Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ministry - Ma'aikata
Ministry of Police Affairs - Ma'aikatar Harkokin 'Ƴansanda
Misfortune/Calamity - A turance tana nufin ja'iba.
Misali; Ya ga ja'iba, bayan ya rasa ɗansa shagonsa ya kama da wuta.
HAU; Ja'iba (Tana nufin masifa ko rashin sa'a ko ibtila'i)
Misfortune/Loss - A turance tana nufin hasara.
Misali; Sun yi hasara sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a yankin su.
HAU; Hasara (Tana nufin rasa wani abu)
Kishiyarta; Riba
Missing Someone - A turance tana nufin kewa.
Misali; Idan mutum ya rasu akan kasance cikin kewarsa a kodayaushe.
HAU; Kewa (Tana nufin son gani ko kasancewa da wanda ba ya kusa ko ya rasu)
Mix Something - A turance tana nufin kwaɓa.
Misali; Farida ta kwaɓa miki fanken mana, za ki samu sauƙin aikin.
HAU; Kwaɓa (Tana nufin haɗa abu da ruwa a jujjuya)
Mix Thoroughly - A turance tana nufin cakuɗa.
Misali; Amina tana cakuɗa kwaɗon zogale.
HAU; Cakuɗa (Tana nufin a yi ta jujjuya abu)
Mix Together - A turance tana nufin gauraya.
Misali; Ado ya gauraya garin dawar da rogo.
HAU; Gauraya (Tana nufin cakuɗa abubuwa su zama ɗaya)
Mockery - A turance yana nufin ba'a.
Misali; Lado ya yi wa Kande ba'a, ya ce mata mai ƙaton hanci.
HAU; Ba'a (Tana nufin aibata mutum ko wata gaɓa ko wani sashe na halittarsa)
Modeling Agencies Association of Nigeria (MAAN) - Kadaurar Ƙungiyoyin Taurari Ta Najeriya