Terms Dictionary

Ma’adinai - Albarkar ko arzikin da ake samu ko hakowa daga karkashin kasa kamar zinare (gwal) ko tama ko azurfa ko mai da makamantansu.
Mabada - masu ba wa mutane musamman dalibai a makarantu shawarwari game da rayuwa da  kuma cigaban karatunsu.
Mabambanta - Abubuwa masu bambanci da juna ta wasu fuskoki na musamman.
Madness - A turance tana nufin hauka. Misali; Ya shekara goma yana fama da ciwon hauka. HAU; Hauka (Tana nufin rashin ciwon rashin hankali ko gushewar hankali) Kishiyarta; Hankali
Mahuldanta - Mutane masu kwarewa wajen kai-komo a tsakani ko iya saurarar koken abokan hulda a ma'aikatu da masana'antu.
Majibanta - Masu taimakawa jama'a
Majority - A turance tana nufin galibi. Misali; Galibi akan yi ruwa mai yawa a watan Agusta. HAU; Galibi (Tana nufin mafi yawa)
Makamashi - Sinadarin da ake hada wuta ko makami da shi kamar itace ko uraniyam.
Makaranta - Makaranta wuri na koyon ilimi wanda mutane suke zuwa dan koyon karatu,kamar yara ko manya jinsin maza da mata suke zuwa dan koyon ilimin addini ko na boko.
makaraya - Masu kai ƙara kotun shari'a, waɗanda suke shari da wani/wasu a gaban Alƙali.
1 2 3 7