Terms Dictionary

Kadaura - Babbar kungiya ko  cibiya wadda ta hado mahimman bangarori masu  zaman kansu ko kwararrun ma'aikata ko mutane.
Kafafen Intanet - Matattara ko inda ake samun bayanan da aka nema daga rumbon sadarwa.
Kai-dauki - Taimakawa ko kai agaji domin ceto.
Karate Fedaration of Nigeria (KFN) - Hukumar Wasan Kareti Ta Najeriya
Karkara - Karkara wani yanki ne na gari wanda yake ke6antaccen waje ne da yakje da karancin jama'a da kuma yake da yawan gonaki da filaye.
Kartagai - Shugabannin caca, wanda suka mallaki kaya da ma wuri ko gidajen yin cacar.
Kufai - Gurbi na ramuka ko koguna ko gine-ginen da suke nuna cewar mutane sun taba wanzuwa/zama a wurin a  zamunnan  baya.
Kumbon Sadarwa - Tauraron dan'adam, wato kumbon da ake harbawa zuwa sararin sama ko wata duniyar domin sadarwa, musamman ta radiyo da waya da tattaro bayanai.