Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Code of Conduct Bureau (CCB) - Hukumar ɗa'ar ma'aikata
Cold - A turance tana nufin hunturu.
Misali; Lokacin hunturu akan kunna wuta domin jin ɗumi.
HAU; Hunturu (Tana nufin lokacin sanyi)
Collar - A turance tana nufin kwala.
Misali; Yana sanye ne da riga mai kwala launin shuɗi.
HAU; Kwala (Tana nufin wuyan riga irin ta Bature)
College - A turance tana nufin kwaleji.
Misali; Duk wanda zai shiga kwaleji sai ya yi jarrabawa.
HAU; Kwaleji (Tana nufin makarantar gaba da firamare ko gaba da sakandire)
College - A turance tana nufin kwaleji.
Misali; Idan matasa suka shiga kwaleji suna jin kansu.
HAU; Kwaleji (Tana nufin makaranta musamman ta gaba da sakandire)
Colleges of Education Academic Staff Union (CEASU) - Ƙungiyar malaman kwalejojin ilimi
Collision - A turance tana nufin karo.
Misali; Karo na yi da bango saboda duhu, shi yasa goshi na ya kumbura.
HAU; Karo (Tana nufin haɗuwar ba-zata)
Comission on things sold - A turance tana nufin kamasho.
Misali; Mukan samu kamasho a kowanne kaya da aka siyar a shago.
HAU; Kamasho (Tana nufin wani kaso na kuɗi da ake samu bayan an yi ciniki)
Commission - Hukuma, Kwamiti
Common Sense - A turance tana nufin kan-gado.
Misali; Yaron yana da kan-gado ainun.
HAU; Kan-gado (Tana nufin hankali ko fahimta)