Terms Dictionary

Person of great energy - A turance tana nufin gwarzo. Misali; Abdulhamid shi ne gwarzon wannan shekarar. HAU; Gwarzo (Tana nufin mai ƙwazo)
Person of weak physical constitution - A turance tana nufin kumama. Misali; Sadiq kumama ne, ko yaya aka yi ruwa sai ya sa rigar sanyi. HAU; Kumama (Tana nufin mutum mai saurin jin sanyi)
Person with extra ordinary ability - A turance tana nufin hatsabibi. Misali; Jauro hatsabibi ne, jiya ya shiga dajin da ba kowa ne yake shiga ya fito lafiya ba. HAU; Hatsabibi (Tana nufin mutum mai ɗabi'un ban mamaki ko wanda yake abubuwan tsautsayin da ba kowa ne zai iya ba)
Person with sixth finger - A turance tana nufin cindo. Misali; Jaririn da Latana ta haifa yana da cindo. HAU; Cindo (Tana nufin wanda aka haifa da yatsu shida)
Petrol - A turance tana nufin fetur. Misali; Fetur ya yi matuƙar tsada a Najeriya. HAU; Fetur (Tana nufin man da ake zubawa a mota ko wani abin hawa don ya yi tafiya)
Petroleum & Natural Gas Senior Staff Association of Nigeria (PENGASSAN) - Ƙungiyar Manyan Ma'aikatan Kamfanin Fetur da Gas Ta Najeriya
Petroleum Equalizing Fund (management) Bord - Hukumar Daidaita Farashin Man Metur
Petroleum Products Pricing Regulatory Agency (PPPR) - Hukumar Ƙayyade Farashin Albarkatun Fetur
Petroleum Technology Development Trust Fund (PTDF) - Asusun Bunƙasa Fasahar Fetur
Petroleum Training Institute (PTI) - Kwalejin Horarwa Ta Ma'aikatan Fetur
1 267 268 269 270 271 337