Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Confederation - Kadaura, Ƙungiya
Confederation of African Football (CAF) - Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka
Confused/Flustered - A turance tana nufin kiɗime.
Misali; Duk sun kiɗime saboda tashin hankali.
HAU; Kiɗime (Tana nufin gigicewa ko shiga wani hali)
Congregation of people for joint prayer - A turance tana nufin jam'i.
Misali; Sun yi jam'i za su yi sallar azahar.
HAU; Jam'i (Tana nufin haɗuwar mutane don yin sallah)
Consortium - Ƙungiya, Kadaura
Consumer Protection Council (CPC) - Hukumar kare Haƙƙin matsayi (Mamori)
Controversy - A turance tana nufin jayayya.
Misali; Tun safe suke jayayya a kan kuɗi.
HAU; Jayayya (Tana nufin faɗi in faɗa)
Cook - A turance tana nufin kuku.
Misali; Gidan attajirai ne ake ajiye kuku.
HAU; Cook (Tana nufin wanda yake aikin dafa abinci)
Cook - A turance tana nufin dafa
Misali; Sai da aka dafa abincin aka yi sadakar da shi.
HAU; Dafa (Tana nufin sa abu a cikin tukunya a zuba ruwa a ɗora a wuta har ya yi laushi)
Cool Off - A turance tana nufin huce.
Misali; Abincin da na kawo har ya huce kuna hira.
HAU; Huce (Tana nufin yin sanyi)