Terms Dictionary

Ulcerated Wound - A turance tana nufin gyambo. Misali; Ai gyambon da ke ƙafarsa ya daɗe sosai. HAU; Gyambo (Tana nufin ciwon da ba ya warkewa ko kuma ya daɗe bai warke ba)
Uncompleted Building - A turance tana nufin kango. Misali; Har yanzu ginin kango ne ba a ƙarasa ba. HAU; Kango (Tana nufin ginin da ba a kammala ba)
Understand - A turance tana nufin fahimta. Misali; Ɗaliban suna da fahimta ƙwarai da gaske. HAU; Fahimta (Tana nufin ganewa) Kishiyarta; Rashin Fahimta
Understand - A turance tana nufin gane. Misali; Ina fatan kun gane abinda nake nufi? HAU; Gane (Tana nufin fahimta) Kishiyarta; Rashin Ganewa
Ungrateful - A turance tana nufin butulu Misali; Cindo butulu ne saboda ya butulcewa maigidansa a kasuwa. HAU; Butulu (Tana nufin wanda yake manta alkahairin da aka yi masa)
Union - Tarayya, Gamayya, Ƙungiya
United Labour Congress (ULC) - Gamayyar Ƙungiyoyin Ƙwadago
United Nations (UN) - Majilisar Ɗinkin Duniya
United Nations Development Program (UNDP) - Shirin Bunƙasa Ƙasashe Na Majilisan Ɗinkin Duniya
United Nations Economic Commission for Africa (UNECA) - Kwamitin Tattalin Arzikin Afrika Na Majalisanr Ɗinkin Duniya
1 2 3