Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Dakaru - Jam'in dakare, jarumai masu tafiya yaki a kafa, kamar sojan kasa a yanzu.
Dakau - Tana nufin yin daka a matsayin sana'a.
Misali; Matar Ado dakau take yi a unguwarsu.
ENG: Pounding corn for pay (A turance tana nufin dakau)
Dakile - Hanawa, kamar hana wani al'amari musamman mara kyau ko barna cigaba da faruwa ko yaduwa
Dako - Tana nufin ɗaukarwa mutum kaya a kai masa inda yake so, ya biya.
Misali; Ƙungiyar masu dako sun koka kan ƙarancin biyansu da mutane ke yi.
ENG; Carrying load for payment (A turance tana nufin dako)
Dakushe - Tana nufin rashin kaifi.
Misali; Wuƙaƙen sun dakushe sai an wasa su.
ENG; Blunt (A turance tana nufin dakushe)
Dala - Tana nufin nau'in kuɗin ƙasar Amurka.
Misali; Babu Nera a lalitarsa sai Dala.
ENG; Dollar (A turance tana nufin dala)
Dalala - Tana nufin zubar yawu daga baki ba ƙaƙƙautawa.
Misali; Yawu yana dalala daga bakinsa saboda nauyin bacci.
ENG;Dribble (of saliva) (A turance tana nufin dalala)
Dalla-Dalla - Tana nufin yin abu daki-daki a bayyane.
Misali; Malamin yana bayani dalla-dalla ga ɗalibansa.
ENG; Clearly (A turance tana nufin dalla-dalla)
Damage - A turance tana nufin ɓarna.
Misali; An yi iska mai ƙarfi jiya kuma ta yi ɓarna sosai
HAU; Ɓarna (Tana nufin lalata abu)
Damatsiri - Tana nufin ƙaramin koren maciji mai dafi.
Misali; Akwai damatsiri a gonar shinkafar da ke bayan gari.
ENG; Small poisonous green snake (A turance tana nufin damatsiri)