule (Tana nufin yanke wani sashi)
Cuta - Tana nufin rashin lafiya.
Misali; Wata sabuwar cuta ta ɓullo mai suna korona.
ENG; Illness (A turance tana nufin cuta)
Cuɗanya - Tana nufin mu'amala da mutane.
Misali; Na yi cudanya da mutane da dama da na je Turai.
ENG; Mingling With Others (A turance tana nufin cuɗanya)
Da - Tana nufin tare.
Misali; Ni da yayana farare ne.
ENG; With (A turance tana nufin da)
Da’ira - Tana nufin zagayayye.
Misali; Yara sun yi da'ira suna wasa.
ENG; Circle (A turance tana nufin da'ira)
Daddawa - Tana nufin sinadarin girki mai sa ƙamshi da armashin abinci.
Misali; Miyar kuka ta fi daɗi idan ta ji daddawa.
ENG; Locust bean (A turance tana nufin daddawa)
Dafa - Tana nufin sa abu a cikin tukunya a zuba ruwa a ɗora a wuta har ya yi laushi.
Misali; Sai da aka dafa abincin aka yi sadakar da shi.
ENG; Cook (A turance tana nufin dafa)
Dafi - Tana nufin abin da ke iya kisa, zai iya kasancewa daga dabbobi ko wani abu daban.
Misali; Dabbobin da suke da dafi suna da hatsari matuƙa.
ENG; Poison (A turance tana nufin dafi)
Dafifi - Tana nufin taruwar jama'a da yawa.
Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa.
ENG;Large Mass (A turance tana nufin dafifi)
Daga - Tana nufin gumurzu ko shan fama.
Misali; An sha daga da shi kafin ya yadda a yi masa allurar.
ENG; Struggle (A turance tana nufin daga)