Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Ɓarza - Tana nufin niƙa tishi ɗaya ko biyu, ma'ana ba mai laushi ba.
Misali; Na kai wa Inna ɓarza, za ta yi dambu da yamma.
ENG; Grind Coarsely (A turance tana nufin ɓarza)
Ɓata - Tana nufin a nemi abu a rasa.
Misali; Ina tunanin takalmin ya ɓata, don na duba ko ina ban ganshi ba.
ENG; Lost (A turance tana nufin ɓata)
Ɓauna - Tana nufin wata dabbar daji mai kama da saniya.
Misali; A gidan ajiyar namun daji akwai ɓauna da sauran manyan dabbobi.
ENG; Bush-cow (A turance tana nufin ɓauna)
Ɓaɓatu - Tana nufin magana ba ƙaƙƙautawa.
Misali; Mun baro su suna ta ɓaɓatu a ɗakin taron.
ENG; Noisy (A turance tana nufin ɓaɓatu)
Ɓaɓe - Tana nufin samun saɓanin da zai kai ga kowa ya kama gabansa.
Misali; Talle ya ɓaɓe da budurwarsa jiya.
ENG; Break Off relationship (A turance tana nufin ɓaɓe)
Ɓaɓɓake - Tana nufin jijjige abu daga tushensa.
Misali; Ya ɓaɓɓake bishiyar daga ƙofar gidansa.
ENG; Uproot (A turance tana nufin ɓaɓɓake)
Ɓingire - Tana nufin kwanciya ba tare da tsammani ba.
Misali; Ta ɓingire da bacci ana karatu.
ENG; Topple Over (A turance tana nufin ɓingire)
Ɓoye - Tana nufin a ɗauke abu a kai shi inda ba za a ganshi ba.
Misali; Yaran sun ɓoye kayan wasan su, mun nema mun rasa.
ENG; Hide (A turance tana nufin ɓoye)
Ɓulele - Tana nufin mai ƙiba.
Misali; Sabon ɗalibin da aka kawo mana ɓulele ne.
ENG; Fat (A turance tana nufin ɓulele)
Ɓullo - Tana nufin fitowa.
Misali; Rana ta ɓullo da wuri yau.
ENG; Appear Suddenly (A turance tana nufin ɓullo)