Ƙamusu

Ƙamus ɗin Hausa wanda yake bada ma’ana da bayanin kalma cikin harshen Hausa ayanar gizo-gizo cikin sauƙi

Love portion smeared on the eye - A turance tana nufin ƙifil. Misali: Wasu mutane sun yarda da cewa ƙifil na iya sa mutum ya ƙaunaci wani. HAU: Ƙifil (Tana nufin wani magani ko haɗi da ake shafawa a ido domin jawo soyayya ko tasiri a kan wani)
Lover / Mistress -

A turance tana nufin kwarto.

Misali: Jiya da yamma an kama kwarto a bayan layinmu ya shiga gidan wani matafiyi.

HAU; Kwarto (Tana nufin masoyi ko wanda ake hulɗar soyayya da shi ba tare da aure ba)

Low mud platform outside compound - A turance tana nufin dakali. Misali; Baba yana zaune a kan dakali da abokinsa suna hira. HAU; Dakali (Tana nufin gini mai ɗan tudu da ake yi a ƙofar gida don zama)
Lungs - A turance tana nufin huhu. Misali; Shan taba yana illata huhu a wasu lokutan ma har a rasa rai. HAU; Huhu (Tana nufin ɓangaren da ke sarrafa iska a jikin ɗan Adam)
Lying down -

A turance tana nufin kwanciya.

Misali; Bayan ya gama aiki ya samu gurin kwanciya domin ya huta.

HAU; Kwanciya (Tana nufin shimfiɗa jiki ko hutawa a kan gado, tabarma ko wani wuri)

Ma’adinai - Albarkar ko arzikin da ake samu ko hakowa daga karkashin kasa kamar zinare (gwal) ko tama ko azurfa ko mai da makamantansu.
Mabada - masu ba wa mutane musamman dalibai a makarantu shawarwari game da rayuwa da  kuma cigaban karatunsu.
Mabambanta - Abubuwa masu bambanci da juna ta wasu fuskoki na musamman.
Madness - A turance tana nufin hauka. Misali; Ya shekara goma yana fama da ciwon hauka. HAU; Hauka (Tana nufin rashin ciwon rashin hankali ko gushewar hankali) Kishiyarta; Hankali
Mahuldanta - Mutane masu kwarewa wajen kai-komo a tsakani ko iya saurarar koken abokan hulda a ma'aikatu da masana'antu.
1 221 222 223 224 225 337