Wages - A turance tana nufin jinga.
Misali; Mun yi jinga da shi zai biya ni da zarar na kammala aikin.
HAU; Jinga (Tana nufin yarjejeniyar biyan kuɗi)
Waistcoat - A turance tana nufin falmaran.
Misali; Falmaran ɗin da yarima ya sa ta yi kyau ƙwarai da gaske.
HAU; Falmaran (Tana nufin riga mara hannu da ake ɗorawa a kan mai dogon hannu)
Wake up - A turance tana nufin Farka.
Misali; Jaririn ya farka tun ɗazu.
HAU; Farka (Tana nufin tashi daga bacci)
Wall - A turance tana nufin garu.
Misali; Ƙadangare yana yawo a juikin garu.
HAU; Garu (Tana nufin bango)
Warning - A turance yana nufin gargaɗi.
Misali; Shugaban ɗalibai ya yi wa ɗalibai gargaɗi akan zuwa makaranta a makare.
HAU; Gargaɗi (Tana nufin jan kunne ko yin hani)
Watch - A turance tana nufin kallo.
Misali; Yana shigowa ɗakin taron kowa ya bi shi da kallo.
HAU; Kallo (Tana nufin duba izuwa wani abu)
Water from leaky roof - A turance tana nufin bi-bango.
Misali; Ɗakin ruwa yana bi-bango musamman idan ana ruwa da yawa.
HAU; Bi-bango (Tana nufin ruwa ya dinga biyo bango daga rufin kwano)
Watermelon - A turance tana nufin kankana.
Misali; Kankana ta fi yawa a cikin kayan marmarin da muka siyo.
HAU; Kankana (Tana nufin ɗaya daga cikin kayan maramari mai ɗauke da ruwa sosai a ciki)
Wealth - A turance tana nufin daula.
Misali; Lami tana cikin daula saboda mijinta yana da kuɗi.
HAU; Daula (Tana nufin dukiya ko kayan alatu da ƙawa na duniya)
Wealthy person - A turance yana nufin mutum mai dukiya.
Misali; Maƙocinmu attajiri ne.
Kishiyarta; Talaka
HAU; Attajiri (Mutum mai tarin dukiya)