Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Muslim Media Practitioners of Nigeria (MMPN) - Ƙungiyar Musulmai 'Ƴanjarida Ta Najeriya
Muslim Rights Concern (MURIC) - Ƙungiyar kare-Haƙƙin Musulmai
Muslim Students Society of Nigeria (MSSN) - Ƙungiyar Ɗalibai Musulmai Ta Najeriya
Must - A turance tana nufin dole. Misali; Dole ne dukkan musulmi ya yi sallah sau biyar a rana. HAU; Dole (Tana nufin wajibi ko tilas)
Mutuntaka - Halaye da ɗabi'un kowane ɗan'adam, wadanda suke bambanta daga mutum zuwa mutum.
Mutuntakar Koyarwa - Ɓangare Ne Na Ilimin Koyarwa Da Ake Naƙaltar Mabambantan Ɗabi'u da Halayen Ɗalibai Ko Mutane.
Naked State - A turance tana nufin gaya. Misali; Ta dama min fura gaya, ba nono bare suga. HAU; Gaya (Tana nufin tsura ko tsirara)
Nape of the neck - A turance tana nufin ƙeya. Misali: Mutumin ya ji ciwo a ƙeya bayan ɗaukar kaya masu nauyi. HAU: Ƙeya (Tana nufin bayan wuya, wato sashen da ke tsakanin kai da kafaɗa)
Nation - A turance tana nufin al'umma. Misali; Al'ummar Hausawa na da ɗimbin tarihi. HAU; Al'umma (Tana nufin mutane ko jama'ar wani yanki)
National Root Crops Research Institute (NRCRI) - Cibiyar Nazarin Amfanin Gona Mabunƙusa-ƙasa Ta Najeriya
1 229 230 231 232 233 337