Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Cowboy - A turance tana nufin kaboyi. Misali; Mutanen da sun kwaikwayi turawa wajen sanya hular kaboyi. HAU; Kaboyi (Tana nufin hula mai faɗi da turawa suke sa wa)
Craving/ Yearning - A turance tana nufin kwaɗayi. Misali; Tun da ta fara kwaɗayi na san tana da juna biyu. HAU; Kwaɗayi (Tana nufin tsananin son cin abu ko yin abu)
Creature - A turance tana nufin halitta. Misali; Allah shi ne ya ƙagi Annabi Muhammad (SAW) ya sa ya zamo shugaban halitta baki ɗaya. HAU; Halitta (Tana nufin ƙirƙirarren abu)
Cricket - A turance tana nufin gyare. Misali; Ƙarar gyare na damuna idan dare ya yi. HAU; Gyare (Tana nufin tsanya. Wani ƙwaro mai ƙara da daddare)
Cries - A turance tana nufin koke-koke. Misali; Na jiyo ana ta koke-koke a gidan mutuwar, Allah ya gafarta masa da rahama. HAU; Koke-koke (Tana nufin jam'in kuka)
Criminal Investigation Division (CID) - Sashen binciken laifuka
Cripple - A turance tana nufin gurgu. Misali; Ya zama gurgu ne sanadiyyar hatsarin motar da suka yi. HAU; Gurgu (Tana nufin wanda ba shi da ƙafa) Kishiyarta; Mai ƙafa
Crocodile - A turance tana nufin kada. Misali; Ruwan sama mai yawa ya sa kada ta fito daga gidan ajiyar namun daji. ENG; Kada (Tana nufin wata dabbamai kaushin baya kuma mai siffar ƙadangare da ke rayuwa a ruwa, amma tana da girma ainun)
Cross In Front - A turance tana nufin gifta. Misali; Na ga Iliya ya gifta ɗazu. HAU: Gifta (Tana nufin wucewa ta gaban abu)
Crown - A turance tana nufin kambi.  Misali; Sarkin yana sanye da kambi a lokacin da aka yi taron. HAU; Kambi (Tana nufin wani abu mai kamar hula da sarakuna da 'ya'yansu ke sa wa)
1 70 71 72 73 74 298