Yadda Ake Addu’a Idan Mutum Yana So Allah Ya Biya Masa Buƙata Cikin Gaggawa

0
1011

Wannan addu’a ita ake kira “gaya wa jini na wuce”; domin biyan buƙata, Wato duk wata buƙata da kake nema wajen Allah (Subahanahu Wata’ala); ko kuma kake son Allah ya biya maka buƙatunka cikin gaggawa; sai ka dage ka ɗauki wannan addu’ar.

Domin samun biyan buƙata, Za ka tashi cikin dare ka inganta alwalarka sannan ka yi nafila raka’ah biyu 2 ko huɗu 4 ko shida 6 ko takwas 8, sannan ka yi istigfari da salatin Annabi da hailala duk adadin da ya sawwaƙa, sai ka yi sujjada sannan ka karanta; 

La ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minal zalimin” – (71)

A cikin sujjada sai ka gaya wa Allah damuwarka sannnan sai ka ɗago ka zauna, sai ka sake istigfari da salatin Annabi da hailala, sai kuma ka karanta suratul Hadid; aya ta ashirin da ɗaya zuwa ta ashirin da huɗu (21-24). Sannan ka karanta wannan addu’ar kamar haka:

Allahumma inni as’aluka bi’ismukal makhzun walmaknun, addahirul muƙaddis; Alhayyul Ƙayyum, Ar-rahmanur Rahim Zil Jalalu Wal Ikram, An Tusalliya Ala Sayyidin Muhammadin (Sallallahu Alaihi Wasallam); wa’an taf’al bi kasha wa kasha (inda zaka faɗi dukkan buƙatunka), birahmatika ya arhamur rahimin”.

Wannan addu’ar an samo ta ne a cikin littafin MIFTAHUL KHAIR shafi na ashirin (20).

Domin karanta cikakken bayani a kan Yadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Shiriyar Ubangiji danna nan.

labarin da ya wuceYadda Ake Addu’ar Nema Wa Yara Shiriyar Ubangiji
Labarin na GabaKalmomi Guda Biyar Masu Amfani A Duniya Da Lahira