Terms Dictionary

Shake dust off something - A turance tana nufin kakkaɓe. Misali; Sai da na kakkaɓe ƙura a kan kujerar kafin na zauna. HAU; Kakkaɓe (Tana nufin goge datti ko ƙura)
Shameless/Disrespectful Person - A turance tana nufin ja'iri. Misali; Babu mai yin rawar Gala sai ja'iri. HAU; Ja'iri (Tana nufin mara kunya)
Sharpen - A turance tana nufin feƙe. Misali; An feƙe wuƙaƙen kafin a yanka naman. HAU; Feƙe (Tana nufin saka abu ya yi kaifi)
Sharpness - A turance tana nufin kaifi. Misali; Wuƙar tana da kaifi sosai don ta yanke ni. HAU; Kaifi (Tana nufin ƙarfin da zai iya yanka)
Shaving - A turance yana nufin kwashe gashi.  Misali; Wanzami yana yi wa Maigari Aski a fadarsa. HAU; Aski (Yana nufin kwashe gashi ta hanyar amfani da aska ko reza ko wani abu daban)
Shea Tree - A turance tana nufin kaɗanya. Misali; Man kaɗanya na gyara fata musamman a lokacin sanyi. HAU; Kaɗanya (Tana nufin 'ya'yan bishiyar kaɗe)
Shivering - A turance tana nufin ɓari. Misali; Gambo sai ɓari yake saboda zafin zazzaɓi. HAU; Ɓari (Tana nufin karkarwa saboda jin sanyi)
Shivering - A turance tana nufin karkarwa. Misali; Idan ba ka sa rigar sanyi ba za ka yi karkarwa saboda yau akwai matuƙar sanyi. HAU; Karkarwa (Tana nufin rawar da jiki yake yi sakamakon zazzaɓi ko jin sanyi)
Shop - A turance tana nufin kanti. Misali; An buɗe sabon kanti a unguwarmu. HAU; Kanti (Tana nufin gurin siyar da kayayyaki)
Short - A turance tana nufin gajere. Misali; Na rubuta gajeren labari a shafin jaridar. HAU: Gajere (Tana nufin mara tsayi)
1 265 266 267 268 269 300