Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Coalition of Northern Youth Groups (CNYG) - Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa
Coalition of Northern Youth Groups (CNYG) - Gamayyar ƙungiyoyin matasan Arewa
Cocin ECWA/ Cocin Ƴaɗa Kiristanci Ta Yammacin Afirka - Evangelical Church of West Africa (ECWA)
Cock Crow - A turance tana nufin cara. Misali; Tun da zakara ya yi cara na farka. HAU; Cara (Tana nufin kukan da zakara yake yi musamman da asuba)
Cocky young person who wears western dress - A turance tana nufin gaye. Misali; Ai yanzu ya zama gaye, kullum za ka gan shi da shigar nasara. ENG; Gaye (Tana nufin matashi wanda yake shiga irin ta turawa)
Coco-yam - A turance tana nufin gwaza. Misali; Na gamu da mai siyar da gwaza da fita kasuwa. HAU; Gwaza (Tana nufin makani)
Cocoa Reserch Institute of Nigeria (CRIN) - Cibiyar Binciken koko Ta Nejeriya
Coconut - A turance tana nufin kwakwa. Misali; Kunun kwakwa na da matuƙar daɗi da ƙara lafiya. HAU; Kwakwa (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan marmari mai mutuƙar amfani ga ɗan Adam)
Cocumber-like Vegetable - A turance tana nufin gurji. Misali; Gurji yana da daɗi idan an kwaɗanta shi da ƙuli-ƙuli. HAU; Gurji (Tana nufin wani nau'i na kayan lambu mai kama da kwakunba amma ya fi ta girma)
Code of Conduct Bureau (CCB) - Hukumar ɗa'ar ma'aikata
1 65 66 67 68 69 300