Terms Dictionary

Fa’ida - Tana nufin amfanin abu. Misali; Zumunci yana da fa'ida don yana sa albarka a rayuwa. ENG; Usefulness (A turance tana nufin fa'ida) Kishiyarta; Rashin Fa'ida
Fabrairu - Wata ne na biyu a shekara.  Misali; Za a gudanar da taron a watan Fabrairun wannan shekarar. ENG; February(A turance yana nufin wata na biyu a shekara)
Facaka - Tana nufin kashe kuɗi ba tare da la'akari ba. Misali; Tun da aka raba musu gado yake facaka da kuɗi. ENG; Squandering (A turance tana nufin facaka)
Face - Tana nufin sai dai. Misali; Babu wanda zai makara face ya kasance mai saɓa alƙawari. ENG; Except (A turance tana nufin face)
Face - A turance tana nufin fuska. Misali; Ta mare shi a fuska hakan ya janyo suka fara faɗa. HAU; Fuska (Tana nufin sashen jiki mai ƙunshe da ido da hanci da baki)
Faci - Tana nufin sacewar taya. Misali; Tayar keken ta yi faci sai an an gyaro. ENG; Patch (A turance tana nufin faci)  
Facial Markings - A turance tana nufin jarfa. Misali; Jarfa, gadon gidansu ne. HAU; Jarfa (Tana nufin tsagun fuska)
Faffaɗar Jami’ar Najeriya - National Open University Of Nigeria (NOUN)
Fage - Tana nufin fili ko dandali. Misali; An ba wa 'yan dambe fage don su fafata. ENG; Open Space/Arena (A turance tana nufin fage)
Fahimta - Tana nufin ganewa. Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske. ENG; Understand (A turance tana nufin fahimta) Kishiyarta; Rashin Fahimta
1 2 3 17