Pagan - A turance tana nufin arne.
Misali; Duk wanda ba shi da addini arne ne.
HAU; Arne (Tana nufin wanda ba shi da addini)
Palm wine - A turance tana nufin bammi.
Misali; Bammi yake sha shi yasa kullum ba ya cikin hayyacinsa.
HAU; Bammi (Abin sha ne mai gusar da hankali)
Panting, Gasping - A turance tana nufin haki.
Misali; Gudun da na yi ya sa ni haki.
HAU; Haki (Tana nufin yin numfashi sama-sama da sauri)
Pardon/Forgiveness - A turance tana nufin gafara.
Misali; Allah mai gafara ne ga bayinsa.
HAU;Gafara (Tana nufin yafiya musamman ta Allah SWT)
Parent Teachers Association (PTA) - Ƙungiyar Iyaye da Malaman Makaranta
Parents - A turance tana nufin iyaye.
Misali; Wajibi ne biyayya ga iyaye idan mutum yana son gamawa lafiya.
HAU; Iyaye (Tana nufin mahaifi da mahaifiya)
Parliamentary Staff Association of Nigeria (PASAN) - Ƙungiyar Ma'aikatan Majalisar Dokoki Ta Najeriya
Pastor - A turance tana nufin fasto.
Misali; Maƙococinsa babban fasto ne.
HAU; Fasto (Tana nufin limamin coci)
Patch - A turance tana nufin faci.
Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro.
HAU; Faci (Tana nufin sacewar taya)
Paternal Uncle - A turance yana nufin Baffa.
Misali; Alhaji Barau baffana ne.
HAU; BAffa (Yana nufin ɗanuwan mahaifi)