Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Move to another place -

A turance tana nufin ƙaura.

Misali; Iyalan sun yi ƙaura daga ƙauyensu zuwa birni domin samun ayyukan yi.

HAU; Ƙaura (Tana nufin barin wani wuri zuwa wani wuri)

Mucus that collects in the eye during sleep -

A turance tana nufin kwantsa.

Misali; Yaron ya goge kwantsa daga idonsa da safe.

HAU; Kwantsa (Tana nufin datti mai kamar majina da ke taruwa a ido yayin barci musamman idan idon yana ciwo)

Mud - A turance tana nufin caɓi . Misali; Ka yi hankali da caɓi a hanyar saboda jiya an kwana ana ruwa. HAU; Caɓi (Tana nufin jiƙaƙƙiyar ƙasa)
Multinational Corporation (MNC) - Kamfanonin Manyan Ƙasashe
Multinational Joint Task Forces (MJTF) - Rundunar Tsaro Ta Haɗin Guiwar Ƙasashe
Multiple Of Ten - A turance tana nufin gomiya. Misali; Gomiya biyar tana nufin hamsin kenan. HAU; Gomiya (Tana nufin goma sau wani adadi)
Mumps - A turance tana nufin hangum. Misali; Hangum ne ya fitowa Safiya, tana kan shan magani. HAU; Hangum (Tana nufin ciwon da ke kumbura gefen kunci zuwa kunne)
Music - A turance tana nufin kiɗa. Misali; Matasan sun kunna kiɗa suna cashewa don murnar bikin abokinsu. HAU; Kiɗa (Tana nufin rauji ko sauti mai daɗi)
Music Producers & Marketers Association of Nigeria (MUPMAN) - Ƙungiyar Mawaƙa da Dillalan Waƙa Ta Najeriya
Musical Copyright Society of Nigeria (MCSN) - Ƙungiyar Haƙƙin Mallakar Mawaka Ta Najeriya
1 228 229 230 231 232 337