Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi
Majibanta - Masu taimakawa jama'a
Majority - A turance tana nufin galibi.
Misali; Galibi akan yi ruwa mai yawa a watan Agusta.
HAU; Galibi (Tana nufin mafi yawa)
Makamashi - Sinadarin da ake hada wuta ko makami da shi kamar itace ko uraniyam.
Makaranta - Makaranta wuri na koyon ilimi wanda mutane suke zuwa dan koyon karatu,kamar yara ko manya jinsin maza da mata suke zuwa dan koyon ilimin addini ko na boko.
makaraya - Masu kai ƙara kotun shari'a, waɗanda suke shari da wani/wasu a gaban Alƙali.
Make beautiful -
A turance tana nufin ƙawata.
Misali: Ta ƙawata ɗakin bikin ta da furanni da fitilu masu launi.
HAU: Ƙawata (Tana nufin gyara wani abu don ya zama mai kyau ko abin kallo)
Make Slushy - A turance tana nufin caɓa.
Misali; Amaryar ta caɓa ado sosai.
HAU; Caɓa (Tana nufin yin ado da yawa)
Makimanta - Masu kimanta darajar ƙasa ko gida, musamman wajen kimanta darajar muhalli.
Male Hyena - A turance tana nufin kure.
Misali; Auwalu ya kamo kure, da shi yake wasa ranar kasuwa.
HAU; Kure (Tana nufin namijin kura)
Malicious Act - A turance tana nufin Ƙeta.
Misali: Ƙeta ce raba makaho da sandarsa.
HAU: Ƙeta (Tana nufin aikata wani mummunan abu da nufin cutarwa ko yin sharri ga wani)