Terms Dictionary

Haba-haba - Tana nufin ba da kulawa ka'in da na'in. Misali; Ana ta haba-haba da manyan baƙi. ENG; Taking good care of something (A turance tana nufin haba-haba)
Habaici - Tana nufin magana a fakaice ba tare da ambaton suna ba, amma shi wanda ake da shi ya sani.  Misali; Tun safe take yi wa kishiyarta habaici. ENG; Indirect Reference (A turance tana nufin habaici)
Hadari - Tana nufin yanayin da ke nuna za a yi ruwan sama. Misali; Hadari ya taso, da alama za a yi ruwa mai yawa. ENG; Storm (A turance tan nufin hadari)
Hadda - Tana nufin riƙe abu da ka. Misali; Usman yana ajin hadda, za su sauke Ƙur'ani cikin shekara ɗaya. ENG; Memorization (A turance tana nufin hadda)
Haddasa - Tana nufin sila ko zama dalilin faruwar wani abu. Misali; Zuwanta a makare shi ya haddasa ta rasa gurin zama. ENG; Cause (A turance tana nufin haddasa)
Haddi - Tana nufin hukuncin da ake wa wanda ya aikata laifi a musulunci. Misali; Haddin sata yanke hannu ne a musulunci. ENG; Fixed Punishment for transgressing islamic law (A turance tana nufin haddi)
Hadejia-Jama’are River Basin Development (HJRBD) - Hukumar Haɓaka kogin Haɗeja-jama'are
Hadisi - Tana nufin maganganun manzon Allah SAW. Misali;Malam Ado yana karanta mana hadisi kullum a makaranta. ENG: Sayings of prophet Muhammad SAW (A turance tana nufin Hadisi)
Hagu - Tana nufin ɓarin hagu a jikin ɗan Adam, idan aka kalli mutum daga sama zuwa ƙasa, ɓari ɗaya shi ne hagu ɗayan kuma dama. Misali; Da hannun hagu yake rubutu. ENG; Left (A turance tana nufin hagu) Kishiyarta; Dama
Haila - Tana nufin jinin da mata ke fitarwa a kowanne wata. Misali; Matan da ke haila ba sa shiga masallaci. ENG; Menstruation (A turance tana nufin haila)
1 2 3 23