Terms Dictionary

Lack - A turance tana nufin fatara. Misali; Gidan suna fatarar abinci. HAU; Fatara (Tana nufin rashin kuɗi ko abin duniya)
Lahadi - Rana ce ta ƙarshe a mako.  Misali; A kan ɗaura aure a ranar Lahadi. ENG; Sunday (A turance tana nufin Lahadi, rana ta ƙarshe a mako)
Lake Chad Research Institute (LCRI) - Cibiyar Binciken Tafkin Cadi
Land-monitor - A turance tana nufin damo. Misali; Ana masa kirari da damo sarkin haƙuri. HAU; Damo (Tana nufin dabba mai siffar ƙadangare amma ta fi ƙadangare girma)
Laraba - Rana ce ta uku a cikin ranakun mako.  Misali; Ranar Laraba za a fara jarabawar. ENG; Wednesday (A turance tana nufin rana ta uku a mako)
Large - A turance tana nufin danƙwalele. Misali;Na siyowa kakata danƙwalelen goro a kasuwa. HAU;Danƙwalele (Tana nufin babba ko mai girma)
Large hen - A turance tana nufin daƙwalwa. Misali; Kazar daƙwalwa ce don ta ƙosar da mu. HAU; Daƙwalwa (Tana nufin babbar kaza ma'abociyar tsoka)
Large hoe with wide blade - A turance tana nufin garma. Misali; Gatari ba zai yi aikin nan ba sai dai a sa garma. HAU; Garma (Tana nufin ƙaton gatari mai faffaɗan kai)
Large Mass - A turance tana nufin dafifi. Misali; Mutane sun yi dafifi a wajen kallon wasan kalankuwa. HAU; Dafifi (Tana nufin taruwar jama'a da yawa)
Large needle - A turance tana nufin basilla. Misali; Na yi amfani da basilla na ɗinke buhun kayana. HAU; Basilla (Tana nufin allura babba da ake amfani da ita wajen ɗinke buhu ko ƙwarya da sauransu)
1 2 3 5